5 GA FABRAIRU, 2015
ARMENIA
Armeniya Ta Yi Nasara Wajen Kafa Aikin Farar Hula
Armeniya ta yi nasara shekara daya bayan da ta kafa tsarin yin aikin farar hula maimakon shiga soja. Matasa maza na farko da suka yi aiki a karkashin wannan tsarin Shaidun Jehobah ne, kuma suna yin ayyuka dabam-dabam don amfanin jama’a maimakon su tafi kurkuku don sun ki yin aikin soja saboda imaninsu.
Tun shekara ta 1985, an ki ba wa Shaidun Jehobah damar yin wani abu dabam maimakon kai su kurkuku a duk lokacin da suka ki yin aikin soja saboda imaninsu. Domin babu wata dokar da ta tanadar musu da aikin farar hula a maimakon aikin soja, a cikin tsawon shekaru 20 an tsare Shaidun Jehobah guda 450 a cikin matsanancin yanayi. Amma wannan yanayin ya canja a watan Yuni, 2013 a lokacin da Armeniya ta yi gyara ga Tsarin Dokokinta a Kan Yin Aikin Farar Hula a Maimakon Aikin Soja.
A ranar 23 ga Oktoba, 2013 ne Armenian Republican Committee (Kwamitin Jamhuriyar Armeniya) ya fara ba da dama ga mutane 57 daga cikin wadanda suka nemi su yi aikin farar hula a maimakon aikin soja. Dukan wadanda suka nemi wannan aikin Shaidun Jehobah ne. a Daga baya kwamitin ya ba wasu Shaidu wannan damar. Matasa maza Shaidun Jehobah guda saba’in da daya ne suka soma wannan aikin a mako na uku a watan Janairu, 2014. Daga wannan lokacin zuwa karshen 2014, Shaidu guda 126 ne suka sami damar yin aikin farar hula dabam-dabam a maimakon aikin soja.
Nasara da Aka Samu a Tsarin
Furucin darektoci da shugabanni da kuma abokan aikin wadanda suka yi irin wannan aikin ya nuna cewa wannan tsarin tana samun nasara sosai. Mutanen nan sun lura da halin kirki da Shaidun suka nuna da yadda suke taimakon mutane da kuma yadda suke aiki da kwazo. Mambobin Kwamitin da dama sun ce Shaidun da suke yin wadannan ayyukan suna yin hakan da dukan zuciyarsu kuma suna taimaka wa gwamnatin Armeniya sosai.
“Kuna yi wa wannan kasar hidima mai kyau ko da yake albashi kadan ne kawai ake biyanku. Babu shakka, kuna aiki tukuru.”—Shugaban Yerevan/Shengavit Community Services.
“Wannan aikin ya dace da ku domin kuna kokari ku yi rayuwar da ta jitu da ka’idodin Kirista kuma kuna yin abin da zai amfani jama’a!”—Nas a wani gidan marayu da aka aika Shaidu su yi hidima.
“Akwai wasu kuma masu halin kirki kamar ku? Su zo su yi mini aiki!”—Darekta a Yerevan/Arabkir Community Services.
Shaidu da aka ba su damar yin aikin farar hula ma sun yi kalamai masu kyau a kan tsarin.
“Abokan aikina suna kaunata kuma suna girmama ni sosai. Akwai ranar da na yi rashin lafiya har na kasa zuwa aiki, kuma abokan aikina suka kira ni don su gai da ni. Ina farin cikin yin aiki a karkashin wannan tsarin domin yana ba ni damar bauta wa Allah hankali kwance.”—Gevorg Taziyan, wanda aka ba shi damar yin hidima a matsayin Direba na Biyu a Territorial Division of the Ministry of Emergency Situations Rescue Services.
“A wurin aikinmu muna da dangantaka mai kyau tsakanin shugabanninmu da kuma masu yi musu aiki. Muna kokari mu faranta musu rai don yadda suke kulawa da mu. Akwai lokatan da suke ba mu ayyuka da asali ba sa cikin aikin da ya kamata mu yi, amma muna taimaka musu mu yi ayyukan.”—Samvel Abrahamyan, wanda aka ba shi aiki a matsayin mai kula da furanni a Sevan Psychiatric Hospital.
“Mu guda 13 ne muka soma aiki da Ministry of Emergency Situations a ranar 14 ga Janairu, 2014. Tun daga wannan ranar har zuwa yau, mun ji dadin cudanya da kowa a wurin aikinmu. Ba mu taba gardama da shugabanninmu ba. Yadda muke da hadin kai a wurin aikinmu yana burge su sosai.”—Artsrun Khachatryan, wanda aka ba shi aiki a matsayin mai kula da furanni a Ministry of Emergency Situations.
Abin da ya sa tsarin yin aikin farar hula a maimakon aikin soja a Armeniya ya yi nasara shi ne, darektoci da shugabanni da ke kula da ayyukan suna da hadin kai kuma Shaidun Jehobah da suke aiki a karkashin wannan tsarin suna da halin kirki kuma suna aiki da kwazo. Shaidun Jehobah a Armeniya suna godiya domin ba za a sake kai su kurkuku saboda imaninsu ba, kuma an ba su damar yi wa kasarsu hidima ba tare da saba wa imaninsu ba.
a Don karin bayani, ka duba talifin nan “Armeniya Ta Ba Wadanda Suka Ki Shiga Soja Wani Aiki”