Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 57

Me Za Ka Yi Idan Ka Yi Zunubi Mai Tsanani?

Me Za Ka Yi Idan Ka Yi Zunubi Mai Tsanani?

Ko da kana ƙaunar Jehobah sosai, kuma kana iya ƙoƙarinka don kar ka yi abin da zai ɓata masa rai, a wasu lokuta, za ka iya yin kuskure. Amma wasu kurakure suna da tsanani fiye da wasu. (1 Korintiyawa 6:​9, 10) Idan ka yi zunubi mai tsanani, ka tuna cewa Jehobah yana ƙaunar ka har ila, yana shirye ya gafarta maka kuma ya taimaka maka.

1. Mene ne za mu yi don Jehobah ya gafarta mana?

Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna baƙin ciki sosai sa’ad da suka gane cewa sun yi zunubi mai tsanani. Amma Jehobah yana ƙarfafa su da alkawarin da ya yi wa bayinsa cewa: “Ko da kun yi ja wur da zunubi, za ku yi fari fat kamar auduga.” (Ishaya 1:18) Idan mun tuba da gaske, Jehobah zai gafarta mana. Yaya za mu nuna cewa mun tuba? Za mu yi nadama, mu daina yin abin da bai da kyau kuma mu roƙi Jehobah ya gafarta mana. Sai mu yi iya ƙoƙarinmu mu daina tunanin banza ko halayen da suka sa mu yi zunubi. Kuma mu yi ƙoƙari mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodin Jehobah.​—Karanta Ishaya 55:​6, 7.

2. Ta yaya Jehobah yake amfani da dattawa ya taimaka mana idan muka yi zunubi?

Idan mun yi zunubi mai tsanani, Jehobah ya gaya mana cewa mu faɗa wa “dattawan ikilisiya.” (Karanta Yakub 5:​14, 15.) Dattawan nan suna ƙaunar Jehobah da kuma bayinsa. An koya musu yadda za su taimaka mana mu gyara dangantakarmu da Jehobah.​—Galatiyawa 6:1.

Ta yaya dattawa suke taimaka mana idan muka yi zunubi mai tsanani? Dattawa biyu ko uku za su yi amfani da Littafi Mai Tsarki don su nuna mana cewa abin da muka yi ba daidai ba ne. Ban da haka, za su ba mu shawarwari kuma su ƙarfafa mu don su taimaka mana kar mu sake yin zunubin. Suna iya hana mu yin wasu ayyuka a ikilisiya na ɗan lokaci, har sai mun gyara dangantakarmu da Jehobah. Idan mutum ya yi zunubi mai tsanani kuma ya ƙi ya tuba, dattawa za su yi masa yankan zumunci don kar ya ɓata sauran ’yan’uwa a ikilisiya.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za mu nuna godiya ga Jehobah don yadda yake taimaka mana idan muka yi zunubi mai tsanani.

3. Furta zunubanmu zai sa mu gyara dangantakarmu da Allah

Duk zunubin da muka yi yakan ɓata wa Jehobah rai. Saboda haka, ya dace mu gaya masa abin da muka yi. Ku karanta Zabura 32:​1-5, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa zai dace mu gaya wa Jehobah zunubin da muka yi maimakon mu ɓoye shi?

Bayan mun gaya wa Jehobah zunubanmu, za mu sami kwanciyar hankali idan muka nemi taimakon dattawa. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon, ta yaya dattawa suka taimaka wa Canon ya komo ga Jehobah?

Wajibi ne mu gaya wa dattawa gaskiya don za su taimaka mana. Ku karanta Yakub 5:​16, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa zai yi wa dattawa sauƙi su taimaka mana idan muka gaya musu gaskiya?

Ka faɗi zunubin da ka yi, ka gaya wa dattawa gaskiya, kuma ka amince da taimakon Jehobah

4. Amfanin yankan zumunci

Idan mutum ya yi zunubi mai tsanani kuma ya ƙi bin ƙa’idodin Jehobah, ba zai ci gaba da zama Mashaidin Jehobah ba. Za a yi masa yankan zumunci, kuma ba wanda zai yi tarayya da shi ko a yi magana da shi. Ku karanta 1 Korintiyawa 5:​6, 11 da 2 Yohanna 9-11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Kamar yadda yisti yake sa fulawa ta kumbura, ta yaya yin tarayya da wanda ya yi zunubi kuma ya ƙi tuba zai shafi ikilisiya?

Mutane da yawa da aka yi musu yankan zumunci, sun dawo ikilisiya. Me ya sa? Domin horon da aka yi musu ya taimaka musu su gane cewa abin da suka yi ba daidai ba ne. (Zabura 141:5) Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A bidiyon, ta yaya yankan zumuncin da aka yi wa Sonja ya taimaka mata?

Idan aka yi wa mutum yankan zumunci, ta yaya hakan . . .

  • yake ɗaukaka sunan Jehobah?

  • yake nuna cewa Jehobah mai ƙauna ne kuma ya san abin da ya dace da mu?

5. Jehobah yana gafarta mana idan mun tuba

Yesu ya yi amfani da wani misali don mu fahimci yadda Jehobah yake ji idan wani ya tuba. Ku karanta Luka 15:​1-7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne misalin nan ya koya maka game da Jehobah?

Ku karanta Ezekiyel 33:​11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane abu mai muhimmanci ne za mu yi don mu nuna cewa mun tuba da gaske?

Kamar makiyayi, Jehobah ya damu da bayinsa

WASU SUN CE: “Ina tsoron gaya wa dattawa zunubin da na yi, don za su mini yankan zumunci.”

  • Me za ka gaya wa mutumin da yake da irin wannan ra’ayin?

TAƘAITAWA

Idan muka yi zunubi mai tsanani, muka tuba kuma muka yanke shawara cewa za mu daina yin abu marar kyau, Jehobah zai gafarta mana.

Bita

  • Me ya sa yake da kyau mu gaya wa Jehobah zunubanmu?

  • Mene ne muke bukatar mu yi don Jehobah ya gafarta mana zunubanmu?

  • Idan mun yi zunubi mai tsanani, me ya sa muke bukatar mu nemi taimakon dattawa?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Jehobah ya nuna ma wani mutum irin jinƙai da aka kwatanta a Ishaya 1:18.

Jehobah Ya Nuna Min Jin Ƙai (5:02)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda yankan zumunci yake taimaka wa mai zunubi da kuma ’yan’uwa a ikilisiya.

“Me Ya Sa Yankan Zumunci Tsari Ne Mai Kyau?” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Afrilu, 2015)

Ku karanta talifin nan don ku san yadda za ku bayyana wa wanda ba Mashaidi ba ne dalilin da ya sa ake yankan zumunci.

“Kuna Guje wa Mutanen da Suka Bar Addininku?” (Talifin jw.org)

Ku karanta labarin nan “Ina Bukatar Komawa ga Bauta wa Jehobah,” don ku ga dalilin da ya sa wani mutumin da ya daina bauta wa Jehobah, yake ganin cewa Jehobah ne ya dawo da shi.

“Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Afrilu, 2012)