Koma ka ga abin da ke ciki

Yana da Kyau Kiristoci Su Yi Amfani da Maganin Hana Haihuwa?

Yana da Kyau Kiristoci Su Yi Amfani da Maganin Hana Haihuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Yesu bai umurci mabiyansa su haifi ko kada su haifi ’ya’ya ba. Babu wani cikin almajiran Yesu da ya ba da wannan umurnin. Babu wani waje cikin Littafi Mai Tsarki da aka haramta maganin hana haihuwa. Saboda haka, ƙa’idar nan da ke Romawa 14:12 zai dace: “Kowane ɗayanmu fa za ya kawo lissafin kansa ga Allah.”

 Saboda haka, ma’aurata suna iya shawarta su haifi ’ya’ya ko kuma su ƙi haihuwa. Suna iya tsai da shawarar yara nawa za su haifa da kuma lokacin da za su haife su. Idan miji da mata sun yi amfani da maganin hana haihuwa wanda ba na zub da ciki ba ne don kada su haihu, zaɓensu ne kuma za su ɗauki nauyin. Kada wani ya shar’anta su.—Romawa 14:4, 10-13.