Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Ina Farin Ciki a Bautar Jehobah

Ina Farin Ciki a Bautar Jehobah

NA SOMA hidima a Bethel na Kanada a 1958, a lokacin da nake shekara 18. Aiki na farko da na yi a wurin shi ne share wurin da ake buga littattafai. Na ji daɗin rayuwata, kuma ba da daɗewa ba, na soma aiki da injin da ke yanka littattafai bayan an buga su. Na yi farin ciki cewa an kira ni yin hidima a Bethel.

Bayan shekara ɗaya, an yi wata sanarwa a Bethel cewa ana bukatar waɗanda za su yarda su je su yi aiki da sabon injin buga littattafai da ke Bethel na ƙasar Afirka ta Kudu. Na ba da kai kuma na yi farin ciki da aka zaɓe ni. Ƙari ga haka, an zaɓi wasu ’yan’uwa uku daga Bethel na Kanada, wato Dennis Leech da Bill McLellan da kuma Ken Nordin. An gaya mana cewa za mu yi shekaru da yawa a Afirka ta Kudu!

Na kira mahaifiyata kuma na gaya mata cewa: “Mama, albishirinki, zan je Afirka ta Kudu! Mahaifiyata ba mai yawan magana ba ce, amma ita mai bangaskiya ce sosai kuma tana ƙaunar Allah. Ba ta yi magana sosai ba, amma na san ta goyi bayana. Ko da yake babana da mamata sun yi baƙin ciki cewa zan yi nisa da su, ba su ƙi amincewa da shawarar da na yanke ba.

NA JE AFIRKA TA KUDU!

Muna cikin jirgin ƙasa daga Cape Town zuwa Johannesburg tare da Dennis Leech da Ken Nordin da kuma Bill McLellan a 1959

Sa’ad da mu huɗun muka sake haɗuwa a Afirka ta Kudu a 2019 bayan shekaru 60

Kafin mu yi tafiyar, mu huɗu mun je Bethel da ke Brooklyn don a koya mana yin amfani da injin buga littattafan. Sai muka shiga jirgin ruwa zuwa birnin Cape Town da ke Afirka ta Kudu. A lokacin, na cika shekara 20 ke nan. Da yamma, mun shiga jirgin ƙasa daga birnin Cape Town zuwa birnin Johannesburg, wani wuri mai nisa sosai. Wuri na farko da muka tsaya washegari shi ne, wani ƙaramin gari a yankin Karoo da ke kusa da hamada. Yankin na da ƙura da zafi sosai. Dukanmu huɗun mun leƙa ta wundo kuma muka yi mamakin wurin. Mun soma tunanin ko yaya wannan sabon aikin da za mu je yi zai kasance. Amma daga baya, mun gano cewa wannan yankin yana da kyau kuma mutanen suna zaman lafiya sosai.

Aikin da na fara yi a cikin ’yan shekaru bayan na isa ƙasar shi ne, yin amfani da injin da ake kira Linotype, ina shirya ƙarafunan da ke ɗauke da harufa a kansu kafin a yi amfani da su wajen buga mujallun Hasumiyar Tsaro da kuma Awake!. A lokacin, ofishinmu da ke Afirka ta Kudu yana buga littattafai a yaruka da yawa don Afirka ta Kudu da kuma wasu ƙasashe a Afirka. Mun yi farin ciki cewa ana amfani da injin buga littattafai da ya kawo mu daga Kanada!

Daga baya, na yi aiki a ofishin da ke kula da buga littattafai da rarraba su da kuma aikin fassara. Na ji daɗin rayuwata a lokacin ko da yake na yi ayyuka sosai.

NA YI AURE KUMA NA SOMA SABON HIDIMA

Ni da Laura, a lokacin da muke hidimar majagaba ta musamman a 1968

A 1968, na auri wata ’yar’uwa majagaba mai suna Laura Bowen da take zama kusa da Bethel. Ta yi wa Bethel aiki a matsayin mai bugun tafireta. A lokacin, ba a barin mutanen da suka yi aure su zauna a Bethel, sai aka tura mu yin hidimar majagaba na musamman. Na ɗan damu, domin na yi shekara goma a Bethel, inda ake ba ni abinci a yalwace da wurin kwana. Ta yaya za mu yi manejin ɗan alawus da ake ba masu hidimar majagaba na musamman? A kowane wata, akan ba kowannenmu kuɗin da a lokacin darajarsa ta kai dalla 35 idan mun iya mun kai adadin sa’o’i da koma ziyara da kuma adadin littattafan da ake bukata a gare mu. Da kuɗin ne muke biyan haya da sayan abinci da magani da yin tafiye-tafiye da dai sauransu.

An tura mu yin hidima a wani ƙarami rukuni da ke kusa da birnin Durban a gaɓar Tekun Indiya. Akwai Indiyawa da yawa a wurin, da yawa daga cikinsu an kawo kakanninsu ne don su yi aiki a kamfanin sukari a wajen 1875. Yanzu suna yin wasu ayyuka dabam, amma ba su manta da al’adunsu da kuma abincinsu ba. Da yake suna jin Turanci, hakan ya sa ya yi mana sauƙi mu yi musu wa’azi.

An bukaci masu hidimar majagaba na musamman su yi sa’o’i 150 a kowace wata, saboda haka, ni da Laura mun shirya cewa za mu yi wa’azi na sa’o’i shida a rana ta farko. A lokacin, ba mu da ɗalibai ko kuma waɗanda za mu koma ziyara a wurinsu, don haka, mun shirya za mu yi awa shida muna wa’azi gida-gida a cikin zafin rana. Bayan mun yi wa’azi na wasu lokuta, na duba agogona sai na ga cewa minti 40 ne kawai muka yi! Na yi tunanin ko za mu iya ci gaba da wannan hidimar.

Nan ba da daɗewa ba, mun tsara ayyukanmu. A kowace rana, mukan ɗauki ɗan abinci da kuma shayi. Idan muka gaji, mukan faka motarmu a ƙarƙashin bishiya. A wasu lokuta, yaran Indiya sukan tsaya su yi ta kallon mu domin mun yi dabam da su! Bayan kwanaki kaɗan, mun soma sabawa, sai muka ga cewa lokaci yana guduwa.

Mutane a yankin suna da karimci, kuma mun yi farin cikin yi musu wa’azi! Indiyawan suna daraja mutane, suna da kirki kuma suna tsoron Allah. ’Yan addinin Hindu da yawa sun saurari wa’azinmu. Sun ji daɗin koya game da Jehobah da Yesu da Littafi Mai Tsarki da salamar da za a mora a duniya a nan gaba da kuma begen tashin matattu. Bayan shekara ɗaya, mun sami ɗalibai 20. A kullum, mukan ci abincin rana tare da ɗaya daga cikin iyalan da muke nazari da su. Mun yi farin ciki sosai.

Nan ba da daɗewa ba, an ba mu sabon aiki, an tura mu yin hidimar mai kula da da’ira a a yankin da ke gaɓar Tekun Indiya. A kowane mako, muna zama a gidan ’yan’uwa yayin da muke ziyartar ikilisiyoyi don mu ƙarfafa ’yan’uwa. Sun ɗauke mu a matsayin iyalinsu, kuma mun ji daɗin cuɗanya da su da yaransu da kuma dabbobinsu. Bayan shekaru biyu, sai aka kira ni daga ofishinmu. An gaya mini cewa: “Muna so ka dawo Bethel.” Sai na ce: “Muna jin daɗin hidimar da muke yi fa.” Amma muna shirye mu je duk inda aka tura mu.

MUN KOMA BETHEL

Na yi aiki a Sashen Hidima sa’ad da na koma Bethel, kuma a wurin na sami damar yin aiki tare da ’yan’uwan da suka manyanta. A lokacin, bayan mai kula da da’ira ya ziyarci ikilisiya, yakan aika rahoto zuwa ofishinmu sa’an nan za a aika wasiƙa zuwa ga ikilisiyar bisa ga rahoton mai kula da da’irar. A wasiƙar, akan ƙarfafa ikilisiyar kuma a gaya musu abin da za su yi. Don haka, sakatarorinmu sukan yi aiki sosai wajen fassara wasiƙu daga yaren Xhosa da Zulu da kuma wasu yaruka zuwa Turanci, kuma su sake fassara daga Turanci zuwa yarukan. Na yi farin cikin yin aiki da waɗannan mafassara domin sun taimaka mini in fahimci matsalolin da ’yan’uwanmu baƙaƙen fata suke fuskanta.

A lokacin, gwamnati ta hana baƙaƙen fata da fararen fata yin cuɗanya da juna. ’Yan’uwanmu baƙaƙen fata suna yin wa’azi da kuma taro da yarensu, kuma ba sa wani yare dabam.

Ban san ’yan’uwanmu baƙaƙen fata sosai ba, da yake na daɗe ina hidima a yankin da ake Turanci. Amma yanzu, na sami damar koyan abubuwa game da ’yan’uwanmu baƙaƙen fata da kuma al’adunsu. Na gano irin matsalolin da ’yan’uwan suke fuskanta domin addini da kuma al’adun ƙasarsu. ’Yan’uwan sun yi ƙarfin zuciya sosai, sun ƙi saka hannu a duk wata al’adar da ta saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, kuma sun guji yin sihiri. Hakan ya sa iyalansu da mutanen ƙauyensu sun tsananta musu sosai amma sun jimre! Mutane a ƙauyuka sun yi fama da talauci sosai. Da yawa ba su je makaranta ba, amma suna daraja Littafi Mai Tsarki.

Akwai lokacin da na sami damar taimakawa a shari’ar da ta shafi ’yancinmu na yin wa’azi da ƙin saka hannu a siyasa da kuma yaƙi. An kori yaran Shaidu daga makaranta domin sun ƙi yin addu’o’i da waƙoƙin coci a makaranta. Ganin yadda waɗannan yaran suka riƙe amincinsu kuma suka nuna ƙarfin zuciya ya ƙarfafa ni sosai.

’Yan’uwanmu da suke ƙasar da a dā ake kira Swaziland kuma sun fuskanci wata matsala dabam. Sa’ad da sarkin ƙasar mai suna Sobhuza na Biyu ya mutu, an bukaci mazaje su aske kansu, mata kuma su rage tsayin gashinsu don su nuna cewa suna makoki. An tsananta wa ’yan’uwa da yawa domin sun ƙi saka hannu a wannan al’ada da take da alaƙa da bautar kakanni. Yadda suka riƙe aminci ya ƙarfafa mu! Mun koyi abubuwa da yawa game da bangaskiya da aminci da kuma haƙuri daga ’yan’uwanmu a Afirka, kuma hakan ya ƙarfafa bangaskiyarmu sosai.

NA KOMA AIKI A SASHEN BUGA LITTATTAFAI

A 1981, an ce in koma Sashen Buga Littattafai don yin amfani da kwamfuta wajen buga littattafai. Na yi farin cikin yin hakan! Hanyoyin buga littattafai sun riga sun soma canjawa. Wakilin wani kamfanin da ke ƙera injin buga littattafai ya ba ofishinmu wani sabon inji mu gwada kyauta. Hakan ya sa mun sauya injuna tara da muke amfani da su da sabbi guda biyar da ake kira phototypesetter. Ƙari ga haka, mun sayo wani sabon injin buga littattafai da ake kira rotary offset kuma hakan ya sa mun soma buga littattafai fiye da yadda muke yi a dā!

Yin amfani da kwamfuta ya taimaka mana mu ƙirƙiro sabuwar hanyar tsara rubutu ta wajen yin amfani da manhajar da ake kira Multilanguage Electronic Publishing System (MEPS). An sami ci gaba sosai a fannin fasaha tun daga lokacin da mu huɗu muka zo Afirka ta Kudu daga Kanada! (Isha. 60:17) Dukanmu huɗun mun auri mata majagaba da ke ƙaunar Jehobah. A lokacin da abubuwan nan ke faruwa, ni da Bill muna hidima a Bethel har ila, amma Ken da Dennis sun riga sun sami ’ya’ya kuma suna zama kusa da Bethel.

Ayyuka sun daɗa ƙaruwa a Bethel. An sami ƙarin yaruka da ake fassara da kuma buga littattafanmu kuma ana kai littattafanmu ƙasashe dabam-dabam. Hakan ya sa an bukaci gina sabuwar Bethel. ’Yan’uwa sun gina wani kyakkyawan Bethel a wani yanki da ke yammacin birnin Johannesburg, kuma an keɓe Bethel ɗin ga Jehobah a 1987. Na yi farin cikin ganin dukan waɗannan abubuwan da kuma yin hidima a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a Afirka ta Kudu na shekaru da yawa.

AN SAKE BA MU WANI SABON AIKI!

A shekara ta 2001, mun yi mamaki da aka ce mu je Bethel na Amirka domin in yi hidima a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu. Ko da yake ba mu ji daɗin barin aikinmu da abokanmu ba, mun yi farin cikin soma sabuwar rayuwa a ofishinmu da ke Amirka.

Amma mun damu cewa za mu rabu da mahaifiyar matata da ta riga ta tsufa. Idan muka ƙaura zuwa New York, zai yi mana wuya mu kula da ita da kyau, amma ’yan’uwan Laura mata uku sun ce za su kula da ita. Sun ce, “Ba za mu iya yin hidima ta cikakken lokaci ba, amma za mu iya kula da mama don ku ci gaba da hidimarku.” Muna musu godiya sosai.

Haka ma ɗan’uwana da matarsa da suke zama a Toronto, a Kanada suka kula da mahaifiyata gwauruwa. A lokacin, ta riga ta yi fiye da shekara 20 tana zama tare da su. Mun gode musu don yadda suka kula da ita har mutuwarta jim kaɗan bayan mun koma Amirka. Babban albarka ne samun ’yan’uwan da suke a shirye su yi canje-canje don su taimaka da kula da iyayen da suka tsufa duk da cewa yin hakan yana iya kasancewa da wuya a wasu lokuta!

Na yi ’yan shekaru a Amirka ina aiki a sashen da ake buga littattafai, inda ake amfani da sabbin injuna na zamani da suka sauƙaƙa aikin. Ba da daɗewa ba, na soma aiki a Sashen da Ke Yin Sayayya. Na ji daɗin shekaru 20 da na yi a wannan Bethel tare da ’yan’uwa da a yanzu sun kai wajen 5,000, da kuma ’yan’uwa wajen 2,000 da suke zuwa aiki daga waje!

Shekaru 60 da suka shige, ban san cewa zan kasance a inda nake yanzu ba. Matata ta goyi bayana a duk shekarun nan. Ina jin daɗin rayuwata! Muna godiya don dukan ayyukan da muka yi, da kuma dukan ’yan’uwa masu ƙaunar Jehobah da muka yi aiki tare da su, haɗe da waɗanda suke ofishinmu a wurare dabam-dabam da muka ziyarta. Yanzu da na wuce shekara 80, ayyukan da nake yi sun ragu domin akwai matasa da za su iya yin ayyukan.

Wani marubucin zabura ya ce: “Mai albarka ce al’ummar da Yahweh shi ne Allahnta.” (Zab. 33:12) Hakan gaskiya ne! Ina godiya cewa na sami damar bauta wa Jehobah tare da bayinsa masu farin ciki.