Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Yanzu Na Sami ’Yanci na Ƙwarai.”

“Yanzu Na Sami ’Yanci na Ƙwarai.”
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1981
  • ƘASAR HAIHUWA: AMIRKA
  • TARIHI: ƊA MUBAZZARI

RAYUWA TA A DĀ:

An haife ni ne a Moundsville, wani gari da ake zaman lafiya kusa da Kogin Ohio, a jihar West Virginia, a Amirka. Mu ’ya’ya huɗu ne iyayenmu suka haifa, maza uku da ta mace ɗaya kuma ni ne na biyu a cikin su. Da yake mu yara huɗu ne a gidan, kullum muna cikin wasa da dariya. Iyayena mutane ne masu ƙwazo masu kirki, kuma suna son jama’a. Ko da yake ba mu da kuɗi sosai, amma muna samun abin biyan bukata a kowane lokaci. Iyayenmu sun yi iya ƙoƙarinsu su tarbiyyatar da mu bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki tun muna ƙanana da yake su Shaidun Jehobah ne.

Amma, a lokacin da na kai ɗan shekara goma sha, na riga na fara bijirewa daga abin da suka koya min. Na soma tunani cewa yin rayuwa bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba zai sa rayuwata ta kasance da ma’ana ba. A ganina, mutum zai kasance da farin ciki ne idan ya yi abin da ya ga dama. Da shigewar lokaci, sai na daina zuwa taron Kirista. Yayana da kuma ƙanwata ma suka bijire. Iyayenmu sun yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka mana mu dawo hanya, amma mun yi watsi da su.

Ban san cewa wannan “’yanci” da nake nema zai jefa ni cikin mummunar jaraba ba. Wata rana da nake dawowa daga makaranta, sai wani abokina ya ba ni taba sigari in sha sai na karɓa. Daga ranar, na soma halayen banza. Da sannu sannu, na soma shaye-shaye da iskanci. Da shigewar shekaru, na duƙufa cikin shan ƙwayoyi kuma hakan ya zama min jaraba. Na soma sayar da miyagun ƙwayoyi domin in sami kuɗin shaye-shaye kuma hakan ya sa na daɗa dulmaya cikin wannan jarabar.

Na san cewa abin da nake yi ba daidai ba kuma hakan ya sa ba na samun kwanciyar hankali. Duk da haka, na ji kamar na zama karen da ya yi nisa da ba ya jin kira. Ko da yake ina zuwa fati da wuraren nishaɗi inda nake kasancewa da mutane, sau da yawa nakan kaɗaita a wurin kuma in yi baƙin ciki. A wasu lokatai nakan tuna cewa iyayena mutane ne masu kirki, amma sai in yi mamakin abin da faru da har na bijire haka.

 YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Na riga na fid da zuciya cewa ba zan iya koma mutumin kirki ba, amma mutane da suke ƙaunata ba su fid da rai a kaina ba. A shekara ta 2000, iyayena suka gayyace ni zuwa wani taron gundumar Shaidun Jehobah. Sai na halarci taron ko da yake ba da son raina ba. Abin mamaki, yayana da ƙanwata da suka bijire ma sun halarci taron.

A wurin taron gundumar, na tuna cewa na taɓa halartar wani fati a wannan wurin shekarar da ta shige. Da na tuna abin da ya faru a wurin fatin da kuma abin da yake faruwa a taron yanzu, sai na ga akwai bambanci sosai kuma hakan ya sa na soma tunani. A lokacin da ake fatin, an ɓata ko’ina da datti da hayaƙin sigari. Yawancin mutanen da ke wurin fatin masu son faɗa ne kuma waƙoƙin da ake yi ba su da kyau. Amma a wannan taron gundumar, ina tare da mutane masu farin ciki, kuma sun karɓe ni da hannu bibiyu duk da cewa mun yi shekaru da rabuwa. Wurin taron na da tsabta, kuma jawaban da aka bayar a wurin masu sa farin ciki ne. Da na lura da amfanin bin Littafi Mai Tsarki, sai na soma tunani, ‘Me ya sa na yi watsi da shi?’—Ishaya 48:17, 18.

“Da taimakon Littafi Mai Tsarki, na daina sha da kuma sayar da ƙwaya, kuma na zama mutumin kirki”

Nan da nan bayan taron, sai na soma halartan taron Kirista. Yayana da ƙanwata suka soma halartan taron Kirista don su ma sun ji daɗin abin da suka ji a taron gundumar. Dukanmu uku muka amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mu.

Ayar Littafi Mai Tsarki da ta ratsa zuciyata ita ce Yaƙub 4:8, da ta ce: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gare ku.” Na fahimci cewa idan ina son in kusaci Allah, dole ne in daina halayen banza. Ina bukatar gyara rayuwata, wato, in daina shan taba da ƙwaya kuma in daina yin maye.—2 Korintiyawa 7:1.

Na daina harka da abokaina na dā kuma na yi abota da wasu da ke cikin ƙungiyar Jehobah. Dattijon da ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni ya taimaka min sosai. Yakan kira ni a waya kuma ya ziyarce ni. Yana cikin abokaina na ƙwarai har wa yau.

A shekara ta 2001, da ni da yayana da ƙanwata duk muka yi baftisma. Babu shakka, iyayena da ƙanena da ya manne wa Jehobah sun yi farin ciki sosai cewa yanzu dukan mu muna bauta wa Jehobah.

YADDA NA AMFANA:

A dā na ɗauka cewa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki suna hana mutum sakewa, amma yanzu na san cewa suna kāre mu ne sosai. Da taimakon Littafi Mai Tsarki, na daina sha da kuma sayar da ƙwaya, kuma na zama mutumin kirki.

Yanzu, ina da gatan zama ɗaya daga cikin waɗanda suke bauta wa Jehobah a faɗin duniya. Shaidun Jehobah suna ƙaunar junansu da gaske kuma suna bauta wa Allah cikin haɗin kai. (Yohanna 13:34, 35) A cikin waɗannan ’yan’uwan ne na sami matata, Adrianne, kuma a gare ni, ita kyauta ce daga Jehobah. Ina ƙaunarta sosai. Abin farin ciki ne cewa ina bauta wa Mahaliccinmu tare da ita.

A maimakon damuwa da kaina kawai, yanzu ina hidima ta cikakken lokaci don in taimaka wa mutane su san yadda za su amfana daga koyarwar Littafi Mai Tsarki. Wannan aikin yana sa ni farin ciki matuƙa. Tabbas, Littafi Mai Tsarki ya gyara rayuwata. Yanzu na sami ’yanci na ƙwarai.