Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 145

Allah Ya Yi Mana Alkawarin Aljanna

Ka Zabi Sauti
Allah Ya Yi Mana Alkawarin Aljanna
DUBA

(Ru’ya ta Yohanna 21:4)

 1. 1. Allah zai dawo da aljanna

  Ta sarautar Yesu Kristi.

  Zai kawar da dukan zunubi

  Da mutuwa da azaba.

  (AMSHI)

  Yin rayuwa a Aljanna,

  A duniya zai yi daɗi.

  Allah zai sa Ɗansa Yesu,

  Ya cika alkawuran nan.

 2. 2. A aljanna Jehobah zai sa

  Ɗansa ya ta da matattu.

  Yesu ya ce: ‘Za ka kasance

  Tare da ni a Aljanna.’

  (AMSHI)

  Yin rayuwa a Aljanna,

  A duniya zai yi daɗi.

  Allah zai sa Ɗansa Yesu,

  Ya cika alkawuran nan.

 3. 3. Yesu Kristi ne Sarkin Mulkin,

  Shi ne Sarkin da ya dace.

  Muna murna don albarkun nan,

  Muna yabon Jehobah fa.

  (AMSHI)

  Yin rayuwa a Aljanna,

  A duniya zai yi daɗi.

  Allah zai sa Ɗansa Yesu,

  Ya cika alkawuran nan.

(Ka kuma duba Mat. 5:5; 6:10; Yoh. 5:​28, 29.)