Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 37

Mu Rika Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciya

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciya
DUBA

(Matta 22:37)

 1. 1. Ya Jehobah Maɗaukaki,

  Kai kaɗai zan yi wa biyayya.

  Ka cancanci in bauta ma,

  Zan riƙa bauta maka kullum.

  Zan bi dukan ƙa’idodinka,

  Ina son duk dokokinka!

  (AMSHI)

  Ya Jehobah, kai kaɗai ne,

  Zan bauta wa da duk zuciya.

 2. 2. Ya Uba, duk ayyukanka,

  Sama da ƙasa na yabon ka.

  Ni ma zan riƙe aminci,

  Zan yi shelar ka a ko’ina.

  Zan bauta maka har abada,

  Zan yi da duk zuciyata.

  (AMSHI)

  Ya Jehobah, kai kaɗai ne,

  Zan bauta wa da duk zuciya.

(Ka kuma duba K. Sha. 6:15; Zab. 40:8; 113:​1-3; M. Wa. 5:4; Yoh. 4:34.)