Dakin Watsa Labarai
Kotun Ruwanda Ya Amince da Kasancewar Addinai Dabam-dabam
Wani Kotu a yankin Karongi a Ruwanda ya goyi bayan ’yancin addini wa dalibai takwas da Shaidun Jehobah ne. Shawarar da kotun ya yanke zai iya taimaka a amince da kasancewar addinai dabam dabam a makarantu na kasar Ruwanda kuwa?
Babban Kotun Isra’ila Ya Daukaka ’Yancin Shaidun Jehobah na Yin Babban Taro Cikin Salama
Hukumomin Isra’ila sun yi tir da wariyar addini ta wajen kāre ’yancin Shaidun Jehobah na yin taro don ibada.
Shaidu Sun Yi Kira da A Saki Matan da Aka Tsare a Azerbaijani
Ana tsananta wa Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova kamar yadda ake yi wa masu laifi mai tsanani domin sun yi magana da wasu game da imaninsu. Shin, Azerbaijani za ta nuna cewa tana daukaka ’yancin addini kamar yadda take da’awa?
Shaidun Jehobah Sun Yi Kira da A Daina Tsare ’Yan’uwansu Ba Bisa Ka’ida Ba a Azerbaijani
Shin Azerbaijani za ta ba kowa ’yancin bin addini kamar yadda take da’awa ta wurin sake wadannan mata biyu, wato Irina Zakharchenko da Valida Jabrayilova, kuma ta bar Shaidun Jehobah su yi ibadarsu cikin salama?
Shaidun Jehobah Sun Yi Kamfen na Ilimantar da Mutane Game da Hukuncin ECHR a Georgia
A watan Afrilu 2015, kamfen da aka yi ya sanar da ’yan doka hukuncin da ECHR ya yanke a kwanan nan kuma zai taimaka musu su san hidimomin Shaidun Jehobah.
Wariyar Addini a Azerbaijani Tana Karuwa
Hukumomi suna damun aikin wa’azi na Shaidun Jehobah ta wajen ci musu tara mai yawa da kuma kai su kurkuku. Hukumomin Azerbaijani za su daidaita wannan rashin adalci kuwa?
Lokacin Daukan Mataki Mai Muhimmanci a Kan ’Yancin Addini a Kyrgyzstan
A ranar 24 ga Disamba, 2014, Kotun Koli ya daukaka ’yancin da ’yan kasa suke da shi na bayyana wa wasu abin da suka yi imani da shi, har da Shaidun Jehobah. Shin Shaidun Jehobah a kudancin Kyrgyzstan za su iya samun ’yancin addini yanzu?
Koriya ta Kudu Tana da Alhakin Tsare Mutane a Kurkuku Ba Bisa Ka’ida Ba don Sun Ki Shiga Soja Saboda Imaninsu
A kowace shekara, hukumomi suna tsare darurruwan Shaidu matasa da suka ki shiga soja saboda imaninsu. Sau biyar ke nan Kwamitin Kāre Hakkin ’Yan Adam na Majalisar Dinkin Duniya yake cewa Koriya ta Kudu ba ta da hujjar yin hakan.
Armeniya Ta Yi Nasara Wajen Kafa Aikin Farar Hula
Shaidun Jehobah da suke aiki a karkashin tsarin da abokan aikinsu da darektocinsu da kuma shugabanninsu duk sun yi kalami mai kyau a kan tsarin.
Armeniya Ta Ba Wadanda Suka Ki Shiga Soja Wani Aiki
Kamar dai idon gwamnatin Armeniya ya bude yanzu da ta soma amincewa da ’yancin da mutane suke da shi na ki da aikin soja saboda imaninsu. An ba wasu Shaidun Jehobah damar yin aikin farar hula a maimakon aikin soja.
Rashin Adalci a Kasar Koriya ta Kudu ta Jawo Rashin Amincewar Kasashen Duniya
Sabuwar kasida da Shaidun Jehobah suka wallafa ta bayyana rashin adalci da ake yi wa darurruwan matasa da suka ki aikin soja a kan imaninsu ta wajen tsare su a kurkuku.

