Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Shaidun Jehobah Suka Gaskata?

Mene ne Shaidun Jehobah Suka Gaskata?

 A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna kokari mu bi tsarin addinin Kirista da Yesu ya kafa, wanda manzanninsa suka bi. Wannan talifin yana dauke da muhimman abubuwa da muka yi imani da su a takaice.

 1.   Allah. Muna bauta wa Madaukakin Sarki, Allah na gaskiya wanda ya halicci dukan abubuwa. Sunansa Jehobah. (Zabura 83:18; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Shi ne Allahn Ibrahim da Musa da kuma Yesu.—Fitowa 3:6; 32:11; Yohanna 20:17.

 2.   Littafi Mai Tsarki. Mun dauki Littafi Mai Tsarki a matsayin hurarriyar Kalmar Allah ga ’yan Adam. (Yohanna 17:17; 2 Timotawus 3:16) Mun yi imani da dukan littattafai 66 da ke cikin Littafi Mai Tsarki, wanda ya kunshi “Tsohon Alkawari” da “Sabon Alkawari.” Wani Farfesa mai suna Jason D. BeDuhn ya rubuta cewa Shaidun Jehobah sun dauko abubuwan da suka yi imani da su daga ainihin koyarwar Littafi Mai Tsarki, ba daga abubuwan da suke tsammani ba.” a

   Ko da yake mun yi imani da dukan abubuwan da ke cikin Littafi Mai Tsarki, ba mu yarda cewa dukan abubuwan da ke ciki Littafi Mai Tsarki suna da ma’ana ta zahiri ba. Mun san cewa an yi bayanin wasu sassan Littafi Mai Tsarki a alamance. Saboda haka, bai kamata mu dauka cewa suna da ma’ana ta zahiri ba.—Ru’ya ta Yohanna 1:1.

 3.   Yesu. Muna bin koyarwar Yesu Kristi da misalinsa, kuma muna daukaka shi a matsayin Mai cetonmu da kuma Dan Allah. (Matta 20:28; Ayyukan Manzanni 5:31) Saboda haka, mu Kiristoci ne. (Ayyukan Manzanni 11:26) Amma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Yesu ba Allah Madaukakin Sarki ba ne kuma ba Littafi Mai Tsarki ba ne tushen koyarwar allah-uku-cikin-daya.—Yohanna 14:28.

 4.   Mulkin Allah. Wannan gwamnati ce ta kwarai da aka kafa a sama, ba wani yanayi da ke zukatan Kiristoci ba. Mulkin zai sauya gwamnatoci ’yan Adam kuma zai sa nufin Allah ga duniyar nan ta cika. (Daniyel 2:44; Matta 6:9, 10) Ba da dadewa ba gwamnatin nan za ta yi wadannan abubuwa da aka ambata domin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa muna rayuwa ne a “kwanaki na karshe.”—2 Timotawus 3:1-5; Matta 24:3-14.

   Yesu shi ne Sarkin Mulkin Allah a sama. Ya soma sarauta a shekara ta 1914.—Ru’ya ta Yohanna 11:15.

 5.   Ceto. Fansar Yesu ne kadai zai iya sa mutane su sami ceto. (Matta 20:28; Ayyukan Manzanni 4:12) Idan mutane suna so su amfana daga wannan fansa, wajibi ne su yi imani da Yesu, su canja salon rayuwarsu kuma su yi baftisma. (Matta 28:19, 20; Yohanna 3:16; Ayyukan Manzanni 3:19, 20) Abubuwan da mutum yake yi ne za su nuna cewa yana da bangaskiya. (Yakub 2:24, 26) Amma za mu sami ceto saboda “alherin Allah” ne ba saboda ayyukanmu ba.—Galatiyawa 2:16, 21.

 6.   Sama. Jehobah Allah da Yesu Kristi da dukan mala’iku masu aminci suna zama a sama. b (Zabura 103:19-21; Ayyukan Manzanni 7:55) Za a ta da mutane kadan ne, wato 144,000, zuwa sama domin su yi sarauta da Yesu a cikin Mulkinsa.—Daniyel 7:27; 2 Timotawus 2:12; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1, 3.

 7.   Duniya. Allah ya halicci duniya don ’yan Adam su zauna a ciki har abada. (Zabura 104:5; 115:16; Mai-Wa’azi 1:4) Allah zai ba wa wadanda suka yi masa biyayya koshin lafiya da kuma rai na har abada a cikin aljanna a duniya.—Zabura 37:11, 34.

 8.   Mugunta da wahala. An soma mugunta da wahala sa’ad da wani mala’ikan Allah ya yi tawaye. (Yohanna 8:44) Bayan ya yi tawaye, an soma kiran wannan mala’ikan “Shaidan” da kuma “Iblis” kuma ya yaudare iyayenmu na farko su yi wa Allah rashin biyayya. Hakan ya jawo mummunan sakamako ga ’yan Adam. (Farawa 3:1-6; Romawa 5:12) Allah ya kyale mugunta da wahala domin yana so ya daidaita batun da Shaidan ya tayar game da wanda ya cancanci ya yi sarauta, amma ba zai bar hakan ya ci gaba har abada ba.

 9.   Mutuwa. Mutanen da suka mutu sun daina wanzuwa. (Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:5, 10) Ba sa shan wahala a cikin wutar jahannama.

   Allah zai ta da biliyoyin mutanen da suka mutu don su sake rayuwa. (Ayyukan Manzanni 24:15) Amma za a hallaka wadanda suka ki su bi ka’idodin Allah bayan an ta da su daga mutuwa.—Ru’ya ta Yohanna 20:14, 15.

 10.   Iyali. Muna bin ka’ida na asali da Allah ya kafa game da aure a matsayin dangantaka tsakanin namiji da tamace, kuma zina ne kawai dalilin da zai sa a kashe aure. (Matta 19:4-9) Mun tabbata cewa bin shawarwari masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su taimaka wa iyalai su zauna lafiya.—Afisawa 5:22–6:1.

 11.   Ibadarmu. Ba ma amfani da giciye da dai sauran sifofi a sujjada. (Kubawar Shari’a 4:15-19; 1 Yohanna 5:21) Muhimman abubuwa da muke yi a ibadarmu su ne:

 12.   Kungiyarmu. Muna cikin ikilisiyoyi dabam-dabam kuma rukunin dattawa ne ke kula da kowace ikilisiya. Amma wadannan dattawan ba limamai ba ne kuma ba a biyansu. (Matta 10:8; 23:8) Ba ma karban zaka da kuma baiko a taronmu. (2 Korintiyawa 9:7) Muna gudanar da ayyukanmu ta gudummawar da mutane suke bayarwa da son rai, kuma masu ba da gudummawar ba sa bayyana kansu.

   Wani rukunin Kiristoci da suka manyanta da ake kira Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da ke hedkwatarmu ne suke ja-gorar ayyukan Shaidun Jehobah a fadin duniya.—Matta 24:45.

 13.   Hadin kai. Ko da yake muna wurare dabam-dabam a fadin duniya, muna da fahimta daya game da koyarwar Littafi Mai Tsarki. (1 Korintiyawa 1:10) Muna aiki tukuru don mu kawar da kabilanci da wariyar launin fata da dai sauransu. (Ayyukan Manzanni 10:34, 35; Yakub 2:4) Duk da cewa muna da hadin kai, kowane mutum yana iya kasancewa da ra’ayin da ya bambanta da na wani, saboda haka kowane yana iya yanke nasa shawara a kan ka’idodin da ba su shafi Littafi Mai Tsarki ba.—Romawa 14:1-4; Ibraniyawa 5:14.

 14.   Halinmu. Muna kaunar dukan mutane da muke hulda da su. (Yohanna 13:34, 35) Muna guje wa ayyukan da za su bata wa Allah rai, kamar karban karin jini. (Ayyukan Manzanni 15:28, 29; Galatiyawa 5:19-21) Mu masu son zaman lafiya ne kuma ba ma saka hannu a yaki. (Matta 5:9; Ishaya 2:4) Muna nuna ladabi ga gwamnatin kasar da muke kuma muna yin biyayya da dokokinta muddin ba za su sa mu keta dokokin Allah ba.—Matta 22:21; Ayyukan Manzanni 5:29.

 15.   Zumunci tsakaninmu da wadanda ba Shaidu ba. Yesu ya ba da doka cewa mu ‘ƙaunaci maƙwabcinmu kamar ranmu.’ Kari ga haka, ya ce Kiristoci “ba na duniya suke ba.” (Matta 22:39; Yohanna 17:16) Saboda haka, muna kokari mu yi ayyukan “nagarta zuwa ga dukan mutane,” amma ba ma saka hannu a siyasa kuma ba ma tarayya da sauran addinai. (Galatiyawa 6:10; 2 Korintiyawa 6:14) Amma ba kushe wa saboda zabin da suka yi a wadannan batutuwa.—Romawa 14:12.

 Idan kana da karin tambayoyi game da imanin Shaidun Jehobah, za ka samu karin bayani game da mu a dandalinmu na intane ko ka tuntube mu a daya daga cikin ofisoshinmu ko ka halarci taro a Majami’ar Mulki da ke kusa da kai ko kuma ka gaya wa wani Mashaidin da ke yankinku.

a Ka duba littafin Truth in Translation: Accuracy and Bias in English Translations of the New Testament, shafi na 165.

b An riga an koro aljannu daga sama, amma har ila suna wanzuwa.​—Ru’ya ta Yohanna 12:7-9.