Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 124

Mu Kasance da Aminci

Mu Kasance da Aminci

(Zabura 18:25)

  1. 1. Za mu riƙa yin biyayya

    Ga Jehobah Allahnmu.

    Za mu bi duk umurninsa,

    Za mu riƙe aminci.

    Bin dokokinsa na da kyau,

    Suna taimaka mana.

    Ya Jehobah, mai aminci,

    Za mu bi umurninka.

  2. 2. Za mu riƙa yin alheri

    Ga dukan ’yan’uwanmu.

    Za mu riƙa nuna cewa

    Muna ƙaunar su sosai.

    Za mu daraja su sosai

    Da dukan zuciyarmu.

    Da aminci, za mu bauta

    Wa Jehobah Allahnmu.

  3. 3. Da aminci za mu riƙa

    Bin umurnin dattawa.

    In suna yin ja-goranci,

    Mu riƙa yin biyayya.

    Yin hakan zai sa Jehobah

    Ya yi mana albarka.

    Sai mu riƙe amincinmu,

    Ga Jehobah Allahnmu.

(Ka kuma duba Zab. 149:1; 1 Tim. 2:8; Ibran. 13:17.)