Za Ka Iya Zaban Yadda Rayuwarka Za Ta Zama
Wajen shekaru 3,500 da suka shige, Allah wanda sunansa shi ne Jehobah ya gaya wa bayinsa abin da za su yi don su ji daɗin rayuwa. Ya ce: “Na shimfiɗa a gabanku rai da mutuwa, albarka da la’ana. Ku zaɓi rai domin ku da zuriyarku ku rayu.”—Maimaitawar Shari’a 30:19.
Allah ya bukace su su yi zaɓin da ya dace don rayuwarsu ta yi kyau. Mu ma zaɓin da ke gabanmu ke nan. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana matakin da za mu ɗauka don mu more rayuwa a nan gaba. Ya ce: “Ku ƙaunaci Yahweh Allahnku, ku yi masa biyayya.”—Maimaitawar Shari’a 30:20.
TA YAYA ZA MU ƘAUNACI JEHOBAH KUMA MU YI MASA BIYAYYA?
BINCIKA LITTAFI MAI TSARKI: Abu na farko da zai taimaka maka ka ƙaunaci Jehobah shi ne bincika Littafi Mai Tsarki don ka san shi da kyau. Idan ka yi hakan, za ka fahimci cewa shi Allah ne mai ƙauna da ke so ka ji daɗin rayuwa. Ya ce ka yi addu’a gare shi domin ‘shi ne mai lura da kai.’ (1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa idan ka ƙoƙarta ka yi kusa da Allah, shi ma “zai yi kusa da kai.”—Yakub 4:8.
KA YI ABIN DA KAKE KOYA: Yin biyayya ga Allah yana nufin mu bi shawarwarin da ya ba mu a Littafi Mai Tsarki. Idan ka yi hakan, “za ka sa hanyarka ta yi albarka, kuma za ka yi nasara.”—Yoshuwa 1:8, Littafi Mai Tsarki.