Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 99

Miliyoyin ’Yan’uwa

Miliyoyin ’Yan’uwa

(Ru’ya ta Yohanna 7:​9, 10)

  1. 1. Ga dubun-dubban jama’a,

    Masu yawan gaske,

    Su masu aminci ne,

    Har da bangaskiya.

    Dubun-dubban ʼyan’uwa,

    Shaidun Jehobah ne

    Muna harsuna dabam-dabam,

    Muna yabon Allah.

  2. 2. Ga dubun-dubban jama’a,

    Muna yin wa’azi,

    Wa’azin Mulkin Allah

    Don a yabi Allah.

    Yayin da muke haka,

    Mukan gaji sosai

    Yesu na tare da dukanmu,

    Za ya taimake mu.

  3. 3. Ga dubun-dubban jama’a,

    Allah zai kāre mu,

    Don shi muke bauta wa

    Kowane lokaci.

    Mu ne Shaidun Jehobah,

    Za mu yi wa’azi,

    Wa’azin Mulkin Maɗaukaki

    Don kowa ya sani.

(Ka kuma duba Isha. 52:7; Mat. 11:29; R. Yoh. 7:15.)