Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 KA YI KOYI DA IMANINSU | HABILA

‘Shi da Ya Ke Matacce Yana Jawabi Har Yanzu’

‘Shi da Ya Ke Matacce Yana Jawabi Har Yanzu’

HABILA ya kalli tumakinsa sa’ad da suke cin ciyawa a kan tudu cikin lumana. Daga baya, mai yiwuwa ya mai da hankalinsa can, gaba da tumakinsa inda ya ga ɗan haske. Ya san cewa a can inda hasken yake, akwai wani takobi mai harshen wuta da ke juyawa. Wannan takobin ne ya rufe hanyar shiga cikin lambun Adnin. Iyayensa sun taɓa zama a wurin, amma yanzu, babu wanda zai iya shiga. Ka yi tunanin iska mai daɗi da ake yi da maraice sa’ad da Habila yake kallon sama kuma yana tunanin Mahaliccinsa. Shin, zai yiwu mutum ya sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah? Hakika, abin da Habila yake sha’awa ke nan.

Habila yana yi maka jawabi a yau. Za ka iya cewa hakan ba zai yiwu ba domin wannan yaron Adamu na biyu ya mutu tun da daɗewa, kusan shekaru dubu shida yanzu kuma ya riga ya zama turɓaya. Balle ma, Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa: “Matattu ba su san komi ba.” (Mai-Wa’azi 9:5, 10) Ƙari ga haka, ba a rubuta wani furucin da Habila ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki ba. To, ta yaya yake yi mana jawabi a yau?

Allah ya hure manzo Bulus ya yi wannan furuci game da Habila: ‘Ta wurin wannan fa shi da yake matacce yana jawabi har yanzu.’ (Ibraniyawa 11:4) Ta yaya Habila yake yi mana jawabi? Ta wurin bangaskiyarsa. Habila ne mutumi na farko da ya taɓa kasancewa da bangaskiya. Misalinsa mai kyau na bangaskiya yana taimaka wa mutane a yau su kasance da bangaskiya. Idan muna koyi da irin bangaskiyar Habila, hakan yana nufin cewa muna sauraron jawabin da yake yi.

Shin, mene ne za mu iya koya game da Habila da kuma yadda ya nuna bangaskiya, tun da Littafi Mai Tsarki bai yi magana sosai game da shi ba? Bari mu gani.

RAYUWA SA’AD DA ’YAN ADAM BA SU DAƊE A DUNIYA BA

An haifi Habila a lokacin da ba a daɗe da halittar ’yan Adam ba. A lokacin da Yesu yake duniya, ya ambaci Habila sa’ad da yake magana game da “farkon duniya.” (Luka 11:50, 51) Hakika, a nan Yesu yana magana ne game da ’yan Adam da suke da begen samun ceto. Ko da yake Habila ne mutumi na huɗu da ya taɓa rayuwa, mai yiwuwa shi ne na farko da Allah ya ga cewa ya cancanci samun ceto. * A bayyane yake cewa Habila bai girma a tsakanin mutanen da suke da halin kirki ba.

Ko da yake mutane ba su daɗe da rayuwa a duniya ba a lokacin, ’yan Adam sun riga sun faɗa mummunan yanayi. Wataƙila Adamu da Hawwa’u, iyayen Habila, kyawawan mutane ne masu kuzari sosai. Amma sun riga sun yi wani babban kuskure a rayuwarsu kuma sun san da hakan. A dā, su kamilai ne kuma suna da begen yin rayuwa har abada. Amma da suka yi wa Jehobah tawaye sai ya kore su daga Aljanna, wato, lambun Adnin. Sun saka burinsu kan gaba fiye da kome, har da bukatun ’ya’yansu, saboda haka, sun daina zama kamilai kuma suka rasa begen rai na har abada.—Farawa 2:15–3:24.

Da aka fid da su daga lambun Adnin, Adamu da  Hawwa’u suka sami kansu a tsaka mai wuya. Duk da haka, sa’ad da suka haifi ɗansu na fari, wato, Kayinu, sai Hawwa’u ta ce: “Na sami namiji da taimakon Ubangiji.” Wataƙila ta yi tunanin alkawarin da Jehobah ya yi a cikin lambun game da wata mace da za ta sami “zuriya.” Wannan zuriyar ce za ta halaka wannan mugun mala’ika da ya yaudari Hawwa’u da mijinta. (Farawa 3:15; 4:1) Shin, Hawwa’u ta ɗauka cewa ita ce wannan macen kuma Kayinu ne “zuriyar” da Allah ya yi alkawarinsa? Allah kaɗai ya sani.

Idan har ta yi wannan tunanin, to, ta yi kuskure. Kuma idan har da wannan ra’ayin ne ita da maigidanta suka tarbiyyatar da Kayinu, to sun sa shi ya kasance da girman kai. Sa’ad da Hawwa’u ta haifi ɗanta na biyu ba ta yi wani furucin yabo game da shi ba. A maimakon haka, aka ba shi suna Habila wanda mai yiwuwa yana nufin “Wofi.” (Farawa 4:2) Wataƙila wannan sunan yana nuna cewa ba su ɗauka Habila zai zama mutumin kirki kamar yadda suke zato Kayinu zai zama ba.

Ko da mene ne yanayin, iyaye a yau za su iya koyan darasi daga iyayenmu na farko. Idan iyaye ba su yi hankali ba, za su iya sa yaransu su kasance da fahariya da mugun buri da kuma son kai. Hakan zai iya faruwa ne ta yadda iyaye suke magana da kuma yin abubuwa. A wani ɓangare kuma, za su iya tarbiyyatar da yaransu su ƙaunaci Jehobah kuma su ƙulla dangantaka mai kyau da shi. Abin baƙin ciki shi ne, Adamu da Hawwa’u ba su cika aikinsu na yi wa yaransu tarbiyya mai kyau ba. Duk da haka, zuriyarsu suna da bege.

MENE NE YA TAIMAKA WA HABILA YA KASANCE DA BANGASKIYA?

Da alama cewa sa’ad da yaran suke girma, Adamu ya koya musu ayyukan da za su yi don su taimaka wajen biya wa iyalin bukata. Kayinu ya zama manomi kuma Habila ya zama makiyayi.

Amma da shigewar shekaru, Habila ya yi abin da ya fi kiwon tumaki muhimmanci. Ya yi ƙoƙari sosai ya kasance da imani kuma daga baya, Bulus ya yi rubutu game da wannan hali mai kyau, wato, bangaskiya. Ka tuna cewa babu wani ɗan Adam da ya kafa misali mai kyau wa Habila. Shin, mene ne ya taimaka masa ya yi imani da Jehobah? Bari mu tattauna abubuwa uku da wataƙila suka taimaka masa ya yi hakan.

Abubuwan da Jehobah ya halitta.

Hakika, Jehobah ya la’anta ƙasa. Saboda hakan, ƙaya da sarƙaƙƙiya ne suke ta tsira maimakon ƙasa ta ba da amfanin gona yadda ya kamata kuma hakan ya sa aikin noma ya zama da wuya. Duk da haka, iyalin sun sami abincin da suke bukata don su rayu. Ƙari ga haka, Allah bai la’anta dabbobi da tsuntsaye da kifaye da tsaunuka da ruwaye da kuma abubuwan da ke sararin sama ba. Duk inda Habila ya juya, sai ya ga halittu da suke nuna cewa Jehobah wanda ya halicci dukan abubuwa, Allah ne mai ƙauna da hikima da kuma nagarta. (Romawa 1:20) Babu shakka, yin bimbini a kan waɗannan abubuwan sun taimaka masa ya ƙara kasancewa da bangaskiya.

Habila ya keɓe lokaci don ya yi tunani game da Jehobah. Ka yi la’akari da lokacin da yake kiwon tumakinsa. Aikin makiyayi ya ƙunshi yin yawo sosai.  Domin haka, yakan kai waɗannan tumakin kiwo a kan tuddai, a cikin kwari da kuma a hayin kogi, wato, a duk inda akwai ciyawa da ruwa da kuma inuwa mai kyau. Tumaki suna bukatar kula sosai, kamar dai Allah ya halicce su ne don ɗan Adam ya yi musu ja-gora kuma ya kāre su daga haɗarurruka. Sa’ad da Habila yake tunani a kan wannan al’amarin, shin, ya fahimci cewa shi ma yana bukatar ja-gora da kāriya da kuma kula daga wajen Allah ne, wanda yake da hikima da kuma iko fiye da ’yan Adam? A bayyane yake cewa ya roƙi Allah ya yi masa ja-gora sa’ad da yake addu’a kuma hakan ya sa bangaskiyarsa ya riƙa ƙaruwa.

Abubuwan da Allah ya halitta sun sa Habila ya kasance da ƙwararren dalili na yin imani da Mahalicci mai ƙauna

Alkawuran da Jehobah ya yi.

Babu shakka, Adamu da Hawwa’u sun gaya wa ’ya’yansu dalilin da ya sa Jehobah ya kore su daga lambun Adnin. Saboda haka, Habila yana da dalilai da dama na yin bimbini.

Jehobah ya annabta cewa zai la’anta ƙasa. Habila ya ga cikar wannan annabci da yake ƙaya da sarƙaƙƙiya sun tsira. Jehobah ya kuma annabta cewa Hawwa’u za ta sha wahala sa’ad da take da juna biyu da kuma a lokacin haihuwa. Habila ya shaida cikar waɗannan kalmomin sa’ad da ake haifan ƙannensa. Jehobah ya hango cewa sakamakon rashin biyayya da suka yi zai sa Hawwa’u ta bukaci Adamu ya ƙaunace ta fiye da kima kuma hakan zai sa shi ya mallake ta. Habila ya ga yadda hakan ya faru tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa. Yadda waɗannan annabcin suka cika sun nuna wa Habila cewa za mu iya dogara da maganar Jehobah. Saboda haka, Habila ya ba da gaskiya cewa alkawarin da Allah ya yi game da “zuriyar” zai cika. Wannan zuriyar ce za ta magance matsalolin ’yan Adam da suka soma a lambun Adnin.—Farawa 3:15-19.

Bayin Jehobah.

Ko da yake a lokacin babu ɗan Adam mai bangaskiya da Habila zai yi koyi da shi, amma akwai mala’iku a duniya da suka kafa wa Habila misali mai kyau. Sa’ad da Jehobah ya kori Adamu da Hawwa’u daga lambun Adnin, ya ɗauki mataki don ya tabbata cewa su da yaransu ba za su sake shiga wannan lambun ba. Jehobah ya saka cherubim da kuma takobi mai harshen wuta da ke juyawa babu fashi domin kada wani ya shiga lambun. Waɗannan cherubim mala’iku ne masu matsayi sosai.—Farawa 3:24.

Ka yi tunanin yadda Habila ya ji sa’ad da yake kallon waɗannan cherubim a lokacin da yake yaro. Da ganin siffarsu, Habila ya fahimci cewa suna da iko sosai. Kuma ‘takobin’ nan mai wuta da ke juyawa babu fashi ma abu ne mai ban al’ajabi. Shin, sa’ad da Habila yake girma, ya taɓa ganin cewa cherubim ɗin sun gaji kuma sun bar wurin aikinsu ne? A’a. Dare da rana, shekara da shekaru, waɗannan halittu masu iko da basira sun ci gaba da kasancewa a wurin. Ta hakan, Habila ya gane cewa Jehobah yana da bayi masu adalci da suke bauta masa babu fashi. Akasin iyalinsa da ba su yi biyayya ga Jehobah ba, Habila ya lura cewa waɗannan cherubim suna da aminci kuma suna biyayya ga Jehobah sosai. Babu shakka, misalin waɗannan mala’ikun ya ƙarfafa bangaskiyarsa.

Habila ya daɗa ƙarfafa bangaskiyarsa ta wajen yin bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya bayyana game da halinsa ta halittunsa da alkawuran da ya yi da kuma misalan bayinsa. Idan muka yi la’akari da misalinsa, zai zama kamar yana mana jawabi, ko ba haka ba? Matasa musamman za su iya kasancewa da gaba gaɗi cewa zai yiwu su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah ko da mene ne ’yan iyalinsu suka yi. Muna da abubuwa da yawa a yau da za su taimaka mana mu kasance da bangaskiya, kamar Littafi Mai Tsarki, abubuwan da Allah ya halitta da kuma misalan amintattun bayin Allah na zamaninmu.

ABIN DA YA SA ALLAH YA KARƁI HAƊAYAR HABILA

Yayin da Habila yana ƙara ganin dalilai na ba da gaskiya ga Jehobah, ya nemi hanyar da zai bayyana bangaskiyarsa. To amma, mene ne ɗan Adam zai iya ba wa Mahaliccin sama da ƙasa? Hakika, Allah ba ya bukatar kyauta ko kuma taimako daga wajen ’yan Adam. Da shigewar lokaci, Habila ya fahimci cewa idan yana da kyakkyawar aniya kuma ya ba da hadaya da dukan zuciyarsa, zai iya faranta ran Ubansa na sama.

Saboda haka, Habila ya shirya ya ba da hadaya daga cikin tumakinsa. Ya zaɓi tumaki mafi kyau, wato, ’ya’yan fari a cikin tumakinsa kuma ya yi hadaya da su. Kayinu ma ya so Allah ya albarkace shi, sai ya shirya  don ya ba da hadayar amfanin gonarsa. Amma muradinsa ba kamar na Habila ba. Yayin da waɗannan ’yan’uwa biyun suke ba da hadayunsu, aniyar kowannensu ya bayyana a fili.

Wataƙila waɗannan ’ya’yan Adamu sun gina bagadi kusa da inda cherubim ɗin suke kuma da wuta suka yi hadayar. A lokacin, waɗannan cherubim ne kaɗai wakilan Jehobah a duniya. Mai zai faru? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji ya kula da Habila da baikonsa.” (Farawa 4:4) Labarin bai nuna mana yadda Jehobah ya bayyana ra’ayinsa ba. Amma me ya sa ya amince da Habila?

Habila ya yi hadaya don yana da imani; Kayinu ma ya yi hadaya, amma ba daga zuciyarsa ba

Shin hadayar da Habila ya bayar ne ya sa hakan? Habila ya yi hadaya da abu mai rai, mai jini, kuma a gaban Allah jini yana wakiltan rai. Wataƙila Habila ya fahimci muhimmancin hakan shi ya sa ya yi hadayar da abu mai rai. Ƙarnuka da yawa bayan haka, Allah ya bukaci a yi masa hadaya da rago marar tabo. Wannan tsarin yana wakiltar hadayar Ɗansa marar aibi, wato, “Ɗan Rago na Allah,” wanda daga baya, ya zub da jininsa a madadin ’yan Adam. (Yohanna 1:29; Fitowa 12:5-7) Amma da alama cewa Habila bai san da wannan shirin ba.

Duk da haka, Habila ya yi hadaya da tumaki mafi kyau daga cikin garkensa. Jehobah ya karɓi hadayar Habila kuma ya amince da shi. Habila ya ɗauki waɗannan matakan ne don yana ƙaunar Jehobah kuma ya ba da gaskiya sosai ga Allah.

Ba hakan yake da Kayinu ba. Jehobah bai “kula da Kayinu da baikonsa ba.” (Farawa 4:5) Kayinu ya yi hadaya da amfanin gona. Shin, hakan ne ya sa Allah ya ƙi karɓar hadayarsa? A’a, domin daga baya, Jehobah ya bar mutanensa su yi hadaya da amfanin gona. (Levitikus 6:14, 15) Amma Littafi Mai Tsarki ya yi bayyani game da Kayinu cewa: “Ayyuka nasa miyagu ne.” (1 Yohanna 3:12) Kayinu yana ganin Allah zai amince da irin ibada da ba ta fito daga zuciya ba. A yau ma mutane da yawa suna da irin wannan ra’ayin. Ba da daɗewa ba, abin da Kayinu ya yi ya nuna cewa bai yi imani da Jehobah ba kuma ba ya ƙaunar Allah.

Sa’ad da Kayinu ya ga cewa Allah bai amince da hadayarsa ba, sai ya fara gāba da Habila maimakon ya yi koyi da shi. Jehobah ya ga cewa Kayinu ya fara kasancewa da mugun nufi a zuciyarsa, sai ya yi masa gargaɗi cikin hankali. Jehobah ya gaya masa cewa mugun tunani da yake yi zai kai shi ga yin zunubi. Ya kuma ce masa idan ya canja halinsa, za a “amsa” masa roƙonsa.—Farawa 4:6, 7.

Kayinu ya yi watsi da gargaɗin da Allah ya yi masa. Sai ya gaya wa ƙanensa su fita yawo a cikin gona. Sa’ad da suka isa wurin, sai Kayinu ya kashe shi. (Farawa 4:8) Ta hakan ne Habila ya zama mutum na farko da aka kashe saboda imaninsa. Ya mutu, amma da sauran rina a kaba.

Kisan Habila ya cancanci sakayya. Kuma Allah ya hukunta Kayinu saboda zunubin da ya yi. (Farawa 4:9-12) Za mu iya koyan darasi daga bangaskiyar da Habila ya nuna. Habila bai daɗe a duniya kamar tsararsa ba, mai yiwuwa shekaru wajen ɗari ne kawai ya yi a duniya. Duk da haka, ya yi rayuwar da ta faranta wa Allah rai. Ya mutu da sanin cewa Allah yana ƙaunarsa kuma shi amintacce ne a gaban Jehobah, Ubansa na sama. (Ibraniyawa 11:4) Saboda haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ba zai manta da shi ba, zai ta da shi daga matattu sa’ad da aka mai da duniya aljanna. (Yohanna 5:28, 29) Za ka so ka gan shi a aljanna? Idan amsarka e ce, to ka ƙudura cewa za ka saurari jawabinsa kuma ka yi koyi da mafificin imaninsa.

^ sakin layi na 8 Wannan furucin “farkon duniya” yana nufin watsa iri kuma hakan yana da alaƙa da haihuwa. Saboda haka, wannan furucin ya shafi zuriyar ’yan Adam da aka fara haifa. Amma, me ya sa Yesu ya ambaci Habila sa’ad da yake magana game da “farkon duniya” a maimakon Kayinu, wanda shi ne ɗa na fari? Domin tunanin Kayinu da ayyukansa sun nuna cewa ya yi wa Jehobah tawaye ne da gangan. Da halama cewa hukuncin da aka yi wa Kayinu ɗaya ne da na iyayensa, wato, ba za a ta da shi daga matattu ba.