Koma ka ga abin da ke ciki

Yadda Aka Yada Bishara a Paris

Yadda Aka Yada Bishara a Paris

Majalisar Dinkin Duniya ta yi taron koli a kan sauyin yanayi a Paris, kasar Faransa, a ranar 30 ga Nuwamba zuwa 12 ga Disamba 2015, don ta tattauna yadda za a rage ayyukan da ke jawo illa ga muhalli. Mutane kusan 38,000 daga kasashe 195 ne sun halarci wannan taron kuma sun hada da jami’an gwamnati da masu kula da muhalli da masanan kimiyya da kuma manyan ‘yan kasuwa. Dubban mutane kuma sun je wata cibiyar yada labarai da ke kusa da wurin don su ji bayanai game da sauyin yanayi.

Shaidun Jehobah ba su halarci taron ba, amma su ma sun damu da muhalli. Da yawa a cikin su sun fita su gaya wa mutane alkawarin da Allah ya yi na sabonta duniyar nan da kuma kawar da abubuwan da ke jawo illa ga muhalli.

Wani Mashaidi ya shiga motar haya kuma a cikin motar ya soma tattaunawa da wani dan Peru da ya yi shige irin na mutanen Peru. Mutumin ya gaya wa Mashaidin cewa, ko da yake yana da koshin lafiya kuma yana zama a inda ba sa fuskantar barazanar sauyin yanayi, ya damu kwarai da abin da zai faru da duniya a nan gaba. Bayan da Mashaidin ya bayyana masa alkawarin da Allah ya yi game da duniyar nan, ya yi farin ciki sosai kuma ya karbi katin jw.org, wanda ke dauke da adireshin dandalinmu na www.jw.org.

Shaidun Jehobah guda biyu da suke tafiya a cikin jirgin kasa sun hadu da wani masanin kimiyya dan kasar Amurka da ya kware a kula da muhalli kuma suka soma tattaunawa da shi. Ya yi mamaki da ya ji cewa kungiyar Green Building Initiative ta ba Shaidun Jehobah lambar yabo na Four Green Globes sau biyu. An ba su wadannan lambobin yabon ne don yadda suka tsara sababbin gine-gine biyu da suka yi a reshensu na Wallkill, a New York, wadanda suka kyautata muhalli. Shi ma ya karbi katin jw.org.

Sa’ad da mutane da yawa suka ga yadda Shaidun Jehobah sun damu da muhalli, sun yi alkawarin za su shiga dandalinmu na jw.org. Da wata mata da ta halarci taron daga Kanada ta ji cewa Shaidun Jehobah sun yi kokari su kāre muhallin tsuntsu mai suna eastern bluebird a sabon hedkwatar da suka gina a kauyen Warwick a birnin New York, sai ta ce: “Kafin in soma yaki da masu gurbata muhalli, ni mai yin bincike a kan tsuntsaye ne. Ban san cewa haka ne Shaidun Jehobah suke daraja dabbobin daji ba. Zan karanta littattafanku kuma in shiga dandalinku domin in sami karin bayani game da ku.”