Koma ka ga abin da ke ciki

Su Wa Za Su Shiga Hell?

Su Wa Za Su Shiga Hell?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Hell wato, “Sheol” ko “Hades” a cikin asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki yana nufin kabari, ba wurin shan azaba ba ne. Su wa za su shiga hell ? Mutanen kirki da marasa kirki. (Ayuba 14:13; Zabura 9:17) Littafi Mai Tsarki ya ce kabari “gidan taruwa da aka sanya ma dukan masu-rai” ne.—Ayuba 30:23.

Yesu ma ya je hell sa’ad da ya mutu. Amma, ‘ba a bar shi cikin hell ba,’ saboda Allah ya ta da shi.—Ayyukan Manzanni 2:31, 32.

Ana iya fitowa daga hell kuwa?

Da ikon Allah Yesu zai ta da dukan wadanda suke hell. (Yohanna 5:28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15) Ga abin da annabcin da ke Ru’ya ta Yohanna 20:13 ya ce game da tashin matattu: “Mutuwa da hades [hell] kuma suka ba da matattun da ke cikinsu.” Idan Hell ya ba da matattun da ke cikinsa, babu wanda zai je wurin kuma saboda “mutuwa kuwa ba za ta kara kasancewa ba.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4; 20:14.

Ba dukan mutanen da suka mutu ne ke shiga hell ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wasu mutane suna mugunta sosai kuma ba sa son su canja halinsu. (Ibraniyawa 10:26, 27) Idan irin wadannan suka mutu, ba hell za su ba, amma Gehenna za su shiga, wato, alamar madawwamiyar halaka. (Matta 5:29, 30) Alal misali, sa’ad da Yesu yake duniya ya ambata cewa, wasu munafukai shugabannin addini za su shiga Gehenna.—Matta 23:27-33.