Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Hell? Wajen Madawwamin Azaba ne?

Mene ne Hell? Wajen Madawwamin Azaba ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar nan “hell” a madadin kalmar Ibranancin nan “Sheol” da ta yi daidai da “Hades” a Helenanci da suke nufin kabari. (Zabura 16:10; Ayyukan Manzanni 2:27) Mutane da yawa sun gaskata da wutar hell, kamar yadda aka nuna cikin hoton da ke wannan talifin. Amma, Littafi Mai Tsarki bai koyar da haka ba.

  1.   Wadanda suke hell ba su san kome ba saboda haka ba sa shan azaba. ‘Gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.’​—Mai-Wa’azi 9:5,​10.

  2.   Mutane masu aminci suna hell. Mutane masu aminci irin su Yakubu da Ayuba ma suna wurin.​—Farawa 37:35; Ayuba 14:13.

  3.   Mutuwa ce sakamakon zunubi, ba azaba cikin wutar hell ba. “Wanda ya mutu ya kubuta daga zunubi.”​—Romawa 6:7.

  4.   Madawwamiyar azaba ba daidai take da tafarkin adalci na Allah ba. (Kubawar Shari’a 32:4) Sa’ad da mutum na farko Adamu ya yi zunubi, Allah ya ce masa zai mutu: “Turbaya ne kai, ga turbaya za ka koma.” (Farawa 3:​19) Zai zama cewa Allah ya yi karya ke nan idan ya jefa Adamu cikin wuta.

  5.   Allah bai taba tunanin madawwamiyar azaba ba. Wannan ra’ayi na cewa zai hukunta mutane cikin wutar hell ya saba da koyarwar Littafi Mai Tsarki da ya ce “Allah kauna ne.”​—1 Yohanna 4:8; Irmiya 7:​31.