Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 36

Mu Rika Kāre Zuciyarmu

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Kāre Zuciyarmu

(Misalai 4:23)

 1. 1. Mu lura da zuciyarmu,

  Mu guji zunubi.

  Allah na ganin zuciya,

  Yana ganin kome.

  Zuci tana da yaudara,

  Takan sa zunubi.

  Ya Allah, ka taimake mu

  Don mu yi nufinka.

 2. 2. Mu riƙa addu’a kullum,

  Mu kusaci Allah.

  Mu miƙa duk damuwarmu

  Ga Allah Jehobah.

  Za mu riƙa bin umurnin

  Jehobah Allahnmu.

  Kuma mu riƙe aminci

  Don mu sa shi murna.

 3. 3. Mu daina tunanin banza,

  Mu riƙa nagarta.

  Mu riƙa barin Kalmarsa

  Ta ratsa zucinmu.

  Jehobah Allah na sama

  Na son mutanensa.

  Za mu riƙa bauta masa

  Da dukan zuciya.

(Ka kuma duba Zab. 34:1; Filib. 4:8; 1 Bit. 3:4.)