Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 11

Yadda Za Ka Amfana Daga Karanta Littafi Mai Tsarki

Yadda Za Ka Amfana Daga Karanta Littafi Mai Tsarki

Ka taɓa tunanin soma wani aiki amma kana ganin yana da wuya? Don aikin ya yi maka sauƙi, wataƙila za ka soma yin sa kaɗan-kaɗan. Haka ma yake da karanta Littafi Mai Tsarki. Kana iya cewa, ‘Ta yaya zan soma wannan gagarumin aiki?’ A wannan darasin, za mu tattauna wasu abubuwa masu sauƙi da za su taimaka maka ka ji daɗin karanta da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki.

1. Me ya sa ya kamata mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana?

Mutumin da yake karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma “koyarwar Yahweh” kowace rana zai yi farin ciki, kuma zai yi nasara. (Karanta Zabura 1:​1-3.) Kana iya somawa ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki na mintoci kaɗan kawai kowace rana. Da zarar ka saba da yin hakan, za ka riƙa jin daɗin karanta Kalmar Allah.

2. Mene ne zai taimaka maka ka amfana daga karanta Littafi Mai Tsarki?

Don mu amfana daga karanta Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu dakata kuma mu yi tunani a kan abin da muke karantawa. Ya kamata mu karanta kuma mu yi “tunani a kansa.” (Yoshuwa 1:8) Sa’ad da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka tambayi kanka: ‘Mene ne wannan ayar ta koya mini game da Jehobah? Ta yaya zan yi amfani da darasin a rayuwata? Ta yaya zan yi amfani da waɗannan ayoyin don in taimaka wa mutane?’

3. Ta yaya za ka sami lokacin karanta Littafi Mai Tsarki?

Yana yi maka wuya ka sami lokacin karanta Littafi Mai Tsarki? Mutane da yawa suna fama da hakan, har da mu ma. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce, mu “yi amfani da kowane zarafi” da muka samu da kyau. (Afisawa 5:16) Kana iya yin hakan ta wajen keɓe lokaci don karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana. Wasu mutane suna karantawa da safe. Wasu suna yin hakan da rana, wataƙila a lokacin cin abincin rana. Wasu kuma suna karanta Littafi Mai Tsarki daddare kafin su yi barci. Wane lokaci ne zai fi dacewa da kai?

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki. Za mu san yadda yin shiri da kyau zai taimaka maka ka amfana sosai daga nazarin Littafi Mai Tsarki.

Kamar yadda za mu iya koyan cin abinci dabam-dabam har mu soma jin daɗinsu, haka ma za mu iya koyan yadda za mu ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki

4. Yadda za ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki

Wataƙila ba zai yi maka sauƙi ka soma karanta Littafi Mai Tsarki ba. Amma za ka iya “marmarin” yin hakan, kamar yadda mutum zai koyi cin abincin da bai taɓa ci ba. Ku karanta 1 Bitrus 2:​2, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, kana ganin za ka ji daɗin karatun kuma ka so ka ci gaba?

Ku kalli BIDIYON nan don ku ga yadda wasu mutane suka soma jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki. Sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, waɗanne matsaloli ne matasan suka magance?

  • Mene ne ya taimaka musu su ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana?

  • Mene ne suka yi don su soma jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki?

Abubuwa da za su taimaka maka:

  • Ka zaɓi juyin Littafi Mai Tsarki da ke da sauƙin fahimta. Za ka iya karanta New World Translation idan ka iya Turanci sosai.

  • Ka soma da wuraren da kake ganin za ka ji daɗin karantawa sosai. Don samun shawarwari, ka duba sashen nan “Ka Soma Karanta Littafi Mai Tsarki.”

  • Ka rubuta wuraren da ka karanta. Ka yi amfani da sashen nan “Ka Saka Maki a Surorin da Ka Karanta” da ke bangon baya na wannan littafin.

  • Ka yi amfani da manhajar JW Library®. Za ka iya yin amfani da wayarka ko wata na’ura don ka karanta ko kuma ka saurari karatun Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa a duk wurin da kake.

  • Ka yi amfani da ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah. Tana ɗauke da taswirori da kuma jadawalai da za su sa ka ji daɗin karatu.

5. Ka yi shiri sosai don nazarin Littafi Mai Tsarki

Ku karanta Zabura 119:​34, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa ya kamata ka yi addu’a kafin ka soma karanta Littafi Mai Tsarki ko kuma shirya yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

Ta yaya za ka amfana daga kowane nazari? Sa’ad da kake shirya kowane darasi a littafin nan, ka bi waɗannan shawarwarin:

  1. Ka karanta sakin layi na ɗaya zuwa uku na wannan darasin.

  2. Ka karanta nassosin da aka ambata kuma ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda suka shafi batun da ake tattaunawa.

  3. Ka ja layi ko ka saka kala a amsar kowace tambaya. Yin hakan zai sa tattauna darasin da malaminka ya yi maka sauƙi.

Ka sani?

Shaidun Jehobah sun yi amfani da juyin Littafi Mai Tsarki dabam-dabam. Amma mun fi son juyin New World Translation of the Holy Scriptures domin yana da sauƙin fahimta kuma akwai sunan Allah a ciki.​—Ka duba wannan talifin jw.org Shaidun Jehobah Suna da Nasu Littafi Mai Tsarki Dabam?

WASU SUN CE: “Karanta da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana da wuya sosai. Ba ni da lokaci ko kuma ƙarfin yin hakan.”

  • Mene ne ra’ayinka?

TAƘAITAWA

Don ka amfana daga nazarin Littafi Mai Tsarki, ka shirya lokacin da za ka riƙa karantawa, ka yi addu’a don ka fahimci abin da ka karanta kuma ka yi shiri sosai don yin nazarin Littafi Mai Tsarki.

Bita

  • Mene ne zai taimaka maka ka amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki?

  • A wane lokaci ne za ka iya karanta kuma ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki?

  • Me ya sa ya dace ka yi shiri don nazarinku?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku yi bitar wasu shawarwarin da muka tattauna da za su taimaka muku ku amfana daga nazarin Littafi Mai Tsarki.

“Yadda Za Ka Ji Daɗin Karanta Littafi Mai Tsarki” (Hasumiyar Tsaro Na 1 2017)

Ku karanta talifin nan don ku koyi hanyoyi uku da za ku iya karanta Littafi Mai Tsarki.

“Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?​—Sashe na 1: Ka Bincika Littafi Mai Tsarki” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan don ku koyi darasi daga mutanen da suka daɗe suna karanta Littafi Mai Tsarki.

Yin Nazari da Kyau (2:06)