HASUMIYAR TSARO Janairu 2013

Zuwa ga Masu Karatu

Somawa da wannan fitowar, wasu talifofi a wannan mujallar za su riƙa fitowa ta Intane ne kaɗai. Ka karanta abin da ya sa aka yi waɗannan canje-canjen.

COVER SUBJECT

Ya Kamata Ka Ji Tsoron Ƙarshen Duniya?

Wataƙila abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ƙarshen duniya zai ba ka mamaki.

KA KUSACI ALLAH

“Ka Bayyana Su ga Jarirai”

Ka koyi yadda za ka fahimci gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da Allah.

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Yanzu Na Sami ’Yanci na Ƙwarai.”

Ka karanta yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa wani matashi ya daina shan taba da ƙwaya kuma ya daina maye.

KA YI KOYI DA BANGASKIYARSU

‘Shi da Ya Ke Matacce Yana Jawabi Har Yanzu’

Bari mu tattauna abubuwa uku da suka sa Habila ya yi imani da Mahalicci mai ƙauna.

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Mene ne sunan Allah, kuma me ya sa ya kamata mu yi amfani da shi?

Ƙarin Abubuwan da Muke da Su

Ka Kiyayi Kishi!

Ka karanta abin da Musa ya yi game da kishi da dan’uwansa da ’yar’uwansa suka yi masa.

Ka Ce “Na Gode”

Iyaye, ku koya wa yaranku amfanin fadin “na gode” tun suna yaranta.