Ka Kusaci Jehobah
Allah yana so ka kusace shi. Wannan littafin zai nuna maka yadda za ka iya yin hakan.
Gabatarwa
Za ka iya kulla abota mai karfi sosai da Jehobah.
BABI NA 1
“Lallai, Wannan Allahnmu Ne!”
Me ya sa Musa ya tambayi Allah sunansa duk da cewa ya riga ya san sunan?
BABI NA 2
Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?
Jehobah Allah, Mahaliccin sama da duniya ya ba mu gayyata kuma ya yi mana alkawari.
BABI NA 3
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne” Jehobah
Me ya sa Baibul ya kamanta tsarki da jamali?
SASHE NA 1
Mai “Girman Iko”
BABI NA 4
Jehobah “Mai Girma Ne”
Shin ya kamata karfin Allah ya sa mu rika jin tsoron shi? Idan ka ce e ko a’a, duka amsar daidai ne.
BABI NA 5
Ikon Halitta—‘Mahaliccin Sama da Kasa’
Daga rana mai girma sosai zuwa karamin tsunsun hummingbird, halittun Allah za su iya koya mana abubuwa masu muhimmnaci game da shi.
BABI NA 7
Ikon Kāriya—Allah “Wurin Buyanmu” Ne
Allah yana kāre bayinsa a hanyoyi biyu, amma hanya daya ya fi muhimmanci sosai.
BABI NA 8
Ikon Maidowa—Jehobah Yana Yin “Kome Sabo”
Jehobah ya riga ya maido da bauta ta gaskiya. Mene ne zai maido da su a nan gaba?
BABI NA 9
“Almasihu Shi Ikon Allah” Ne
Mene ne mu’ujizai da koyarwar Yesu suka nuna game da Jehobah?
BABI NA 10
“Ku Ɗauki Misali Daga Wurin Allah” Wajen Amfani da Iko
Kana da iko fiye da yadda kake tsammani. Ta yaya za ka yi amfani da shi yadda ya dace?
SASHE NA 2
Jehobah “Yana Ƙaunar Shari’ar Gaskiya”
BABI NA 12
Allah Yana Yin Rashin Adalci Ne?
Idan Jehobah ya tsani rashin adalci, me ya sa duniya ke cike da rashin adalci?
BABI NA 14
Jehobah Ya Yi Tanadin Fansa don “Mutane da Yawa”
Koyarwa mai sauki amma mai muhimmanci zai iya taimaka maka ka kusaci Allah.
BABI NA 15
Yesu “Ya Kafa Yin Gaskiya a Duniya”
Ta yaya Yesu ya nuna adalci a da? Ta yaya yake yin hakan a yau? Kuma ta yaya zai sa a rika yin adalci a nan gaba?
BABI NA 16
“Ka Yi Adalci” Wajen Tafiya da Allah
Adalci ya kunshi yadda muke daukan abin da ya dace da wanda bai dace ba da kuma yadda muke bi da mutane.
SASHE NA 3
“Mai Zuciyar Hikima”
BABI NA 17
“Ina Misalin Zurfin . . . Hikimar Allah!”
Me ya sa hikimar Allah ta fi iliminsa da fahintarsa da kuma saninsa?
BABI NA 18
Hikima Cikin “Maganar Allah”
Me ya sa Allah ya yi amfani da ’yan Adam don rubuta Kalmarsa, kuma me ya sa take dauke da wasu abubuwa wasu kuma babu?
BABI NA 20
“Mai Zuciyar Hikima”—Amma Kuma Mai Tawali’u
Ta yaya mahaliccin dukan duniya yake da saukin kai?
BABI NA 21
Yesu Ya Bayyana ‘Hikima Daga Allah’
Yesu ya iya koyarwa sosai har ma sojojin da aka tura su kama shi suka kasa yin hakan!
BABI NA 22
“Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa A Rayuwarka?
Littafi Mai Tsarki ya bayyana abubuwa 4 da za su taimaka maka ka kasance da hikima irin ta Allah.
SASHE NA 4
“Allah Ƙauna Ne”
BABI NA 24
Babu Abin da Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”
Ka yi banza da raꞌayin nan cewa Allah ba zai taba kaunar ka ba, kuma ba ka da wani amfani a gabansa.
BABI NA 25
“Yawan Jinƙai . . . na Allahnmu”
A wace hanya ce yadda Allah yake ji game da kai ya yi kama da yadda mahaifiya take ji game da jaririnta?
BABI NA 26
Allah “Mai Yin Gafara”
Da yake Jehobah zai iya tunawa da kome, a wace hanya ce zai gafarta zunubi kuma ya manta da shi?
BABI NA 27
“Allah Mai Nagarta Ne da Babu Kamarsa!”
Me ake nufi sa’ad da aka ce Allah yana nuna nagarta?
BABI NA 29
“Ku Sani Kuma Ƙaunar Kristi”
Fannoni uku da Yesu ya nuna kauna duk sun nuna yadda Jehobah yake nuna wa mutane kauna.
BABI NA 30
“Ku Yi Zaman Ƙauna”
Korintiyawa na farko yan nuna hanyoyi da yawa da za mu iya nuna kauna.
BABI NA 31
‘Ka Yi Kusa da Allah, Shi Kuwa Zai Yi Kusa da Kai’
Wace tambaya mafi muhimmanci ce za ka iya yi wa kanka? Mece ce amsarka?