Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 27

Ka Jimre Kamar Jehobah

Ka Jimre Kamar Jehobah

“Idan kuka jimre, za ku tsira.”​—LUK. 21:19.

WAƘA TA 114 Ku Kasance Masu “Haƙuri”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Ta yaya abin da Jehobah ya faɗa a Ishaya 65:16,17 yake ƙarfafa mu kada mu gaji?

“KAR KA GAJI!” shi ne jigon taron yankinmu na 2017. Taron yankin ya nuna mana yadda za mu iya jimre matsaloli. Shekaru huɗu sun riga sun wuce tun da aka yi wannan taron yankin, kuma har ila muna kan jimre matsaloli dabam-dabam a wannan muguwar duniya.

2 Waɗanne matsaloli ne kake fuskanta? Shin wani a iyalinku ko abokinka ya rasu? Kana fama da rashin lafiya ko tsufa? Kana zama a inda bala’i ya auku, ko ana wulaƙanta ka, ko kuma tsananta maka? Ko dai kana fama da matsaloli saboda cututtuka kamar annobar koronabairas? Muna marmarin lokacin da dukan abubuwan nan za su wuce, kuma ba za mu ƙara ganin su ba!​—Karanta Ishaya 65:16, 17.

3. Mene ne muke bukatar mu yi yanzu, kuma me ya sa?

3 Rayuwa a wannan duniyar tana da wuya, kuma a nan gaba za mu iya fuskantar matsalolin da suka fi waɗannan wuya. (Mat. 24:21) Shi ya sa muke bukatar mu ci gaba da jimrewa. Me ya sa? Domin Yesu ya ce: “Idan kuka jimre, za ku tsira.” (Luk. 21:19) Za mu iya jimrewa idan muka yi tunanin yadda wasu ma suke jimre irin matsalolin da muke fuskanta.

4. Me ya sa muka ce Jehobah ne ya fi jimrewa?

4 Wane ne ya fi jimrewa? Jehobah ne. Shin hakan ya ba ka mamaki ne? Wataƙila hakan ya ba ka mamaki, amma idan ka yi tunani a kai, ba za ka yi mamaki ba. Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar, kuma tana cike da matsaloli. Jehobah yana da ikon kawar da waɗannan matsalolin nan take, amma yana jiran lokacin da ya dace ya yi hakan. (Rom. 9:22) Kafin wannan lokacin, Allahnmu yana kan jimrewa har sai lokacin da zai hallaka mugaye. Bari mu tattauna abubuwa tara da Jehobah yake jimrewa.

MENE NE JEHOBAH YAKE JIMREWA?

5. Ta yaya ake ɓata sunan Allah, kuma yaya hakan yake sa ka ji?

5 Jehobah yana jimre yadda ake ɓata sunansa. Jehobah yana ƙaunar sunansa, kuma yana so kowa ya daraja sunan. (Isha. 42:8) Amma an yi wajen shekaru 6,000 yanzu, ana ɓata sunansa. (Zab. 74:10, 18, 23) An soma yin hakan ne a lokacin da Iblis ya zargi Allah da hana Adamu da Hauwa’u abin da suke bukata don su yi farin ciki. (Far. 3:1-5) Tun daga lokacin, an ci gaba da zargin Jehobah da hana ’yan Adam abubuwan da suke bukata. Yesu ya damu da yadda ake ɓata sunan Ubansa. Saboda haka, ya koya wa almajiransa su yi addu’a cewa: “Ubanmu wanda yake cikin sama, a kiyaye sunanka da tsarki.”​—Mat. 6:9.

6. Me ya sa Jehobah ya bar dogon lokaci ya wuce kafin ya nuna cewa shi ne yake da ikon mulkin sama da ƙasa?

6 Jehobah yana jimre yadda mutane da yawa suka ƙi shi da kuma mulkinsa. Jehobah ne yake da iko ya yi mulki a kan sama da ƙasa, kuma sarautarsa ce mafi kyau. (R. Yar. 4:11) Amma Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya ruɗe mala’iku da kuma ’yan Adam don ya sa su ga kamar Allah ba shi da ikon yin sarauta a kansu. Zai ɗauki lokaci kafin kowa ya ga cewa Jehobah ne yake da ikon yin mulki kuma sarautarsa ce ta fi kyau. Allah ya bar ’yan Adam su riƙa mulki na dogon lokaci don su ga cewa ba za su iya yin nasara idan suna mulkin kansu ba. (Irm. 10:23) Yadda Jehobah ya jimre zai sa a warware wannan batun gabaki ɗaya. Kowa zai ga cewa yadda Jehobah yake sarauta ne ya fi kyau, kuma mulkinsa ne kaɗai zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

7. Su waye ne suka yi wa Jehobah tawaye, kuma mene ne zai yi musu?

7 Jehobah ya jimre yadda wasu daga cikin yaransa suka yi tawaye. Jehobah bai halicci mala’iku da mutane da zunubi ba. Amma mala’ikan nan Shaiɗan ya yi wa Jehobah tawaye, kuma ya rinjayi kamiltattun mutane wato Adamu da Hauwa’u su ma su yi wa Jehobah tawaye. Wasu mala’iku har da ’yan Adam ma sun bi misalinsu. (Yahu. 6) Daga baya, wasu daga cikin al’ummar Isra’ila, wato mutanen Allah, sun yi masa tawaye kuma suka soma bauta wa gumaka. (Isha. 63:8, 10) Jehobah ya ce sun ci amanarsa. Duk da haka ya jimre, kuma zai ci gaba da jimrewa har sai lokacin da zai kawar da dukan masu tawaye. A lokacin, Jehobah da amintattun bayinsa za su yi farin ciki, domin ba za su ƙara jimre muguntar da ake yi a duniya ba!

8-9. Waɗanne ƙaryace-ƙaryace ne ake yi a kan Jehobah, kuma mene ne za mu iya yi game da hakan?

8 Jehobah yana jimre ƙaryar da Shaiɗan yake yi. Shaiɗan ya zargi Ayuba da kuma dukan bayin Allah masu aminci cewa suna bauta wa Jehobah ne domin abubuwan da yake ba su. (Ayu. 1:8-11; 2:3-5) Shaiɗan yana kan zargin mutane har a yau. (R. Yar. 12:10) Za mu iya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne ta wajen jimre matsaloli da kuma riƙe aminci ga Jehobah domin muna ƙaunar shi. Jehobah ya albarkaci Ayuba, kuma abin da zai yi mana ke nan idan muka jimre.​—Yak. 5:11.

9 Shaiɗan yana amfani da shugabannin addinan ƙarya yana cewa Jehobah mugu ne kuma shi ne yake sa ’yan Adam su sha wahala. Idan yara suka mutu, wasu daga cikinsu sukan ce Allah ne ya ɗauki yaran domin yana bukatar ƙarin mala’iku a sama. Wannan saɓo ne sosai! Mun san cewa Jehobah Uba ne mai ƙauna. Ba ma ɗora wa Allah laifi idan muka kamu da wani rashin lafiya mai tsanani ko kuma wani da muke ƙauna ya mutu. A maimakon haka, muna da bangaskiya cewa Allah zai kawar da rashin lafiya kuma ya tā da matattu. Za mu iya gaya wa duk wanda yake so ya saurare mu cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna. Hakan zai ba Jehobah damar mai da martani ga wanda yake zargin sa.​—K. Mag. 27:11.

10. Mene ne Zabura 22:23, 24 suka bayyana game da Jehobah?

10 Jehobah yana jimre yadda bayinsa suke shan wahala. Jehobah Allah ne mai tausayi sosai. Yana baƙin ciki a duk lokacin da ya ga muna kuka saboda wahalar da muke sha, wataƙila domin tsanantawa ko rashin lafiya ko kuma ajizancinmu. (Karanta Zabura 22:23, 24.) Jehobah ya san yadda muke ji, yana so ya magance matsalar kuma zai yi hakan. (Ka gwada Fitowa 3:7, 8; Ishaya 63:9.) Lokaci na zuwa da ‘zai share dukan hawaye daga idanunmu’ ba za a sake “mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba.​—R. Yar. 21:4.

11. Yaya Jehobah yake ji game da amintattun bayinsa da suka mutu?

11 Jehobah yana kewar abokansa da suka mutu. Yaya Jehobah yake ji game da bayinsa masu aminci da suka mutu? Yana so ya sake ganin su! (Ayu. 14:15) Ka yi tunanin yadda Jehobah yake marmarin sake ganin abokinsa Ibrahim! (Yak. 2:23) Ko kuma Musa wanda ya yi magana da shi “fuska da fuska.” (Fit. 33:11) Jehobah yana marmarin sake jin Dauda da sauran marubutan zabura suna rera masa waƙoƙin yabo! (Zab. 104:33) Ko da yake waɗannan abokan Allah sun mutu, Jehobah bai manta da su ba. (Isha. 49:15) Yana tuna kome game da su. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘A wurinsa dukansu rayayyu ne.’ (Luk. 20:38, Littafi Mai Tsarki) Wata rana, zai tā da su daga mutuwa, ya saurari addu’o’insu kuma ya amince da ibadarsu. Idan aka yi maka rasuwa, waɗannan kalmomi za su iya ta’azantar da kai.

12. Mene ne yake sa Jehobah baƙin ciki sosai a wannan kwanaki na ƙarshe?

12 Jehobah yana jimre yadda ’yan Adam masu mugunta suke sa wasu shan wahala. Bayan da aka yi tawaye a lambun Adnin, Jehobah ya san cewa abubuwa za su daɗa muni kafin su gyaru. Jehobah ba ya son yadda ake mugunta da rashin adalci da kuma yaƙe-yaƙe a duniya. Ya daɗe yana tausaya wa waɗanda ake yawan wulaƙanta su, kamar marayu da gwauraye. (Zak. 7:9, 10) Wani abin da yake sa Jehobah baƙin ciki sosai shi ne yadda ake wulaƙanta amintattun bayinsa da kuma saka su a kurkuku. Ku kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar dukanku yayin da kuke jimrewa kamar sa.

13. Waɗanne irin halaye masu ƙazanta ne Allah yake gani tsakanin ’yan Adam, kuma mene ne zai yi game da su?

13 Jehobah yana jimre yadda ɗabi’un ’yan Adam suka lalace. Jehobah ya halicci ’yan Adam yadda za su yi koyi da halayensa, amma Shaiɗan yana jin daɗin sa su su ɓata ɗabi’unsu. A zamanin Nuhu, Jehobah ya “lura cewa muguntar ’yan Adam ta yi yawa.” Ya yi “baƙin ciki da ya yi ’yan Adam a duniya, kuma zuciyarsa ta ɓaci ƙwarai.” (Far. 6:5,6, Littafi Mai Tsarki11) Shin ’yan Adam sun gyara halayensu tun daga lokacin ne? A’a! Shaiɗan yana farin cikin ganin yadda ’yan Adam suke lalata, har da lalata tsakanin jinsi ɗaya! (Afis. 4:18, 19) Shaiɗan yana farin ciki sosai a duk lokacin da ya sa waɗanda suke bauta wa Jehobah su yi zunubi. Idan lokaci ya yi, Jehobah zai nuna cewa ya tsane kowace irin lalata ta wajen hallaka mutanen da suka ƙi tuba.

14. Mene ne ’yan Adam suke yi wa shuke-shuke da dabbobi?

14 Jehobah yana jimre yadda ’yan Adam suke lalata duniya. Mutane suna wahalar da juna kuma ba sa kula da duniya da dabbobi kamar yadda Jehobah ya ce su yi. (M. Wa. 8:9; Far. 1:28) Wasu ’yan kimiyya sun yi gargaɗi cewa abubuwan da ’yan Adam suke yi zai iya sa wasu shuke-shuke da dabbobi miliyan ɗaya su hallaka nan da ’yan shekaru. Abin da ya sa mutane suke damuwa game da mahalli ke nan! Amma muna farin ciki domin Jehobah ya yi alkawari cewa zai “halaka masu halaka duniya” kuma ya mai da duniya ta zama aljanna.​—R. Yar. 11:18; Isha. 35:1.

ABIN DA MUKA KOYA DAGA YADDA JEHOBAH YAKE JIMREWA

15-16. Mene ne ya kamata ya sa mu ci gaba da jimrewa kamar Jehobah? Ka ba da misali.

15 Ka yi tunanin yadda Jehobah ya yi shekaru da yawa yana jimre matsaloli. (Ka duba akwatin nan “ Abubuwan da Jehobah Yake.”) Jehobah zai iya hallaka muguwar duniyar nan a duk lokacin da ya ga dama. Amma yadda yake jimrewa ya taimaka mana sosai! Ga wani misalin da zai taimaka mana mu fahimci hakan. A ce an gaya ma wani mutum da matarsa cewa jaririn da za su haifa zai kasance da naƙasa, zai sha wuya sosai kuma zai yi saurin mutuwa. Amma iyayen sun yi farin ciki sa’ad da aka haifi jaririn duk da cewa kula da shi ba zai yi musu sauƙi ba. Yadda suke ƙaunar jaririn zai sa su jimre duk matsalar da za su fuskanta yayin da suke kula da shi.

16 Haka ma, an haifi duka ’ya’yan Adamu da Hauwa’u da ajizanci. Duk da haka, Jehobah yana ƙaunar su kuma yana kula da su. (1 Yoh. 4:19) Amma bambancin da ke tsakanin Jehobah da iyayen da muka ambata a misalin shi ne, Jehobah zai iya magance matsalolin ’yan Adam. Ya riga ya saka ranar da zai kawar da duk matsalolin ’yan Adam. (Mat. 24:36) Ya kamata yadda muke ƙaunar Jehobah ta sa mu ci gaba da jimrewa kamar yadda yake yi.

17. Me ya sa abin da aka faɗa a 1 Bitrus 2:21-24 game da Yesu zai iya ƙarfafa mu mu ci gaba da jimrewa?

17 Jehobah ne ya fi kafa misali mai kyau na jimrewa. Yesu ya yi nasarar bin misalin Ubansa ta wajen jimrewa. A lokacin da Yesu yake duniya, an zage shi, an kunyatar da shi kuma an kashe shi a kan gungumen azaba, amma Yesu ya jimre dominmu. (Karanta 1 Bitrus 2:​21-24.) Misalin da Jehobah ya kafa na jimrewa ne ya taimaka wa Yesu shi ma ya jimre. Mu ma zai iya taimaka mana.

18. Ta yaya 2 Bitrus 3:9 za ta taimaka mana mu fahimci abin da yake faruwa domin Jehobah yana haƙuri?

18 Karanta 2 Bitrus 3:9. Jehobah ya san lokacin da ya dace ya kawar da mugunta da ake yi a wannan duniya. Domin yadda yake jimrewa, miliyoyin mutane sun sami damar koya game da shi da kuma bauta masa. Dukansu suna farin ciki cewa Jehobah ya yi shekaru yana jimrewa har aka haife su, suka koya game da shi, suka soma ƙaunar sa da kuma bauta masa. Sa’ad da miliyoyin mutane suka jimre har ƙarshe, za mu ga cewa shawarar da Jehobah ya yanke na yin haƙuri ta dace!

19. Mene ne za mu ci gaba da yi, kuma wane lada ne za mu samu?

19 Jehobah yana nuna mana yadda za mu iya jimrewa tare da farin ciki. Duk da baƙin ciki da matsalolin da Shaiɗan yake jawowa, Jehobah ya ci gaba da kasancewa “Allah mai farin ciki.” (1 Tim. 1:11, New World Translation) Mu ma za mu iya yin farin ciki yayin da muke jiran lokacin da Jehobah zai tsarkake sunansa, ya nuna cewa shi ke da ikon yin sarauta, ya kawar da mugunta da ake yi kuma ya magance dukan matsalolin da muke fuskanta. Bari mu ci gaba da jimrewa kuma mu sami ƙarfafa ta wajen sanin cewa Ubanmu na sama ma yana jimrewa. Idan muka yi hakan za mu more abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa: “Mai albarka ne mutumin da ya jimre cikin wahalarsa, gama in ya jimre cikin gwaji, zai karɓi hular lada na rai madawwami wanda Allah ya yi alkawari zai ba dukan masu ƙaunarsa.”​—Yak. 1:12.

WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna

^ sakin layi na 5 Dukanmu muna da matsalolin da muke fuskanta. A yanzu ba za mu iya magance dukansu ba, don haka, muna bukatar mu jimre. Amma ba mu kaɗai ba ne muke jimrewa. Jehobah ma yana jimre abubuwa da yawa. A wannan talifin, za mu tattauna tara daga cikin abubuwan nan. Ƙari ga haka, za mu ga abubuwa masu kyau da suka faru domin Jehobah ya jimre, da kuma yadda za mu iya bin misalinsa.