Koma ka ga abin da ke ciki

Shin Mutum Zai Iya Daina Zama Mashaidin Jehobah Ne?

Shin Mutum Zai Iya Daina Zama Mashaidin Jehobah Ne?

Kwarai kuwa. Akwai abubuwa biyu da mutum zai iya yi da za su nuna cewa ba ya so ya ci gaba da zama Mashaidin Jehobah:

  • Da baki ko kuma a rubuce. Mutum zai iya fada ko kuma ya rubuta ta wasika cewa ya yanke shawara ba ya so ya ci gaba da zama Mashaidin Jehobah.

  • Ta wurin ayyukansa. Mutum zai iya yin wani abin da zai nuna cewa ba ya so ya zama Mashaidin Jehobah kuma. (1 Bitrus 5:9) Alal misali, yana iya soma bin wani addini dabam kuma ya nuna cewa wannan addinin ne ya fi so.​—1 Yohanna 2:19.

Idan wani mutum ya daina fita wa’azi da kuma halartan taro fa? Kuna daukan sa a matsayin wanda ba ya so ya ci gaba da zama mashaidi?

A’a, ba ma haka. Da akwai bambanci tsakanin wanda ba ya so ya ci gaba da zama Mashaidi da kuma wanda ya karaya. A yawacin lokaci, wadanda suka daina halartan taro da kuma fita wa’azi sun yi hakan ne don wata matsalar da suke fuskanta ba don ba sa so su zama Shaidun Jehobah kuma ba. Maimakon mu guji irin wadannan mutane, muna iya kokarin mu wajen taimaka musu da kuma karfafa su. (1 Tasalonikawa 5:14; Yahuda 22) Idan mutumin yana bukatar taimako, dattawan ikilisiya ne suke yin ja-gora wajen tabbatar da cewa an taimaka wa mutumin.​—Galatiyawa 6:1; 1 Bitrus 5:1-3.

Amma, ba a umurci dattawa su tilasta wa wani ya ci gaba da zama Mashaidin Jehobah ba. Kowa yana da ’yancin zaban addinin da yake so ya bi. (Joshua 24:15) Mun gaskata cewa wajibi ne wadanda suke bauta wa Allah su yi hakan da son ransu.​—Zabura 110:3; Matta 22:37.