Koma ka ga abin da ke ciki

Shin Wajibi Ne Mutum Ya Kasance da Addini?

Shin Wajibi Ne Mutum Ya Kasance da Addini?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 E. Don Allah yana son mutane su rika taruwa don su yi ibada. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga kauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu.”—Ibraniyawa 10:24, 25.

 Yesu ya nuna cewa mabiyansa za su rika bin wani addini, shi ya sa ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da kauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Kuma hanya ta musamman da za su nuna irin wannan kaunar ita ce yin cudanya da juna. Za su kasance a ikilisiyoyi dabam-dabam da suke yin taro a kai a kai. (1 Korintiyawa 16:19) Amma dukansu ’yan’uwa ne ko da daga wace kasa suka fito.—1 Bitrus 2:17.

Za a yi wani abu ba kawai kasancewa da addini ba

 Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata mutane su rika yin taro don ibada, bai ce kasancewa kawai da addini shi yake faranta masa rai ba. Sai mutum ya yi amfani da abubuwan da yake koya a taro kafin ya faranta wa Allah rai. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Addini mai tsarki marar bāci a gaban Allah Ubanmu ke nan, mutum ya ziyarci marayu da gwauraye cikin kuncinsu, shi tsare kansa marar aibi daga duniya.”—Yakub 1:27.