Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 9

Abin da Za Mu Iya Koya Daga Almasihu Shugaba

Abin da Za Mu Iya Koya Daga Almasihu Shugaba

ALLAH ya annabta cewa zai naɗa Almasihu a matsayin Shugaba ga dukan mutane. Allah ya san irin shugaban da muke bukata kuma ya zaɓar mana Shugaba mafi kyau. Wane irin Shugaba ne Almasihu ya zama? Ya zama babban janar ne? Ƙwararren ɗan siyasa? Ko ɗan falsafa? In ji Nassosi Masu Tsarki, Almasihu annabi ne na musamman, wato, Yesu Kristi.—Matta 23:10.

Allah ya tabbatar da cewa an haifi Yesu a matsayin kamiltacce, mai tsarki. Ƙari ga hakan, Yesu ya yi tsayayya da dukan ƙoƙarin da Shaiɗan ya yi don ya ɓata shi. A kalamansa da ayyukansa, Yesu ya nuna yadda Allah yake yin amfani da ikonsa, adalcinsa, hikimarsa da kuma ƙauna. Ka yi la’akari da yadda za mu iya yin koyi da misalin Yesu.

Yesu ya taimaka wa mutane sosai

Ya yi amfani da ikon da Allah ya ba shi wajen taimaka wa wasu. Yesu ya kula da mutane sosai, kuma ya yi amfani da ikonsa don kula da bukatunsu. Ya ce: “Ina jin juyayin taron nan, gama . . . ba su da abin da za su ci.” (Markus 8:2) Bayan haka, ta hanyar mu’ujiza, Yesu ya ciyar da babban taron da suka zo su saurari koyarwarsa.

Yesu ya kuma yi tafiye-tafiye, yana koyarwa yana kuma “warkar da kowace irin cuta da kowane irin rashin lafiya a cikin mutane.” (Matta 4:23) Domin hakan, mutane da yawa suka bi shi, kuma “dukan taro fa suka nemi su taɓa shi, gama iko yana fitowa daga wurinsa, yana warkar da dukansu.” (Luka 6:19) Hakika, Yesu ya zo, “ba domin a yi masa bauta ba, amma domin shi bauta wa waɗansu, shi bada ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28) * Shugabannin ’yan Adam nawa ne suke nuna irin wannan sadaukar da kai?

Yesu yana ƙaunar yara

Ya nuna adalci irin na Allah. Yesu ya bi umurnin da ke cikin dokokin Allah kuma ya aikata su a rayuwarsa. Kamar yadda Nassosi suka annabta, kamar dai yana cewa ne: “Murna na ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.” (Zabura 40:8) Kamar yadda Allah yake yi, Yesu ya girmama kowa, masu kuɗi, talakawa, mace da namiji, babba da ƙarami, ya daraja su kuma bai nuna son kai ba. Da akwai lokacin da almajiran Yesu suka hana iyaye su kawo yaransu wurin Yesu. Yesu ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su: gama na irin waɗannan mulkin Allah ya ke.”—Markus 10:14.

Ya nuna hikima irin ta Allah. Yesu ya fahimci mutane sosai. “Shi da kansa yana sane da abin da ke cikin mutum.” (Yohanna 2:25) Sa’ad da maƙiyan Yesu suka aika maza su kamo shi, su da kansu sun ce: “Babu mutumin da ya taɓa yin magana haka.” Daga ina ne Yesu ya samo hikimarsa? Ya bayyana: “Koyarwana ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni.”—Yohanna 7:16, 46.

Yesu ya warkar da marasa lafiya cikin tausayi

Ya nuna ƙauna irin ta Allah. Yesu ya kuma nuna juyayi ga mutane. Wani mutumin da ke “cike da kuturta” ya roƙe shi: “Ubangiji, idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Cike da juyayi, Yesu ya “miƙa hannu, ya taɓa shi, ya ce, Na yarda; ka tsarkaka. Nan da nan fa kuturta ta rabu da shi.” (Luka 5:12, 13; Markus 1:41, 42) Yesu yana son ya raba mutumin nan da wahalar da yake sha.

Shin Yesu damu da kai? Yesu da kansa ya amsa: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗaukar wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.”—Matta 11:28, 29.

Yesu ne Shugaba mafi kyau da za mu iya samu. Shi ya sa ya aririce mu: “Ku koya daga wurina.” Za ka yi na’am da wannan gayyatar kuwa? Yin hakan zai kai ga rayuwa ta farin ciki.