Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZA KA IYA KUSANTAR ALLAH

Kana Yin Abin da Allah Ya Ce?

Kana Yin Abin da Allah Ya Ce?

“Ka gaya mini duk abin da kake so kuma zan yi maka.” Babu shakka, da ƙyar ka yi irin wannan alkawarin ga baƙo ko mutumin da ba ka sani ba sosai. Amma yin hakan ga amininka ba zai zama matsala ba. Aminai suna jin daɗin yi wa juna alheri.

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana yin abin da zai sa bayinsa farin ciki. Alal misali, Sarki Dauda wanda aminin Allah ne ya ce: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajibi, waɗanda ka yi, suna da yawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: . . . sun fi gaban lissafi.” (Zabura 40:5) Ƙari ga haka, Jehobah yana yin alheri ga mutanen da ba su san shi ba, ‘yana ƙosar da su da abinci, yana kuma faranta musu rai.’—Ayyukan Manzanni 14:17, Littafi Mai Tsarki.

Muna jin daɗin yin alheri ga waɗanda muke ƙauna da kuma darajawa

Tun da Jehobah yana sha’awar yin abin da ke sa mutane farin ciki, ya kamata waɗanda suke so su zama aminansa su riƙa yin abubuwan da za su ‘faranta zuciyarsa.’ (Misalai 27:11) Amma wane takamaiman abu ne za ka yi don ka faranta wa Allah rai? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada kuwa ku daina yin alheri da gudummawa, domin irin waɗannan suke faranta wa Allah rai.” (Ibraniyawa 13:16, LMT) Shin hakan yana nufi cewa ta wajen yin alheri da gudummawa ne kawai za mu faranta wa Jehobah rai?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe [Allah] . . . sai tare da bangaskiya.” (Ibraniyawa 11:6) Kuma sai da “Ibrahim ya gaskanta Allah” ne ‘aka ce da shi abokin Allah.’ (Yaƙub 2:23) Yesu Kristi ya kuma ce idan muna so Allah ya albarkace mu, muna bukatar mu “ba da gaskiya ga Allah.” (Yohanna 14:1) Saboda haka, ta yaya za ka sami bangaskiyar da za ta sa ka kusaci Allah? Mataki na farko shi ne yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai. Yayin da kake yin haka, za ka sami ‘sani’ na gaske game da “nufinsa” kuma za ka san yadda za ka “gamshe shi” sosai. Ƙari ga haka, yayin da kake daɗa koyon gaskiya game da Jehobah kuma kana yin abin da ya ce, bangaskiyarka za ta ƙaru kuma Jehobah zai daɗa kusantar ka.—Kolosiyawa 1:9, 10.