Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 100

Mu Rika Marabtar Baki

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Marabtar Baki
DUBA

(Ayyukan Manzanni 17:7)

 1. 1. Jehobah na mana alheri sosai,

  Yana kula da dukan halittunsa.

  Yana yin tanadi,

  ga dukan ’yan Adam

  Domin su ji daɗin rayuwa.

  In muna taimaka wa duk mutane,

  Muna yin koyi da Jehobah Allah.

  Jehobah Allah zai

  yi mana albarka

  Don muna yin alheri sosai.

 2. 2. In muna taimaka wa mabukata,

  Jehobah zai saka mana fa sosai.

  Ko da su baƙi ne,

  mu taimaka musu,

  Su iya biyan bukatunsu.

  Lidiya ta marabci baƙi sosai,

  Mu ma mu yi koyi da misalinta.

  Allah ba zai manta

  da waɗanda suke

  Yin koyi da alherinsa ba.

(Ka kuma duba A. M. 16:​14, 15; Rom. 12:13; 1 Tim. 3:2; Ibran. 13:2; 1 Bit. 4:9.)