Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne ke Faruwa da Kai Sa’ad da Ka Mutu?

Mene ne ke Faruwa da Kai Sa’ad da Ka Mutu?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba.” (Mai-Wa’azi 9:5; Zabura 146:4) Saboda haka, sa’ad da muka mutu, mun daina wanzuwa ke nan. Matattu ba su tunani, ba sa iya kome ko kuma su ji wani abu.

“Ga turbaya za ka koma”

 Allah ya bayyana wa mutum na farko, wato Adamu, abin da zai faru da mu sa’ad da muka mutu. Domin Adamu ya yi rashin biyayya, Allah ya ce masa: “Turbaya ne kai, ga turbaya za ka koma.” (Farawa 3:19) Adamu bai wanzu a wani wuri ba kafin Allah ya halicce shi “daga turbayar kasa.” (Farawa 2:7) Haka nan kuma, lokacin da Adamu ya mutu, ya zama turbaya kuma ya daina wanzuwa.

 Abin da ke faruwa yanzu ke nan da wadanda suka mutu. Sa’ad da Littafi Mai Tsarki yake magana game da abin da ke faruwa da mutane da kuma dabbobi ya ce: “Dukansu biyu daga turbaya suka fito, dukansu biyu kuma za su koma cikinta.”—Mai-Wa’azi 3:19, 20, Littafi Mai Tsarki.

Mutuwa ba ita ce karshen kome ba

 Sau da yawa Littafi Mai Tsarki yana kwatanta mutuwa da barci. (Zabura 13:3; Yohanna 11:11-14; Ayyukan Manzanni 7:60) Mutumin da yake barci mai nauyi ba ya sanin abin da ke faruwa. Haka nan ma, matattu ba su san kome ba. Har ila, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Allah zai ta da matattu kamar yadda ake ta da mutum daga barci kuma ya ba su rai. (Ayuba 14:13-15) Mutuwa ba ita ce karshen kome ba ga wadanda Allah zai tayar da su.