Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | A GOVERNMENT FREE OF CORRUPTION

Mulkin Allah—Gwamnatin da Babu Cin Hanci da Rashawa

Mulkin Allah—Gwamnatin da Babu Cin Hanci da Rashawa

“Ma’aikatan gwamnati ’yan ƙasa ne, kuma idan ’yan ƙasa suna karɓan cin hanci da rashawa, ba yadda za a yi barewa ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe.” Kalamin wani babban oditan ƙasar Nicaragua ke nan, a yayin da yake furta albarkacin bakinsa a kan dalilin da ya sa a ganinsa ba za a iya kawar da cin hanci da rashawa a gwamnati ba.

Hakika, idan ’yan ƙasa suna cin hanci da rashawa, babu shakka, gwamnati ma za ta kasance da wannan ɗabi’ar, ko ba haka ba? Saboda haka, ’yan Adam ba za su iya kafa gwamnatin da babu cin hanci da rashawa ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai wata gwamnati da babu cin hanci da rashawa. Wannan gwamnatin ita ce Mulkin Allah, wadda Yesu ya ce almajiransa su riƙa yin addu’a ya zo.—Matta 6:9, 10.

Mulkin Allah gwamnati ce da take mulki a sama a yanzu haka, kuma zai sauya dukan gwamnatocin duniya. (Zabura 2:8, 9; Ru’ya ta Yohanna 16:14; 19:19-21) Ɗaya daga cikin abubuwa masu ban sha’awa da Mulkin Allah zai yi wa ’yan Adam shi ne kawar da cin hanci da rashawa. Ka yi la’akari da abubuwa shida da suka ba da tabbacin haka.

1. IKO

HALIN DA AKE CIKI: A yawancin lokatai, gwamnatocin duniya suna samun kuɗaɗen tafiyar da ayyukansu ne daga harajin da mutane suke biya. Waɗannan kuɗaɗen sun zama jaraba ga wasu ma’aikatan gwamnati kuma hakan na sa su sata. Wasu kuma suna karɓan toshiya daga mutanen da suke so a rage musu haraji ko kuma kuɗaɗen da ya kamata su biya gwamnati. Wannan yana sa gwamnati ta ƙara yawan haraji don ta sami isashen kuɗi kuma a sakamakon  haka, cin hanci da rashawa tana daɗa yaɗuwa. A irin wannan yanayin, matalauta ne suke yawan shan wahala.

MAFITA: Mulkin Allah yana tafiyar da al’amuransa ne da ikon Jehobah, * Allah maɗaukaki. (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Wannan gwamnatin ba ta bukatar haraji don tafiyar da al’amuranta. A maimakon haka, za ta biya wa kowa bukatarsa, saboda ‘girman ikon’ Allah da kuma karimcinsa.—Ishaya 40:26; Zabura 145:16.

2. MASARAUCI

HALIN DA AKE CIKI: Susan Rose-Ackerman, wadda aka ambata a talifin baya ta ce idan ana so a yaƙi cin hanci da rashawa, “wajibi ne a soma daga shugabanni.” Babu yadda gwamnati za ta iya hana ’yan sanda da ma’aikatan kwastam cin hanci da rashawa idan su shugabannin da kansu ma ba a bar su a baya ba. Ƙari ga haka, kome adalcin masarauci, yana iya yin kuskure saboda ajizanci. Littafi Mai Tsarki ya ce “babu wani mai adalci ko ɗaya cikin duniya, wanda yana aika[ta] nagarta, ba tare da zunubi ba.”—Mai-Wa’azi 7:20.

Yesu ya ƙi da toshiya mafi girma a tarihi

MAFITA: Yesu Kristi wanda Allah ya naɗa a matsayin sarkin wannan Mulkin ba ajizi ba ne kamar ’yan Adam. Saboda haka, babu wanda zai iya jarabtarsa ya yi abin da bai dace ba. Mun ga tabbacin hakan a yadda Yesu ya ƙi da toshiya mafi girma a tarihi, wato “dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.” Iblis mai mulkin wannan duniyar ne ya yi alkawari zai ba Yesu wannan toshiyar idan Yesu ya yi masa sujada sau ɗaya kawai. (Matta 4:8-10; Yohanna 14:30) Ko a lokacin da Yesu yake bakin mutuwa ma, ya riƙe amincinsa kuma ya ƙi da maganin kashe zafi, don ya san da cewa hakan zai sa ya fita daga hayyacinsa. (Matta 27:34) Allah ya ta da Yesu daga mutuwa, kuma a yanzu da yake raye a sama, ya nuna cewa ya cancanci zama sarkin Mulkin.—Filibiyawa 2:8-11.

3. GWAMNATI MAI ƊOREWA

HALIN DA AKE CIKI: Ƙasashe da yawa suna yin zaɓe a kai a kai don suna ganin ta hakan ne za su kawar da shugabanni masu cin hanci. Amma a gaskiya, ana cin hanci da rashawa a lokacin kamfen da kuma zaɓe har ma a ƙasashe masu arziki. Masu kuɗi sukan ba ’yan siyasa goyon baya da kuɗi a lokacin kamfen kuma hakan yana ba su iko a kan waɗannan ’yan siyasan sa’ad da suka soma mulki.

John Paul Stevens, wani alƙali a Kotun Ƙoli ta Amirka ya ruwaito cewa irin wannan tasirin da masu arziki suke da shi a kan shugabanni yana yin barazana ga “cancantar gwamnati da ingancinta da kuma yadda jama’a suke dogara da ita.” Wannan ne ya sa mutane da yawa a faɗin duniya suke ganin babu cibiyar da ta kai na siyasa cin hanci da rashawa.

MAFITA: Mulkin Allah gwamnati ce da za ta dawwama. Saboda haka, ba za a yi kamfen ba balle a yi cuwa-cuwa a zaɓe. (Daniyel 7:13, 14) Tun da yake Allah ne ya naɗa sarkin, zaɓen ’yan Adam ba zai yi  tasiri a kan gwamnatin ba. Da yaƙe ba za a sauya wannan gwamnatin ba, tabbas ne cewa dukan abubuwan da za ta cim ma za su amfani talakawanta dindindin.

4. DOKOKI

Mulkin Allah gwamnati ce da take mulki a sama a yanzu haka

HALIN DA AKE CIKI: Da farko, ana iya gani kamar idan aka kafa sababbin dokoki, za a sauƙaƙa matsalar cin hanci da rashawa. Amma masana sun gano cewa a yawancin lokuta, yin hakan yana daɗa ba da zarafin cin hanci da rashawa ne kawai. Ƙari ga haka, ana kashe ɗimbin kuɗi wajen zartar da dokokin da za su sauƙaƙa matsalar cin hanci da rashawa, amma a ƙarshe, ba a cim ma wani abin kirki.

MAFITA: Dokokin Mulkin Allah suna da fifiko a kan dokokin gwamnatocin duniya. Alal misali, maimakon Yesu ya ba da jerin dokoki, ya ba da wata sananniyar doka a kan yadda ya kamata mu bi da mutane. Ya ce: “Dukan abu fa iyakar abin da kuke so mutane su yi muku, ku yi musu haka nan kuma.” (Matta 7:12) Mafi muhimmanci ma dokokin Mulkin Allah suna shafan ayyukan mutane har da muradinsu. Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:39) Hakika, Allah ya san zuciyar ’yan Adam, saboda haka, shi ne zai iya zartar da irin wannan dokar.—1 Sama’ila 16:7.

5. MURADI

HALIN DA AKE CIKI: Abubuwan da ke haifar da cin hanci da rashawa su ne kwaɗayi da kuma son zuciya, kuma a yawanci lokatai shugabanni da kuma mazauna ƙasa suna da waɗannan munanan ɗabi’un. A batun cibiyar kasuwanci da ta rushe a birnin Seoul, wadda aka ambata a talifin baya, ma’aikatan gwamnati ne suka karɓi hanci daga ’yan kwangilar domin ’yan kwangilar su sami damar yin amfani da kayayyakin gini masu araha kuma su ƙeta dokokin gini.

Saboda haka, idan ana so a kawar da cin hanci, wajibi ne a koyar da mutane yadda za su shawo kan munanan ɗabi’u kamar su kwaɗayi da kuma son zuciya. Amma, gwamnatocin duniya ba su da niyyar kafa irin wannan tsarin ilimantarwa, kuma ko da tana da shi, ba za ta iya aiwatarwa ba.

 MAFITA: Mulkin Allah za ta magance matsalar cin hanci da rashawa ta wajen koya wa mutane yadda za su shawo kan munanan muradi da ke haifar da wannan halin. * Wannan ilimantarwar za ta sa su ‘sabonta azancinsu.’ (Afisawa 4:23) Za su koyi yadda za su zama masu wadar zuci da son mutane maimakon masu kwaɗayi da kuma son kai.—Filibiyawa 2:4; 1 Timotawus 6:6.

6. TALAKAWA

HALIN DA AKE CIKI: Kome kyan abubuwa da kuma tarbiyyar da mutane suka samu, wasu daga cikinsu za su zama masu rashin gaskiya da karɓan rashawa. Masana sun gano cewa wannan ne dalilin da ya sa gwamnatocin duniya ba za su iya kawo ƙarshen cin hanci da rashawa ba. Abin da za su iya yi kawai shi ne su rage yawan wannan matsalar da kuma lahaninta.

MAFITA: Wata yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Kan Cin Hanci da Rashawa ta nuna cewa gwamnati tana bukatar ta koya wa mutane “yin gaskiya da kuma ɗaukan hakki” idan tana so ta kawar da cin hanci da rashawa. Hakika, wannan buri ne mai kyau, amma a ƙarƙashin mulkin Allah, wajibi ne talakawanta su kasance da waɗannan halayen, ba kawai su san halin ba. Littafi Mai Tsarki ya ce “masu-ƙyashi” da “maƙaryata” ba za su shiga Mulkin Allah ba.—1 Korintiyawa 6:9-11; Ru’ya ta Yohanna 21:8.

Mutane za su iya koyan waɗannan ɗabi’u masu kyau, kuma tabbacin hakan shi ne misalin Kiristoci na zamanin dā. Alal misali, wani almajiri mai suna Siman ya yi ƙoƙari ya ba manzannin Yesu kuɗi don su ba shi ikon ba mutane ruhu mai tsarki, amma manzannin sun yi tir da roƙonsa kuma suka ce masa: “Ka tuba fa da wannan muguntarka.” Da Siman ya gano cewa abin da yake so ya yi babban zunubi ne, sai ya ce wa manzannin su yi masa addu’a don ya shawo kan wannan muradin.—Ayyukan Manzanni 8:18-24.

YADDA ZA KA IYA SHIGA MULKIN ALLAH

Za ka iya zama ɗaya daga cikin talakawan Mulkin Allah ko da kai ɗan wace ƙasa ce. (Ayyukan Manzanni 10:34, 35) Wannan Mulkin ya kafa wani tsarin ilimantarwa a duk faɗin duniya da zai taimaka maka ka yi hakan. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin nuna maka yadda suke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a gidajensu kyauta, ko da na tsawon minti goma ne kawai, sau ɗaya a mako. Ta wannan nazarin, za ka sami ƙarin haske a kan “bishara ta Mulkin Allah” da kuma yadda Mulkin zai kawar da cin hanci da rashawa a gwamnati. (Luka 4:43) Don Allah ka tuntuɓi Shaidun Jehobah a yankinku ko kuma ka ziyarci shafinmu na jw.org/ha.

Za ka so a riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai a gidanka kyauta?

^ sakin layi na 8 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.

^ sakin layi na 22 Alal misali, ka duba talifin nan “Yaƙi da Rashawa da Takobi na Ruhu” a cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Mayu, 2000.