Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi

Ka nemi shawarwari masu kyau da za su taimaka maka ka yi nasara a rayuwarka.

TAMBAYA TA 1

Na San Kaina Kuwa?

Idan ka san baiwarka da halayenka da kasawarka da kuma makasudanka, hakan zai taimaka maka ka yanke shawarar da ta dace sa’ad da ka fuskanci matsi.

TAMBAYA TA 2

Me Ya Sa Nake Yawan Damuwa da Surar Jikina?

Shin kana bakin ciki don abin da ka gani a madubi? Wadanne matakai ne za ka dauka don ka inganta surar jikinka?

TAMBAYA TA 3

Ta Yaya Zan Rika Tattaunawa da Iyayena?

Wadannan abubuwa za su sa ya yi maka sauki ka tattauna da iyayenka.

TAMBAYA TA 4

Mene ne Ya Kamata In Yi Sa’ad da Na Yi Kuskure?

Nan ba da dadewa ba za ka yi kuskure don kowa ma yana yin kuskure. Amma, mene ne za ka yi idan hakan ya faru?

TAMBAYA TA 5

Me Zan Yi Idan Aka Zolaye Ni a Makaranta?

Kana da karfi. Za ka iya bugun azzalumi ba tare da yin amfani da damtse ba.

TAMBAYA TA  6

Ta Yaya Zan Ki Matsi Daga Tsarana?

Yin abin da ya dace bai da sauki.

TAMBAYA TA 7

Me Zan Yi Idan Aka Matsa Mini In Yi Zina?

Ka yi la’akari da sakamakon da wasu matasa suka samu sa’ad da suka yi zina kafin aure.

TAMBAYA TA 8

Me Ya Kamata In Sani Game da Cin Zarafi ta Hanyar Lalata?

Matasa ne suka fi fuskantar wannan mugun yanayin. Mene ne za ku yi a irin wannan yanayin?

TAMBAYA TA 9

Shin Ya Kamata in Yi Imani da Koyarwar Juyin Halitta?

Wane bayani ne ya fi dacewa?

TAMBAYA TA 10

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?

Mutane da yawa sun ce Littafi Mai Tsarki yana cike ne da tatsuniya, sun ce tsohon yayi ne, ko kuma yana da wuyar fahimta. Hakan ba gaskiya ba ne.