Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 114

Ku Kasance Masu “Haƙuri”

Ka Zabi Sauti
Ku Kasance Masu “Haƙuri”
DUBA

(Yaƙub 5:8)

 1. 1. Jehobah Allah ne da

  Yake son sunansa sosai.

  Kuma burinsa shi ne

  Ya tsarkake sunansa fa.

  Ya jima yana nuna

  Haƙuri har da ƙauna,

  Amma ba ya jinkiri

  Don shi mai ƙauna ne.

  Yana son duk mu tsira

  Shi ya sa yake haƙuri.

  Yana ba wa mutane

  Damar canja hanyoyinsu.

 2. 2. Halinmu na haƙuri

  Zai sa mu riƙe aminci.

  Zai sa mu farin ciki,

  Zai sa mu daina yin fushi.

  Zai sa mu riƙa nuna

  Ƙauna ga duk mutane,

  Idan muna wahala

  Zai taimaka mana.

  Allahnmu yana so mu

  Kasance da halayensa.

  In muna yin haƙuri

  Muna bin misalin Allah.

(Ka kuma duba Fit. 34:14; Isha. 40:28; 1 Kor. 13:​4, 7; 1 Tim. 2:4.)