Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 146

‘Allah Zai Sabonta Kome’

Ka Zabi Sauti
‘Allah Zai Sabonta Kome’
DUBA

(Ru’ya ta Yohanna 21:​1-5)

 1. 1. Mun tabbata cewa Yesu na mulki,

  Jehobah Allah ne ya naɗa shi.

  Ya jefo Shaiɗan zuwa duniya,

  Zai sa mutane yin nufin Allah.

  (AMSHI)

  Jehobah zai taimake mu,

  Kuma zai kasance da mu.

  Ba za mu riƙa shan wahala ba,

  Ba za mu sake mutuwa ba fa.

  Allah ya ce: ‘Zan sabonta kome,’

  Don shi mai aminci ne.

 2. 2. Ku ga sabuwar Urushalimar nan,

  Allah ya zaɓi abokan Mulkin.

  Tare da Yesu za su haskaka,

  Za su sa mu bi umurnin Allah.

  (AMSHI)

  Jehobah zai taimake mu,

  Kuma zai kasance da mu.

  Ba za mu riƙa shan wahala ba,

  Ba za mu sake mutuwa ba fa.

  Allah ya ce: ‘Zan sabonta kome,’

  Don shi mai aminci ne.

 3. 3. Mulkin Jehobah zai kawo albarka,

  Za a buɗe ƙofar birnin kullum.

  Za mu riƙa more albarkunsa,

  Sai mu ci gaba da shelar Mulkin.

  (AMSHI)

  Jehobah zai taimake mu,

  Kuma zai kasance da mu.

  Ba za mu riƙa shan wahala ba,

  Ba za mu sake mutuwa ba fa.

  Allah ya ce: ‘Zan sabonta kome,’

  Don shi mai aminci ne.

(Ka kuma duba Mat. 16:3; R. Yoh. 12:​7-9; 21:​23-25.)