Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

HASUMIYAR TSARO Na 3 2021 | Me Zai Sa Ka More Rayuwa a Nan Gaba?

Me za ka yi don ka more rayuwa a nan gaba? A wannan mujallar, za a tattauna ra’ayoyin mutane game da wannan batun. Bayan haka, za a bayyana abin da kake bukata ka yi don rayuwarka ta yi kyau a nan gaba.

 

Kowa Yana So Ya More Rayuwa a Nan Gaba

Idan abubuwa marasa kyau suka same mu ba zato, me zai iya taimaka mana?

Me Yake Shafan Yadda Rayuwarmu Za Ta Kasance?

Mutane da yawa da suke duba da taurari da bokaye da masu bauta wa kakanninsu da suka mutu da kuma wadanda suka yi imani da sake haihuwa sun gaskata cewa akwai wasu abubuwa da suke sa su yi sa’a ko rashin sa’a a rayuwa.

Neman Kudi da Ilimi Ne Zai Sa Mu More Rayuwa a Nan Gaba?

Mutane da yawa sun gano cewa neman ilimi ko kudi ba ya sa su more rayuwa.

Idan Muna da Halin Kirki, Shi Ke Nan Rayuwarmu Za Ta Yi Kyau?

Yana da kyau mutum ya zama mai halin kirki, amma hakan ba lallai shi ne zai sa ya more rayuwa a nan gaba ba.

A Ina Za Mu Sami Shawara da Za Ta Sa Mu More Rayuwa?

In muna son mu yi wani abu, mukan nemi shawara daga wanda ya girme mu kuma ya fi mu hikima. A yau ma, za mu sami shawara mai kyau a kan yadda za mu more rayuwa a nan gaba idan muka tuntubi wani da ya girme mu kuma ya fi mu hikima.

Yadda Za Ka More Rayuwa a Nan Gaba

Me kake gani zai sa mutum ya more rayuwa a nan gaba?