Koma ka ga abin da ke ciki

19 GA FABRAIRU, 2015
South Korea

Koriya ta Kudu Tana da Alhakin Tsare Mutane a Kurkuku Ba Bisa Ka’ida Ba don Sun Ki Shiga Soja Saboda Imaninsu

Koriya ta Kudu Tana da Alhakin Tsare Mutane a Kurkuku Ba Bisa Ka’ida Ba don Sun Ki Shiga Soja Saboda Imaninsu

Kwamitin Kāre Hakkin ’Yan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya kama gwamnatin Koriya ta Kudu da laifin tsare mutane a kurkuku ba bisa ka’ida ba a kan su ki shiga soja saboda imaninsu, kuma ta hakan, gwamnati ta keta ’yancinsu na bin lamirinsu. Wannan ne hukunci na biyar da Kwamitin ya yanke a kan Koriya ta Kudu don tsare mutane a kurkuku, amma wannan ne lokaci na farko da ya ce hakan “ba bisa ka’ida ba.” a

A hukunci guda hudu da Kwamitin ya yanke game da mutane 501 da suka ki su shiga soja, Kwamitin ya ce Koriya ta Kudu ta keta ’yancinsu na yin tunani da ’yancin bin lamiri da kuma addini kamar yadda yake cikin Talifi na 18 a yarjejeniyar International Covenant on Civil and Political Rights (ICCPR). Wannan hukuncin da aka yanke da ya shafi matasa Shaidu 50 a ranar 15 ga Oktoba, 2014 kuma aka sanar wa jama’a a ranar 14 ga Janairu, 2015 ya ba da karin bayani sosai. b Kwamitin ya ce ta wajen tsare wadannan matasa a kurkuku, gwamnati ta saba wa Talifi na 9 na ICCPR, wanda ya hana tsare mutane ba bisa ka’ida ba kuma ya ce wadanda aka tsare suna da ’yanci su bukaci a biya su diyya. Kwamitin ya ce ya kamata a fahimci cewa yin abubuwa da “‘ba bisa ka’ida ba’ ya kunshi rashin adalci [da] kuma taka doka.” Ya karasa da cewa, bisa ga talifi na 18 na yarjejeniyar ICCPR “tsare mutane don sun bi ’yancinsu na bin addini da kuma lamiri ya saba wa ka’ida.”

Hakkin Daidaita Batun

Kwamitin ya gaya wa gwamnatin Koriya ta Kudu cewa ta cire sunayen Shaidu guda 50 din daga cikin masu aikata laifi kuma su biya su diyya da ya kamata. Ya kara da cewa gwamnati “tana da hakkin [kafa] dokokin da za su ba kowa ’yancin kin aikin soja saboda imaninsa.” Cikin kwanaki 180 da aka yanke wannan hukuncin, ana bukatar Koriya ta Kudu “ta ba da bayani game da matakin da ta dauka don ta bi wannan Dokar.”

Sau da sau Koriya ta Kudu ta ki ta kafa wannan doka domin ta ce ana yin barazana ga tsaron kasarta kuma ba dukan ’yan kasar ba ne suka yarda a ba da damar yin aikin farar hula a maimakon na soja. Sau biyar ke nan Kwamitin yake yin watsi da hujjoji da gwamnatin take bayarwa a kan wannan batun kuma a kowane lokaci kwamitin yana maimaita Dokar da ya bayar a shekara ta 2006. A wannan Dokar, Kwamitin ya ce Koriya ta Kudu ta “kasa ba da kwararrun hujjoji da suka nuna cewa ba wa kowa ’yancinsa zai yi mummunan tasiri a kan kasar.” A batun zaman lafiya, Kwamitin ya ce “idan kasa ta amince cewa kowa yana da ’yanci ya bi imanin da ya ga dama da ka’idodinsa, hakan zai taimaka wa mutane su zauna lafiya duk da cewa kowa na da bambancinsa.” Saboda haka, Kwamitin ya dāge cewa Koriya ta Kudu ba ta da hujjar tsare wadanda suka ki shiga soja saboda imaninsu.

Ta wajen tsare mutane domin sun ki su shiga soja, Koriya ta Kudu ta ki bin dokokin kasa da kasa a kan wannan batun. Hakan ya saba wa ka’ida.

Ko da yake Koriya ta Kudu ta sa hannu a yarjejeniyar ICCPR a shekara ta 1990, ta ki bin sharudan yarjejeniya da aka yi game da ’yancin kin yin wani abu saboda imani. Hukumomin Koriya sun ci gaba da tsare darurruwan Shaidu matasa a kowace shekara. Kwamitin Kāre Hakkin ’Yan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi magana sau da sau a madadin wadanda suka ki shiga soja saboda imaninsu a Koriya ta Kudu. Da shigewar lokaci za mu ga ko gwamnati za ta daina tsare mutane a kurkuku ba bisa ka’ida ba kuma ta tsara dokar da za ta daukaka ’yancin kowane dan kasarta.

a Ka duba yarjejeniyar CCPR Communication No. 2179/2012, Young-kwan Kim et al. v. Republic of Korea, Dokokin da aka kafa a ranar 15 ga Oktoba, 2014, sakin layi na 7.5.

b Hoton Shaidu matasa 30 daga cikin 50 da suka daukaka kara zuwa Kotun Koli na Koriya ta Kudu, a tsaye a gaban kotun.