Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Nawa Ne a Fadin Duniya?

Shaidun Jehobah Nawa Ne a Fadin Duniya?

Rahoto na Shekarar Hidima * na 2020

Adadin Shaidun Jehobah a dukan duniya

8,695,808

Ikilisiyoyi

120,387

Kasashen da Shaidun Jehobah suke wa’azi

240

Su waye ne kuke dauka a matsayin mambobinku?

Wadanda suke wa’azin bisharar Mulkin Allah a kowace wata ne kawai muke kirgawa a matsayin Shaidun Jehobah. (Matta 24:14) Wannan ya kunshi wadanda suka yi baftisma a matsayinsu na Shaidu da kuma wadanda da ba su yi baftisma ba amma sun cancanci su yi wa’azin bishara.

Shin sai mutum ya ba da gudummawar kudi kafin ya zama memba?

A’a. Ba sai mutum ya ba da gudummawar kudi ko kuma sai ya samu wani aiki ko gata na musamman kafin a kirga shi a matsayin Mashaidi a kungiyarmu ba. (Ayyukan Manzanni 8:18-20) Hakika, ba a sanin lokacin da ake ba da yawancin gudummawar ba. Kowane Mashaidi yana ba da lokacinsa da kuzarinsa da kuma dukiyoyinsa ga aikinmu da ake yi a dukan duniya daidai da abin da yake so ya bayar da kuma yanayinsa.—2 Korintiyawa 9:7.

Ta yaya kuke sanin adadin mutane da suke wa’azi?

Kowace wata, Shaidun Jehobah suna ba da rahoton wa’azin da suka yi a ikilisiyarsu. Suna ba da wannan rahoton da son ransu ba sai an tilasta musu ba.

Ana hada adadin rahoton kuma a tura zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke kasar. Sai ofishin ya tura adadin kowace kasa ko yanki zuwa hedkwatarmu.

A karshen kowace shekarar hidima, ana kirga adadin Shaidun Jehobah da ke kowace kasa a shekarar. Sai a hada wannan adadin don a san adadin Shaidu da suke dukan fadin duniya. Ana wallafa rahoto na kowace kasa, har da labarai na wa’azin bishara da aka yi a cikin littafin nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses. Wadannan rahotanni suna karfafa mu, kamar yadda irin wadannan rahotanni suka karfafa Kiristoci na farko.—Ayyukan Manzanni 2:41; 4:4; 15:3.

Shin kuna kirga wadanda suke tarayya da kungiyarku amma ba sa wa’azi?

Ko da yake ba ma kirga irin wadannan mutane a adadin Shaidun Jehobah ba, muna marabtarsu sosai a ikilisiyoyinmu. Tun da yake yawancinsu suna halartan taron Tuna da Mutuwar Kristi, ana iya sanin adadinsu ta wajen kirga adadin wadanda suka halarci wannan taro da adadin Shaidun Jehobah. A shekara ta 2020, mutane 17,844,773 ne suka halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu.

Mutane da yawa da ba sa halartan taronmu suna amfana daga nazarin da Shaidun Jehobah suke yi da su a gidajensu kyauta. A shekara ta 2020, a kowace wata mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane akalla 7,705,765. Kari ga haka, an yi wasu cikin wadannan nazarin da mutane da yawa a lokaci daya.

Me ya sa yawan Shaidun Jehobah da gwamnati ta lissafta ya fi naku yawa?

Kungiyar kirge ta gwamnati takan sami adadinsu ta wurin tambayar mutane rukunin addinin da suke bi. Alal misali, kungiyar kirge na Amirka, wato U.S. Census Bureau ta ce “sukan nemi su sani ko mutane suna daukan kansu mabiyan wasu addinai,” kuma sun dada cewa adadin da suka samu ya dangana ne ga “ra’ayin mutane ba bisa ga ainihin addini da suke bi ba.” Maimakon haka, muna kirga wadanda suke wa’azi kuma suka ba da rahoton aikinsu kawai, ba wadanda suke da’awa cewa su Shaidun Jehobah ne.

^ sakin layi na 2 Muna kirga shekarar hidima daga ranar 1 ga Satumba zuwa ranar 31 ga Agusta na wata shekara. Alal misali, shekarar hidima ta 2015 ta soma daga ranar 1 ga Satumba, 2014 zuwa ranar 31 ga Agusta, 2015.