Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 1

Na San Kaina Kuwa?

Na San Kaina Kuwa?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Idan ka san kanka da kuma abin da ka yi imani da shi, hakan zai taimaka maka ka yanke shawarwarin da suka dace sa’ad da kake fuskantar matsi.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Karen ta je liyafa, ba ta yi minti goma da zuwa ba sai ta ji wata murya daga bayanta.

“Me ya sa kika tsaya a nan haka kawai?”

Da Karen ta juya, sai ta ga ƙawarta Jessica tana riƙe da kwalaben giya guda biyu. Jessica ta miƙa mata kwalba guda kuma ta ce, “Ke ba ƙaramar yarinya ba ce, ki sha ki more rayuwarki, ko kina jin tsoro ne?”

Karen ba ta so ta karɓa, amma Jessica ƙawarta ce. Kuma ba ta son Jessica ta ɗauka cewa ita ba mai son jin daɗi ba ce. Ƙari ga haka, Jessica yarinya ce mai hankali. Idan har tana shan giya, hakan ya nuna cewa shan giya ba laifi ba ne. Sai ta soma tunani cewa: ‘Ai giya ce kawai, ba shan ƙwaya ba.’

Idan ka sami kanka a yanayin da Karen take ciki, me za ka yi?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

Idan ka san kanka da kyau kuma ka gaskata da abin da ka yi imani da shi, hakan zai taimaka maka ka yanke shawarar da ta dace a irin wannan yanayin. Sanin kanka da kyau zai taimaka maka ka yi abin da ya dace maimakon ka bari mutane su riƙa juya ka kamar waina.—1 Korintiyawa 9:26, 27.

Ta yaya za ka iya kasancewa da gaba gaɗin yin abin da ya dace? Waɗannan tambayoyi na gaba za su taimaka maka ka yi hakan.

1 WAƊANNE HALAYE MASU KYAU NE NAKE DA SU?

Idan ka san halayenka masu kyau da kuma baiwarka, hakan zai sa ka kasance da gaba gaɗi.

MISALI DAGA LITTAFI MAI TSARKI: Manzo Bulus ya ce: “Ko da [shi] marar-lafazin baki ne,” shi “ba marar-ilimi ba ne.” (2 Korintiyawa 11:6) Saboda Bulus ya fahimci Littafi Mai Tsarki sosai, ya kasance da gaba gaɗi sa’ad da mutane suka ƙalubalance shi. Bai ƙyale baƙar maganarsu ta sa shi sanyin gwiwa ba.—2 Korintiyawa 10:10; 11:5.

KA BINCIKA KANKA: Ka rubuta wata baiwarka.

Yanzu ka rubuta wani hali mai kyau da kake da shi. (Alal misali, kai mai ƙaunar mutane ne? kai mai son ba da kyauta ne? ka mai aminci ne? kai mai riƙe amana ne?)

2 WAƊANNE KASAWA NE NAKE DA SU?

Idan muka bar kasawarmu su mamaye halayenmu, hakan zai ɓata tarbiyyarmu.

MISALI DAGA LITTAFI MAI TSARKI: Bulus ya san kasawarsa. Ya ce: “Ina murna da shari’ar Allah bisa ga mutum na ciki: amma ina ganin wata shari’a dabam a cikin gaɓaɓuwana, tana yaƙi da shari’ar hankalina, tana saka ni bauta ƙarƙashin shari’ar zunubi.”—Romawa 7:22, 23.

KA BINCIKA KANKA: Wace kasawarka ce kake so ka gyara?

3 WAƊANNE MAƘASUDAI NE NAKE DA SU?

Shin za ka shiga tasi kuma ka gaya wa direban ya riƙa zagayawa da kai har sai mansa ya ƙare? Yin hakan wawanci ne kuma ɓarnan kuɗi ne!

Mene ne darasin? Idan ka kafa maƙasudai, hakan zai sa rayuwarka ta kasance da ma’ana. Ka san abin da kake so da kuma yadda za ka cim ma hakan.

MISALI DAGA LITTAFI MAI TSARKI: Bulus ya ce ‘gudun’ da yake yi ba na banza ba ne. (1 Korintiyawa 9:26, LMT) Bulus bai yi zaman jiran sa’a ba, maimakon haka, ya kafa maƙasudai kuma ya ɗauki matakai don ya cim ma hakan.—Filibbiyawa 3:12-14.

KA BINCIKA KANKA: Ka rubuta maƙasudai uku da za ka so ka cim ma cikin shekara ɗaya mai zuwa.

4 MENE NE NA YI IMANI DA SHI?

Idan ka san kanka da kyau kuma ka gaskata da abin da ka yi imani da shi, za ka zama kamar bishiyar da ke tsaye daram, wadda guguwa mai ƙarfi ba za ta iya kaɗawa ba

Idan kana shakka, ba za ka iya tsai da shawara ba. Za ka zama kamar hawainiyar da take canja kala bisa ga launin yanayin mahallinta, wato za ka riƙa bin ra’ayin tsararka. Hakan zai nuna cewa ba ka san kanka ba.

Akasin haka, idan kana yin abubuwa bisa ga imaninka, hakan zai nuna cewa ka san kanka kuma ba za ka yarda mutane su riƙa rinjayar ka ba.

MISALI DAGA LITTAFI MAI TSARKI: Lokacin da annabi Daniyel yake matashi, ya “yi ƙuduri a zuciyarsa” cewa zai bi dokokin Allah duk da cewa yana nesa da inda iyalinsa suke. (Daniyel 1:8) Hakan ya nuna cewa ya tabbata da abin da ya yi imani da shi. Daniyel ya bi imaninsa.

KA BINCIKA KANKA: Mene ne ka yi imani da shi? Alal misali: Ka gaskata cewa akwai Allah? Idan amsarka e ce, me ya sa? Wane tabbaci ne kake da shi cewa akwai Allah?

Ka gaskata cewa ƙa’idodin Allah game da ɗabi’a za su amfane ka? Idan haka ne, me ya sa?

Shin za ka so ka zama kamar ganyen bishiyar da iska yake kaɗawa ko’ina, ko kuma za ka so ka zama kamar bishiyar da za ta tsaya daram ko da ana guguwar iska mai tsanani? Idan ka ɗauki matakan da za su sa ka san kanka sosai da kuma abin da ka yi imani da shi, za ka zama kamar wannan bishiyar. Hakika, za ka san kanka sosai.