Wa’azin da Muke Yi

FITA WA’AZI

Amalanken Wa’azi a Wuraren Hutu na Kasar Jamus

Shaidun Jehobah sun kafa amalanken wa’azi a Berlin da Cologne da Hamburg da Munich da kuma wasu birane. Za a iya amfani da irin wannan wa’azin a wuraren da mutanen suke zuwa hutu a Jamus?

FITA WA’AZI

Amalanken Wa’azi a Wuraren Hutu na Kasar Jamus

Shaidun Jehobah sun kafa amalanken wa’azi a Berlin da Cologne da Hamburg da Munich da kuma wasu birane. Za a iya amfani da irin wannan wa’azin a wuraren da mutanen suke zuwa hutu a Jamus?

Baza Kolin da Aka Yi a Treasure City “Kyauta” Ce Daga Allah

Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da kuma bidiyoyinmu sun burge dalibai da kuma malamai a wurin baza kolin Gaudeamus na littattafai da aka yi a kasar Romania.

An Yi Wa Mutanen Sinti da Roma Wa’azi a Jamus

A lokacin da aka yi kamfen din wa’azin, Shaidun Jehobah sun rarraba kasidu da warkoki fiye da 3,000. Ban da haka ma, Shaidun suna yi wa mutanen Sinti da Roma fiye da 360 wa’azi kuma sun soma nazari da guda 19.

An Baza Wani Irin Koli Mai Tamani a Kasar Botswana

Bidiyoyin Ka Zama Abokin Jehobah da yake koyar da yadda za a rika bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki ya jawo hankalin yara sosai.

Yadda Ake Yi wa Matukan Jirgin Ruwa Wa’azi

Don su yi wa ma’aikatan jirgin ruwa da ba sa zama a wuri daya wa’azi, Shaidun Jehobah sun kafa wurin koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a tashoshin jiragen ruwa. Mene ne matukan jiragen ruwa suka yi?

Yadda Aka Yada Bishara a Paris

Shaidun Jehobah sun fita wa’azi musamman don su gaya wa mutane albishiri cewa a nan gaba babu abin da zai gurbata duniya.

Zuwa Yin Wa’azin Bishara a Yankunan da Asalin ’Yan Kanada Suke

Shaidun Jehobah su yi wa’azin bishara a harsuna dabam-dabam don su taimaka wa mutane su koyi game da Mahalicci a yarensu na asali.

Biki da wasu Bayanai don Asalin ’Yan Amirka a Birnin New York

A bikin ‘Gateway to Nations’ da aka yi a shekara ta 2015, mutane da yawa sun yaba wa Shaidun Jehobah a kan yadda suka baza littattafai a harsuna da yawa na Asalin ’Yan Amirka.

Takawa a kan Gadon Teku don Wa’azi

Shaidun Jehobah suna amfani da wata hanya ta musamman su kai wa’azin bishara ga mutanen da ke zama a wasu kananan tsibirai da ake kira Halligen.

Yin Wa’azin Bishara a Arewacin Amirka da Turai

Shaidun Jehobah suna zuwa arewacin Amirka da Turai su dade suna taimaka wa mutanen da suke so su san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa duk da cewa yin hakan yana tattare da kalubale.

Yin Wa’azi a Yankin da Shaidun Jehobah Ba Sa Yawan Zuwa Wa’azi—Ostareliya

Wasu iyalai Shaidun Jehobah sun yi tafiya don su yi wa mutanen da ke karkarar Ostareliya wa’azi.

Yin Amfani da JW.ORG don Yaɗa Saƙon Littafi Mai Tsarki

Shaidun Jehobah, manya da kanana, suna amfani sosai da dandalinsu da aka canja wa fasali don su gaya wa mutane da yawa bisharar Mulkin Allah.

Gajeren Bidiyo: Ya Cancanci Sake Kallo!

Dubi yadda wani salon wa’azi na musamman a Manhattan, New York, ya sa mutane da dama suka sami littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki.

Kamfen na Musamman na Shaidun Jehobah a Manhattan, New York

Ka koyi game da ƙoƙarinmu na musamman mu sanar wa mutane da saƙon Littafi Mai Tsarki.