Koma ka ga abin da ke ciki

23 GA MARIS 2015
Azerbaijan

Wariyar Addini a Azerbaijani Tana Karuwa

Wariyar Addini a Azerbaijani Tana Karuwa

Yadda hukumomi suke ci wa Shaidun Jehobah tara mai yawa da kuma yadda suke jefa su a kurkuku ya sa wariyar addini tana karuwa a Azerbaijani. Hukumomi suna hukunta Shaidun Jehobah don yin taron ibada da kuma bayyana wa mutane abin da suka yi imani da shi.

Yin Ayyukan Ibada Ya Zama Laifi

Shaidun Jehobah guda biyu, Irina Zakharchenko wata gwauruwa nakassashiya mai shekara 55 da kuma Valida Jabrayilova mai shekara 38, wadda ita ce ke kula da mahaifiyarta, sun je wa’azi a wani gida a Baku a ranar 5 ga Disamba, 2014. A lokacin suna rarraba wa mutane kasidar nan Ku Koyar da Yaranku don taimaka wa iyaye su koya wa yaransu labaran Littafi Mai Tsarki. a

Wani dan sanda mai bincike ya kama su kuma ya tuhume su da laifin rarraba littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki ba “tare da izini ba.” An yanke musu hukuncin tara da ta kai dalla 6,690 zuwa dalla 8,600 b ko kuma zaman kurkuku na tsawon shekara biyu zuwa biyar.

Ma’aikatar Tsaro ta Kasa (MNS) ta yi wa matan tambayoyi sau da sau. A ranar 17 ga Fabrairu, 2015, MNS ta kira matan don a yi musu tambayoyi amma da matan suka isa wurin sai suka ga cewa ana tuhumarsu da laifi a Kotun Gunduma da ke Sabail a Baku, kuma aka yi musu shari’a ba tare da barin jama’a su saurari shari’ar ba.

Bayan da dan sanda mai yin binciken ya ba da hujjojinsa, sai ya nemi damar tsare matan a inda ake tsare masu jiran shari’a domin a ganinsa matan za su sake aikata laifin kuma “su boye.” Lauyan da ke kāre matan ya ce hujjojin da dan sandan ya bayar ba su taka kara ya karya ba domin matan ba su taba jayayya da hukuma ba. Ko da yake alkalin ya ce ba a taba tuhumar wadannan matan da wani laifi ba, amma ya ce hidimar da suke yi “barazana ce ga jama’a” saboda haka ya ba da dama a tsare su a kurkuku na tsawon watanni uku a karkashin kulawar ’yan sandan ciki.

Lauyan matan ya daukaka karar, sai a ranar 26 ga Fabrairu, 2015 ’yan sanda suka kai su kotun afil na Baku a cikin wata mota mai bakar gilashi kuma aka saka musu ankwa a hannu. A lokacin da ake shari’ar, wanda ya shigar da karar da dan sandan MNS da yake binciken sun kasa ba da kwararrun hujjoji na tsare matan a inda ake ajiye masu jiran shari’a. Duk da haka, kotun ya yarda da abin da mai shigar da karar da kuma dan sanda mai yin binciken suka fada kuma aka mayar da Malama Zakharchenko da Malama Jabrayilova kurkuku.

A ranar 6 ga Maris 2015, kotu ya ba rukunoni biyu daga MNS izini su bincika gidajen Malama Zakharchenko da Malama Jabrayilova kuma sun kwace littattafan addini da littattafan rubutu da kwamfutar tafi-da-gidanka da kuma wayar salula. A ranar 10 ga Maris, 2015, wasu ma’aikata da suke wakiltar MNS da wakilan State Committee for Work with Religious Associations da kuma ’yan sanda suka je yin bincike a Majami’ar Mulki (wurin sujjada) da gidan wani dattijo a ikilisiyar matan. Kari ga haka, ma’aikatar MNS ta kira Shaidun Jehobah da dama a Baku don ta bincike su a kan wannan batun.

Shaidun Jehobah sun rubuta wasika zuwa ga UN Special Rapporteur on freedom of religion or belief da kuma Working Group on Arbitrary Detention a kan yadda aka tsare Malama Zakharchenko da Malama Jabrayilova kuma sun nemi su sa baki a batun. Lauyan da ke kāre matan shirya ya shigar da kara don a tsare matan a gidajensu maimakon a ci gaba da tsare su a inda masu jiran shari’a suke.

Ana Ci wa Mutane Tara Mai Yawa Kuma Ana Tsare Su a Kurkuku don Halartan Taron Ibada

Hukumomi a Ganja sun ci wa mutane da suke halartan taron Shaidun Jehobah tara mai yawa har ma sun tsare wasu a kurkuku. Tarar ta kama daga dalla 1,433 zuwa dalla 1,911.

A watan Oktoba 2014, kotuna a Ganja sun tsare Shaidun Jehobah guda uku tare da wani mutum da ya je ibada da su a kurkuku domin sun kasa biyan tarar da aka ci su a baya. Duk da cewa sun riga sun biya rabin tarar da aka ci su, hukumomi sun tsare su a kurkuku na tsawon kwanaki 3 zuwa 20.

Mutumin da ya je ibada tare da Shaidun Jehobah ya ce: “Dalla 1,433 kudi ne mai yawa a gare ni. . . . A farko, ban so in biya kudin ba domin ban ga laifin da na yi ba.” Shaidu guda biyu da aka tsare ma sun ce tsare su da aka yi ba adalci ba ne kuma sun ce hukumomin sun wulakanta su kamar masu aikata laifi.

Mashaidiyar da aka tsare tare da mazan ta ce: “Babu wanda ya damu cewa iyalinmu suna cikin talauci mai tsanani ko kuwa ni ce mai kula da mahaifiyata da ta nakasa ko kuma na soma biyan tarar da son raina.”

Wadannan mutanen hudu sun riga sun gama zaman kurkuku amma kotun yana kan nacewa cewa sai sun biya dukan tara da aka yi musu. Idan ba su biya sauran kudin a cikin lokacin da kotun ya kayyade ba, kotun zai iya sa a mai da su kurkuku.

Shin Azerbaijani Za Ta Yi Adalci?

Ma’aikata a Azerbaijani suna amfani da hanyoyi dabam-dabam don su hana Shaidun Jehobah yin wa’azi a kasar. A yanzu haka, Shaidun Jehobah sun shigar da kararraki guda 19 a kan Azerbaijani kuma suna jiran Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya warware batun wariya da suke fuskanta. Kafin wannan lokacin, Shaidun Jehobah suna sa rai ko hukumomin Azerbaijani za su gyara kuskuren da aka yi wajen tsare Malama Zakharchenko da Malama Jabrayilova a inda ake tsare masu jiran shari’a. Idan Azerbaijani ta daidaita wannan batun da kuma sauran batutuwan da suka shafi wariyar addini, za ta nuna cewa tana daraja ’yan kasarta da tsarin dokar kasarta, kuma tana goyon bayan ’yancin ’yan Adam.

a State Committee for Work with Religious Associations na Jamhuriyar Azerbaijani ne ya ba da izini a ranar 11 ga Agusta, 2014 don a shigar da wannan kasidar da Shaidun Jehobah suka wallafa.

b A watan Agusta 2014 an kimanta cewa avirejin albashi da ake biya a wata a Azerbaijani shi ne dalla 420.