Ta Hannun Yohanna 14:1-31
14 “Kada ku bar wani abu ya dami zukatanku. Ku ba da gaskiya ga Allah, ku kuma ba da gaskiya gare ni.
2 A gidan Ubana akwai wuraren zama da yawa. Da a ce babu, da zan gaya muku, gama zan tafi in shirya muku wurin zama.
3 Ƙari ga haka, idan na je na shirya muku wuri, zan sake dawowa domin in ɗauke ku zuwa wurin da nake, domin ku ma ku kasance a wurin da nake.
4 Kuma kun san hanyar zuwa wurin da zan je.”
5 Toma ya amsa masa ya ce: “Ubangiji, ba mu san wurin da za ka je ba. To, ta yaya za mu san hanyar?”
6 Yesu ya amsa masa ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Babu wanda zai iya zuwa wurin Uba, sai ta wurina.
7 Da kun san ni, da kun san Ubana ma; amma daga yanzu kun san shi kuma kun gan shi.”
8 Filibus ya ce masa: “Ubangiji, ka nuna mana Uban, in ka yi hakan, bukatarmu ta biya.”
9 Yesu ya ce masa: “Duk da cewa na daɗe ina tare da ku, har yanzu ba ka san ni ba Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban ma. To, me ya sa ka ce, ‘Ka nuna mana Uban’?
10 Ba ka gaskata cewa ina da haɗin kai da Uban, kuma Uban yana da haɗin kai da ni ba ne? Abubuwan da nake gaya muku ba daga wurina suka fito ba, amma Uba wanda yake da haɗin kai da ni ne yake yin ayyukansa ta wurina.
11 Ku yarda da ni saꞌad da na ce ina da haɗin kai da Uban, kuma Uban yana da haɗin kai da ni. Idan ba ku gaskata da abin da na faɗa ba, ku gaskata domin ayyukan da nake yi.
12 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda yake ba da gaskiya a gare ni, shi ma zai yi ayyukan da nake yi; kuma zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uban.
13 Ƙari ga haka, duk abin da kuka roƙa a cikin sunana, zan yi shi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan.
14 Idan kuka roƙi kome a cikin sunana, zan yi shi.
15 “Idan kuna ƙauna ta, za ku bi dokokina.
16 Zan roƙi Uban kuma zai ba ku wani mai taimako* da zai kasance da ku har abada,
17 shi ne ruhun gaskiya, da duniya ba za ta iya samu ba, domin duniya ba ta iya ganin shi kuma ba ta san shi ba. Kun san shi, domin ya kasance a cikinku kuma yana cikinku.
18 Ba zan bar ku kamar marayu ba. Zan dawo wurinku.
19 A cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, duniya ba za ta sake gani na ba, amma za ku gan ni. Domin ina rayuwa, ku ma za ku rayu.
20 A ranar, za ku san cewa ina da haɗin kai da Uban kuma kuna da haɗin kai da ni, ni ma ina da haɗin kai da ku.
21 Duk wanda ya amince da dokokina kuma yana bin su, shi ne wanda yake ƙauna ta. Kuma duk wanda ya ƙaunace ni, Ubana ma zai ƙaunace shi, zan ƙaunace shi kuma zan bayyana masa kaina da kyau.”
22 Sai Yahuda wanda ba Iskariyoti ba ne, ya ce masa: “Ubangiji, mene ne ya faru da kake shirin bayyana kanka da kyau a gare mu amma ba ga duniya ba?”
23 Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Idan mutum yana ƙauna ta, zai yi abin da na faɗa, Ubana zai ƙaunace shi, kuma za mu zo wurin mutumin mu zauna tare da shi.
24 Duk wanda ba ya ƙauna ta, ba ya yin abin da na faɗa. Maganar da kuke ji ba tawa ba ce, amma ta Ubana wanda ya aiko ni ne.
25 “Na gaya muku abubuwan nan yanzu da nake tare da ku.
26 Amma mai taimakon, wato ruhu mai tsarki, wanda Uban zai aiko cikin sunana, shi ne zai koya muku dukan abubuwa, kuma ya tuna muku da dukan abubuwan da na gaya muku.
27 Na bar ku cikin salama; kuma ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku bar wani abu ya dami zukatanku kuma kada ku bar zukatanku su tsinke saboda tsoro.
28 Kun ji na ce, ‘Zan tafi kuma in sake dawowa wurinku.’ Idan kuna ƙauna ta, za ku yi farin ciki cewa zan koma wurin Uban, domin Uban ya fi ni girma.
29 Na faɗa muku yanzu tun bai faru ba, domin saꞌad da ya faru, ku ba da gaskiya.
30 Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyar nan yana zuwa, kuma ba shi da iko a kaina.
31 Amma domin duniya ta san cewa ina ƙaunar Uban, ina yin daidai abin da Uban ya umurce ni in yi. Ku tashi mu bar nan.
Hasiya
^ Ko kuma “mai ƙarfafa.”