BABI NA 9

“Almasihu Shi Ikon Allah” Ne

“Almasihu Shi Ikon Allah” Ne

1-3. (a) Wane abu mai razanarwa almajiran suka fuskanta a cikin Tekun Galili, kuma Mene ne Yesu ya yi? (b) Me ya sa ya dace da manzo Bulus ya ce “Almasihu shi ikon Allah” ne?

 ALMAJIRAN sun razana. Suna ƙetare Tekun Galili sai hadari ya ɗauro farat ɗaya. Babu shakka sun saba da hadari a wannan tekun da ma—ban da haka ma, wasu cikin mutanen ƙwararru ne wajen sū. a (Matiyu 4:18, 19) Amma wannan “babban hadari mai iska,” nan da nan ya ta da rakuman ruwa ya sa ruwan ya fusata. Mutanen suka yi aiki tuƙuru domin su riƙe jirgin amma ina, hadarin ya fi ƙarfinsu. Rakuman ruwa suna “bubbuga jirgin,” wanda ruwa ya fara cika shi. Duk da rikicewar, Yesu yana barci mai zurfi a bayan jirgin, domin gajiya daga koyar da taro a ranar. Da suka tsorata domin rayukansu, sai almajiran suka ta da shi, suna roƙo: “Ubangiji, ka cece mu, za mu halaka!”—Markus 4:35-38; Matiyu 8:23-25.

2 Yesu bai tsorata ba. Da cikakken tabbaci, ya tsauta wa iskar da kuma tekun: “Natsu! Ka yi shiru!” Nan da nan, iskar da tekun suka yi biyayya, hadarin ya watse, rakuman ruwan suka baje, sai “wuri duk ya yi tsit.” Sai wani irin tsoro ya kama almajiran. Suka ce wa junansu, “Wane ne wannan?” Hakika, wane irin mutum ne wannan da ya tsauta wa iska da kuma teku kamar yana yi wa yaro mai taurin kai tsawa?—Markus 4:39-41; Matiyu 8:26, 27.

3 Amma Yesu ba mutum ba ne kawai. Ikon Jehobah yana aiki cikinsa a hanyoyi na ban mamaki. Manzo Bulus da aka hure ya ce: “Almasihu shi ikon Allah.” (1 Korintiyawa 1:24) A wace hanya ce ikon Allah ya bayyana wajen Yesu? Kuma wace rinjaya, yadda Yesu ya yi amfani da ikonsa za ta yi a rayukanmu?

Ikon Ɗan Allah Makaɗaici

4, 5. (a) Jehobah ya ba wa Ɗansa makaɗaici wane irin iko? (b) Ta yaya aka shirya Ɗan domin ya yi nufe-nufen Ubansa wajen halitta?

4 Ka yi la’akari da ikon da Yesu yake da shi lokacin rayuwarsa a sama kafin ya zama mutum. Jehobah ya nuna “ikonsa na har abada” sa’ad da ya halicci Ɗansa makaɗaici, wanda ya zo duniya aka san shi da Yesu Kristi. (Romawa 1:20; Kolosiyawa 1:15) Daga baya, Jehobah ya ba wa Ɗansa iko mai girma, ya sa shi ya yi nufe-nufensa na halitta. Game da Ɗan, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ta wurinsa ne aka yi dukan abubuwa, kuma babu wani abu a cikin dukan halittar da aka yi wadda ba tare da shi aka yi ba.”—Yohanna 1:3.

5 Za mu iya fahimtar girman wannan aiki kaɗan ne kawai. Ka yi tunanin ikon da ake bukata don a sa miliyoyin mala’iku masu ƙarfi su rayu, wannan sararin sama da biliyoyin dami damin taurarinta, da kuma duniya da iri-irin rayukanta masu yawa. Domin ya cim ma waɗannan ayyuka, makaɗaicin Ɗan yana da iko mafi ƙarfi a dukan sararin sama a hannunsa, wato ruhu mai tsarki na Allah. Ɗansa ya yi farin ciki ƙwarai da ya kasance Gwanin Aiki, da Jehobah ya yi amfani da shi wajen halittar dukan abu.—Karin Magana 8:22-31.

6. Bayan mutuwarsa a duniya da tashinsa daga matattu, wane iko aka ba wa Yesu?

6 Shin makaɗaicin Ɗan zai samu ƙarin iko ne? Bayan mutuwarsa a duniya da kuma tashinsa daga matattu, ya ce: “An ba ni dukan iko a sama da kuma nan duniya.” (Matiyu 28:18) Hakika, an ba wa Yesu iyawa da kuma damar nuna iko a dukan sararin sama. An ba wa “Sarkin sarakuna, da kuma Ubangijin iyayengiji,” iko ya “kawar da dukan masu mulki, da mulki, da iko.” Wanda ake gani da wanda ba a gani, da ke yin gaba da Ubansa. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 19:16; 1 Korintiyawa 15:24-26) Allah “ya mai da dukan abu a ƙarƙashin” ikon Yesu, amma ban da Jehobah da kansa.—Ibraniyawa 2:8; 1 Korintiyawa 15:27.

7. Me ya sa za mu tabbata cewa Yesu ba zai taɓa yin ɓarna da ikon da Jehobah ya saka cikin hannunsa ba?

7 Muna bukatar mu damu ne cewa Yesu wataƙila ya yi ɓarna da ikonsa? Ko kaɗan! Yesu yana ƙaunar Ubansa da gaske kuma ba zai taɓa yin wani abin da zai ɓata masa rai ba. (Yohanna 8:29; 14:31) Yesu ya sani cewa Jehobah ba ya ɓarna da ikonsa mafi girma. Yesu ya lura da kansa cewa Jehobah yana neman zarafi “domin ya ƙarfafa waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.” (2 Tarihi 16:9) Hakika, Yesu yana da irin ƙaunar Ubansa ga ’yan Adam, saboda haka, za mu iya tabbata cewa Yesu zai yi amfani da ikonsa a nagarin hanya. (Yohanna 13:1) Yesu ya kafa tarihi marar aibi a wannan batun. Bari mu bincika ikon da yake da shi lokacin da yake duniya da kuma yadda ya motsa ya yi amfani da shi.

“Mai Iko Cikin . . . Magana”

8. Bayan an shafe shi, Mene ne aka ba wa Yesu ikon ya yi, kuma yaya ya yi amfani da ikonsa?

8 Babu shakka cewa Yesu bai yi mu’ujiza ba sa’ad da yake yaro yake girma a Nazarat. Amma wannan ya canja bayan da ya yi baftisma a shekara ta 29 A.Z., yana ɗan shekara 30. (Luka 3:21-23) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Allah ya shafe shi da ruhu mai tsarki, da kuma iko. Domin Allah yana tare da shi, ya dinga zagayawa yana yin aikin alheri, yana warkar da waɗanda Shaiɗan ya matsa musu.” (Ayyukan Manzanni 10:38) Shin “aikin alheri” bai nuna ba cewa Yesu ya yi amfani da ikonsa a hanya mai kyau? Bayan an shafe shi, ya zama annabi “mai iko cikin ayyuka da magana.”—Luka 24:19.

9-11. (a) A ina Yesu ya yi yawancin koyarwarsa, kuma wane ƙalubale ya fuskanta? (b) Me ya sa taron suka yi mamakin koyarwar Yesu?

9 Ta yaya Yesu ya kasance mai iko cikin magana? Ya koyar sau da yawa a fili—a bakin kogi da kuma gefen duwatsu har ma da tituna da kuma kasuwoyi. (Markus 6:53-56; Luka 5:1-3; 13:26) Da a ce maganarsa ba ta ba masu sauraronsa sha’awa ba da sai su yi tafiyarsu. A zamanin da babu littattafai da aka buga, masu sauraro da suka ɗauki koyarwarsa da muhimmanci dole ne su riƙe maganarsa cikin zuciyarsu. Saboda haka, koyarwar Yesu dole ne ta kasance da ban sha’awa ƙwarai, a bayyane sarai, kuma ta kasance ba ta da wuyar tunawa. Amma wannan ƙalubalen bai kasance matsala ba ga Yesu. Alal misali, ka yi la’akari da Huɗubarsa a kan Dutse.

10 Wata safiya a farkon shekara ta 31 A.Z., jama’a sun taru a gefen dutse kusa da Tekun Galili. Wasu sun zo daga Yahudiya da kuma Urushalima, tafiyar mil 60 ko 70. Wasu sun zo daga iyakar Tyre da Sidon kusa da teku, ta arewa. Majiyata da yawa suka matso kusa da Yesu su taɓa shi, kuma ya warkar da dukansu. Sa’ad da babu ko ɗaya cikinsu da yake ciwo, sai ya fara koyar da su. (Luka 6:17-19) Sa’ad da ya gama magana bayan ɗan lokaci, dukansu suka yi mamakin abin da suka ji. Me ya sa?

11 Bayan wasu shekaru, wani da ya saurari huɗubar ya rubuta: “Taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koya musu kamar mutumin da yake da iko.” (Matiyu 7:28, 29) Yesu ya yi magana da iko da suka so. Ya yi magana a madadin Allah kuma ya tabbatar da koyarwarsa da ikon Kalmar Allah. (Yohanna 7:16) Furcin Yesu sun fita sarai, gargaɗinsa suna motsawa, maganarsa ta fi gaban a musanta. Maganarsa tana taɓa cibiyar batu da kuma zuciyar masu sauraronsa. Ya koya musu yadda za su sami farin ciki, yadda za su yi addu’a, da kuma yadda za su gina rayuwa mai kwanciyar rai a nan gaba. (Matiyu 5:3–7:27) Kalmominsa sun taɓa zukatan waɗanda suke neman gaskiya da kuma adalci. Irin waɗannan mutane suna shirye su “ƙi” kansu su bar kome domin su bi shi. (Matiyu 16:24; Luka 5:10, 11) Wannan shaida ce ga iko cikin maganar Yesu!

“Mai Iko Cikin Ayyuka”

12, 13. A wace hanya ce Yesu yake da “iko cikin ayyuka,” kuma mu’ujizojinsa wane irin bambanci ne suke da shi?

12 Yesu yana kuma da iko “cikin ayyuka.” (Luka 24:19) Lingila ta ba da rahotannin ayyukan mu’ujiza takamammu guda 30 da ya yi, duka cikin “ikon Ubangiji.” b (Luka 5:17) Mu’ujizojin Yesu sun taɓa rayukan dubban mutane. Ka yi la’akar da mu’ujizoji biyu kawai, wato ya ciyar da maza 5,000, daga baya maza 4,000. Idan an haɗa da mata da yara, za a sami ƙarin dubban mutane!—Matiyu 14:13-21; 15:32-38.

13 Mu’ujizojin Yesu iri-iri ne. Yana da iko bisa aljanu, yana fitar da su da sauƙi. (Luka 9:37-43) Yana da iko bisa abubuwa na zahiri, ya juya ruwa ya zama giya. (Yohanna 2:1-11) Ka yi tunanin irin mamakin da almajiransa suka yi, sa’ad da suka ga “Yesu yana tafiya a kan ruwa.” (Yohanna 6:18, 19) Ya yi iko bisa cuta, ya warkar da naƙasa, ciwo mai tsanani, da kuma cututtuka masu razana rai. (Markus 3:1-5; Yohanna 4:46-54) Ya yi irin wannan warkarwa a hanyoyi dabam dabam. An warkar da wasu daga nesa, wasu kuma Yesu ya taɓa su. (Matiyu 8:2, 3, 5-13) Wasu sun warke a take, wasu kuma sannu a hankali.—Markus 8:22-25; Luka 8:43, 44.

Sun ga “Yesu yana tafiya a kan ruwa”

14. A cikin waɗanne yanayi ne Yesu ya nuna yana da iko ya sa a daina mutuwa?

14 Mafifici ma, Yesu yana da ikon sa a daina mutuwa. A lokaci uku dabam dabam da aka rubuta, ya ta da matattu, ya mayar da yarinya ’yar shekara 12 ga iyayenta, ɗan tilo ga uwarsa gwauruwa, kuma ƙaunatacce ga ƙannensa mata. (Luka 7:11-15; 8:49-56; Yohanna 11:38-44) Ba yanayi da ya gagari Yesu. Ya ta da ’yar shekara 12 daga gado bayan ta mutu ba da daɗewa ba. Ya ta da ɗan gwauruwa daga kan makara, a ranar da ya mutu. Kuma ya ta da Li’azaru daga kabari bayan ya mutu da kwana huɗu.

Amfani da Iko Cikin Rashin Son Kai, Cikin Fahimi, da Kuma La’akari

15, 16. Wane tabbaci ne ake da shi cewa Yesu ba shi da son kai wajen amfani da ikonsa?

15 Za ka yi tunanin alamun yin ɓarna da iko da a ce ikon Yesu yana hannun masarauta ajizai? Amma Yesu ba shi da zunubi. (1 Bitrus 2:22) Bai ƙyale son kai da dogon buri su lalata shi ba, da kuma haɗama da take tura mutane ajizai su yi amfani da ikonsu su zalunci wasu.

16 Yesu bai nuna son kai ba wajen amfani da ikonsa, bai taɓa amfani da ikonsa ba domin ya amfani kansa. Sa’ad da yake jin yunwa, ya ƙi ya mai da duwatsu su zama burodi wa kansa. (Matiyu 4:1-4) Ɗan abin da yake da shi tabbaci ne cewa bai amfana ba da abin duniya ta wajen amfani da ikonsa. (Matiyu 8:20) Da akwai ƙarin tabbaci cewa ayyukansa na iko ya yi ne ba da son kai ba. Sa’ad da ya yi mu’ujizoji, yana yin haka domin sadaukarwa. Sa’ad da ya warkar da marasa lafiya, iko yana fita a jikinsa. Yana jin fitar ikonsa, har a lokacin warkar da mutum guda kawai. (Markus 5:25-34) Duk da haka, ya ƙyale taron mutane su taɓa shi, kuma sukan samu lafiya. (Luka 6:19) Hakika kuwa sadaukarwa ce!

17. Ta yaya Yesu ya nuna cewa yana da fahimi wajen amfani da ikonsa?

17 Yesu yana da fahimi wajen amfani da ikonsa. Bai taɓa yin mu’ujiza ba kawai domin ya nuna iko ko kuma yi wasan banza ba. (Matiyu 4:5-7) Bai yarda ya ba da alamu ba domin ya gamsar da muradin da bai dace ba na Hirudus. (Luka 23:8, 9) Maimakon ya sanar da ikonsa, Yesu sau da yawa ya umurci waɗanda ya warkar kada su gaya wa kowa. (Markus 5:43; 7:36) Ba ya so mutane su zo ga kammala game da shi kawai bisa jita-jita.—Matiyu 12:15-19.

18-20. (a) Mene ne ya rinjayi yadda Yesu ya yi amfani da ikonsa? (b) Yaya kake ji game da yadda Yesu ya warkar da wani kurma?

18 Wannan mutum mai iko Yesu, ya bambanta ƙwarai daga sarakuna waɗanda suke nuna iko cikin rashin la’akari da bukatu da kuma wahalar wasu. Yesu yana ƙaunar mutane. Ganin waɗanda suke wahala yana taɓa shi ƙwarai kuma yana motsa shi ya taimake su. (Matiyu 14:14) Yana la’akari da yadda suke ji da kuma bukatunsu, kuma ƙaunarsa tana rinjayar yadda yake amfani da ikonsa. Akwai misali mai sosa zuciya a Markus 7:31-37.

19 A wannan lokacin, taro mai girma sun samu Yesu kuma sun kawo masa marasa lafiya da yawa, kuma ya warkar da duka. (Matiyu 15:29, 30) Amma Yesu ya fitar da mutum ɗaya domin taimako na musamman. Mutumin kurma ne kuma baya iya magana. Wataƙila ya lura da tozartuwar wannan mutumin. Yesu ya fitar da mutumin daga cikin jama’ar zuwa wajen da babu kowa. Sai Yesu ya yi amfani da bebenci ya gaya wa mutumin abin da yake so ya yi. Ya “sa yatsunsa a kunnuwansa, ya tofa miyau, ya kuma taɓa harshensa da miyaun.” c (Markus 7:33) Sai Yesu ya duba sama ya yi addu’a. Waɗannan ayyuka za su ce wa mutumin, ‘Abin da nake so na yi maka da ikon Allah ne.’ A ƙarshe Yesu ya ce: “Buɗe.” (Markus 7:34) Sai mutumin ya soma ji kuma yana magana daidai.

20 Lalle yana sosa zuciya a yi tunani cewa har sa’ad da yake amfani da ikon da Allah ya ba shi ya warkar da mawahalta, Yesu ya nuna juyayi ga yadda suke ji! Ba ya ba da tabbaci ne mu san cewa Jehobah ya saka Mulkin Almasihu cikin hannun irin wannan Masarauci mai ƙauna da la’akari?

Annabcin Abubuwa da Suke Zuwa

21, 22. (a) Mene ne mu’ujizojin Yesu suke annabtawa? (b) Domin Yesu yana da iko bisa yanayi, me za mu yi tsammaninsa a ƙarƙashin Mulkinsa?

21 Mu’ujizojin da Yesu ya yi a duniya alama ce kawai ta albarka mai girma da take zuwa a ƙarƙashin sarautarsa ta kirki. A sabuwar duniya ta Allah, Yesu zai sake yin mu’ujizoji—amma a dukan duniya! Ka yi la’akari da abubuwa masu ban sha’awa da suke zuwa a nan gaba.

22 Yesu zai mai da yanayin duniya cikakke. Ka tuna cewa ya nuna iko ta wajen sa hadari ya lafa. Hakika, a ƙarƙashin Mulkin Kristi, ’yan Adam ba za su bukaci su tsorata cewa hadari na wajajen tekun Sin, girgizar ƙasa, gobarar dutse, ko wasu bala’i za su yi musu lahani ba. Tun da Yesu shi ne Gwanin Aiki, wanda Jehobah ya yi amfani da shi wajen halittar duniya da dukan rai da ke bisanta, yana da cikakken sanin yanayin duniya. Ya san yadda zai iya amfani da arzikinta yadda ya dace. A ƙarƙashin mulkinsa, dukan duniya za a juya ta zuwa Aljanna.—Luka 23:43.

23. Tun da Sarki ne, ta yaya Yesu zai biya bukatun ’yan Adam?

23 Yaya game da bukatu na ’yan Adam? Da yake Yesu ya iya ciyar da dubbai sosai, ta wajen amfani da abubuwa kaɗan, ya tabbatar mana cewa sarautarsa za ta kawo ’yanci daga yunwa. Hakika, abinci da yawa, idan aka raba shi daidai, zai kawo ƙarshen yunwa har abada. (Zabura 72:16) Ikonsa bisa ciwo da cuta ya nuna mana cewa marasa lafiya, makafi, kurame, naƙasassu, da kuma guragu za su warke—gabaki ɗaya kuma na dindindin. (Ishaya 33:24; 35:5, 6) Iyawarsa na ta da matattu kuma ya tabbatar da cewa girmansa na Sarkin sama ya haɗa da ikonsa ya ta da miliyoyin mutane babu iyaka da Ubansa zai yi farin cikin tunawa da su.—Yohanna 5:28, 29.

24. Yayin da muke bimbini bisa ikon Yesu, Mene ne ya kamata mu tuna da shi, kuma me ya sa?

24 Yayin da muke bimbini bisa ikon Yesu, bari mu tuna cewa wannan Ɗan ya yi kamiltaccen koyi da Ubansa. (Yohanna 14:9) Amfani da iko na Yesu ya bayyana sarai yadda Jehobah yake yin amfani da iko. Alal misali, ka yi tunanin hanya ta ƙauna da Yesu ya warkar da wani kuturu. Ya ji tausayinsa, ya taɓa mutumin ya ce: “Na yarda”! (Markus 1:40-42) Ta wajen tarihi irin wannan, Jehobah yana cewa ne, ‘Haka nake amfani da ikona!’ Ba ka motsa ba ka yaba wa Allah mai girma kuma ka yi masa godiya domin yana amfani da ikonsa a hanya ta ƙauna?

a Tasowar hadari ba labari abin yau da kullum ne a Tekun Galili. Domin tekun ta yi ƙasa ainu (wajen ƙafa 700 ƙasa da bakin teku), iska ya fi zafi a wurin fiye da wuraren da suke kewaye, kuma wannan yana jawo hadari. Iska mai ƙarfi takan sauƙo daga Kwarin Urdun na Dutsen Hermon, da yake arewaci. In wuri ya yi shuru yanzu an jima hadari ya fara.

b Bugu da ƙari, Lingila a wani lokaci tana tara mu’ujizoji da yawa a ƙarƙashin kwatanci guda. Alal misali, a wani lokaci “dukan mutanen garin” suka zo su gan shi, kuma ya warkar da masu ciwo “da yawa.”—Markus 1:32-34.

c Tofar da yau alama ce ta warkarwa da Yahudawa da kuma ’Yan Al’umma suka yarda da ita, kuma yin amfani da yau wajen magani an ba da rahoton haka a rubuce-rubucen malaman Yahudawa. Wataƙila Yesu ya tofar da yau ne ya gaya wa mutumin cewa ya kusa ya warke. Ko yaya dai, Yesu ba amfani ya yi da yaunsa wajen magani ba.