Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA BIYAR

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah

Fansa—Kyauta Mafi Girma Daga Allah
  • Mecece fansa?

  • Ta yaya aka ba da ita?

  • Menene amfaninta a gareka?

  • Ta yaya za ka nuna godiyarka dominta?

1, 2. (a) Yaushe ne kyauta take da muhimmanci ƙwarai a gareka? (b) Me ya sa za a ce fansa ita ce kyauta mafi muhimmanci da za a taɓa yi maka?

WANE abu ne mafi girma aka taɓa ba ka kyauta? Ba dole ba ne abin da aka bayar ya kasance mai tsada kafin ya zama mai muhimmanci. Hakika, muhimmancin abin da aka ba da kyauta ba dole ba ne a kwatanta shi da farashinsa. Maimakon haka, idan abin da aka ba ka kyauta ya sa ka farin ciki ko kuma ya biya wani muhimmin bukata a rayuwarka, yana da muhimmanci matuƙa a gareka.

2 A dukan kyauta da za ka yi begen a yi maka, da akwai ɗaya da ta fi fice. Kyauta ce da Allah ya yi wa ’yan adam. Jehobah ya ba mu abubuwa masu yawan gaske, amma kyauta mafi girma da ya yi mana ita ce hadayar fansa ta Ɗansa, Yesu Kristi. (Matta 20:28) Kamar yadda za mu gani a wannan babin, fansar ita ce kyauta mafi tamani da za a taɓa yi maka, domin za ta ba ka farin ciki gaya kuma ta biya maka bukatarka mafi muhimmanci. Hakika, fansar ita ce nuna matuƙar ƙauna na Jehobah a gareka.

MECECE CE FANSA?

3. Mecece ce fansa, kuma me muke bukata domin mu fahimci muhimmancinta?

3 A taƙaice, fansa hanyar da Jehobah zai ceci ’yan adam daga zunubi da kuma mutuwa ce. (Afisawa 1:7) Domin ka fahimci ma’anar wannan abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, muna bukatar mu tuna abin da ya faru a gonar Adnin. Sai mun fahimci abin da Adamu ya yi hasara sa’ad da ya yi zunubi, kafin mu fahimci abin da ya sa fansar kyauta ce mai muhimmanci.

4. Menene kamiltaccen rai yake nufi ga Adamu?

4 Sa’ad da ya halicci Adamu, Jehobah ya ba shi abin da yake da muhimmanci—kamiltaccen rai. Ka yi la’akari da amfani da Adamu ya samu daga wannan. An halicce shi da kamiltaccen jiki da tunani, ba zai yi ciwo ba, ko ya tsufa, balle ya mutu. Sa’ad da yake kamiltaccen mutum, yana da dangantaka ta musamman da Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ce Adamu “na Allah.” (Luka 3:38) Saboda haka, Adamu ya more dangantaka ta kusa da Jehobah Allah, irin dangantakar da ke tsakanin ɗa da ubansa. Jehobah ya yi magana da ɗansa a duniya, ya ba shi aiki mai kayatarwa kuma ya sanar da shi abin da ake bukata a gare shi.—Farawa 1:28-30; 2:16, 17.

5. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce an halicci Adamu cikin “surar Allah”?

5 An halicci Adamu cikin “surar Allah.” (Farawa 1:27) Wannan ba ya nufin cewa Adamu ya yi kama da Allah a zahiri. Kamar yadda muka gani a Babi na 1 na wannan littafin, Jehobah ruhu ne da ba ya ganuwa. (Yohanna 4:24) Saboda haka Jehobah ba shi da jiki na tsoka da jini. Halittar Adamu cikin surar Allah tana nufin cewa an halicce shi da halaye waɗanda Allah yake da irin su, ƙauna, hikima, shari’a, da iko. Adamu yana da surar Ubansa a wata hanya kuma mai muhimmanci, domin yana da ’yanci ya zaɓi abin da yake so. Saboda haka, Adamu ba kamar inji ba ne da yake yin abin da aka ƙera shi ya yi kawai. Maimakon haka, zai iya yanke shawarar kansa, ya zaɓi tsakanin abin da ke mai kyau da abin da ke mugu. Da ya zaɓi ya yi wa Allah biyayya, da ya rayu har abada a cikin Aljanna a duniya.

6. Sa’ad da Adamu ya yi rashin biyayya ga Allah, me ya yi hasara, kuma ta yaya wannan ya shafi ’ya’yansa?

6 A bayyane yake cewa sa’ad da Adamu ya yi wa Allah rashin biyayya kuma aka yi masa hukuncin kisa, ya yi hasara mai girma. Zunubinsa ya sa ya yi hasarar kamiltaccen rai da dukan albarkatai da ke tattare da shi. (Farawa 3:17-19) Abin baƙin ciki, Adamu ya yi rashin rai mai tamani ga kansa da kuma ’ya’ya da zai haifa a nan gaba. Kalmar Allah ta ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da shi ke duka sun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Hakika, dukanmu mun gaji zunubi daga Adamu. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya ce ya ‘sayar’ da kansa da kuma ’ya’yansa ga zunubi da mutuwa. (Romawa 7:14) Babu wani sauran sa rai ga Adamu da Hauwa’u domin da son ransu suka zaɓi su yi wa Allah rashin biyayya. Amma mu kuma fa, da kuma sauran ’ya’yansu?

7, 8. Waɗanne abubuwa biyu ne fansa ta ƙunsa?

7 Jehobah ya ceci ’yan Adam ta wurin fansa. Mecece ce fansa? Fansa ta ƙunshi abubuwa biyu ne. Na farko, ana biyan fansa domin a ƙyale abin da aka kama ko kuma a sake sayan wani abu. Ana iya kwatanta wannan da kuɗi da ake biya domin a saki fursunonin yaƙi. Na biyu, fansa diyya ce da ake biya domin wani abu. Ta yi daidai da diyyar da ake biya domin naƙasa da aka yi wa wani. Alal misali, idan mutum ya haddasa haɗari, dole ne ya biya diyyar da za ta yi daidai da muhimmancin abin da aka lalata.

8 Zai yiwu kuwa a biya diyya ta babbar hasara da Adamu ya jawo mana kuma a kwato mu daga bautar zunubi da mutuwa? Bari mu bincika fansa da Jehobah ya yi tanadinta da kuma abin da wannan take nufi a gare mu.

YADDA JEHOBAH YA YI TANADIN FANSA

9. Wace irin fansa ce ake bukata?

9 Tun da kamiltaccen rai ne aka yi hasara, babu mutum ajizi da zai iya biyan diyyar. (Zabura 49:7, 8) Abin da ake bukata fansa ce da ta yi daidai da farashin abin da aka yi hasara. Wannan ya jitu da mizanin kamiltacciyar shari’a da take Kalmar Allah, wadda ta ce: “Rai maimakon rai.” (Kubawar Shari’a 19:21) Saboda haka, menene zai biya diyyar kamiltaccen rai da Adamu ya yi hasara? Ran wani kamiltacce mutum ne ake bukata don fansa da ta yi daidai.—1 Timothawus 2:6.

10. Ta yaya Jehobah ya yi tanadin fansa?

10 Ta yaya Jehobah ya ba da fansar? Ya aiko da ɗaya daga cikin ’ya’yansa kamiltattu na ruhu zuwa duniya. Amma Jehobah bai aiko da kowace halittar ruhu ba. Ya aiko wadda ta fi tamani a gare shi, Ɗansa makaɗaici. (1 Yohanna 4:9, 10) Da son ransa, wannan Ɗan ya bar wurin zamansa a samaniya. (Filibbiyawa 2:7) Kamar yadda muka koya a babi da ya gabata na wannan littafi, Jehobah ya yi mu’ujiza wajen ƙaurar da ran wannan Ɗan zuwa cikin Maryamu. Ta wajen ruhun Allah, aka haifi Yesu kamiltaccen mutum kuma ba shi da hukuncin kisa a bisa kansa.—Luka 1:35.

Jehobah ya ba da Ɗansa makaɗaici domin fansa a garemu

11. Ta yaya mutum ɗaya zai fanshi miliyoyin mutane?

11 Ta yaya mutum ɗaya zai kasance fansa ga mutane da yawa, miliyoyin mutane kuwa? To, ta yaya ma mutane miliyoyin suka kasance masu zunubi da fari? Ka tuna cewa domin zunubi, Adamu ya yi hasarar abu mai muhimmanci da yake da shi, kamiltaccen rai. Saboda haka, ba zai iya ba da shi ga ’ya’yansa ba. Maimakon haka, abin da ya ba su shi ne zunubi da mutuwa. Yesu, da Littafi Mai Tsarki ya kira “Adamu na ƙarshe,” ya kasance da kamiltaccen rai na mutum, kuma bai taɓa yin zunubi ba. (1 Korinthiyawa 15:45) Wato abin nufi, Yesu ya ɗauki matsayin Adamu ne domin ya cece mu. Ta wajen hadaya, wato ba da ransa, ransa kamiltacce wajen biyayya marar aibi ga Allah, Yesu ya biya diyyar zunubin da Adamu ya yi. Da haka, Yesu ya ba da bege ga ’ya’yan Adamu.—Romawa 5:19; 1 Korinthiyawa 15:21, 22.

12. Menene mutuwar Yesu ta tabbatar?

12 Littafi Mai Tsarki ya ba da cikakken kwatanci na wahalar da Yesu ya jimre kafin mutuwarsa. Ya sha muguwar bulala, baƙar rataya, da kuma mutuwar akuba a kan gungumen azaba. (Yohanna 19:1, 16-18, 30; Dubi Rataye, shafi na 204-206) Me ya sa dole ne Yesu ya wahala haka? A wani babi a gaba a wannan littafin, za mu ga cewa Shaiɗan ya yi zargin cewa Jehobah ba shi da bawa da zai kasance da aminci sa’ad da yake fuskantar gwaji. Ta wajen kasancewa da aminci cikin matsananciyar wahala, Yesu ya ba da amsa ga ƙalubale na Shaiɗan. Yesu ya tabbatar da cewa kamiltaccen mutum da yake da dama ya zaɓi abin da yake so zai iya kasancewa da aminci ga Allah ko da menene Iblis ya yi. Hakika Jehobah ya yi farin ciki gaya domin amincin Ɗansa abin ƙauna!—Misalai 27:11.

13. Ta yaya aka biya fansar?

13 Ta yaya aka ba da fansa? A ranar 14 ga watan Nisan na Yahudawa, 33 A.Z., Allah ya ƙyale aka kashe Ɗansa kamili kuma marar zunubi. Ta haka Yesu ya ba da hadayar ransa kamiltacce “sau ɗaya ɗungum.” (Ibraniyawa 10:10) A rana ta uku bayan mutuwarsa, Jehobah ya tashe shi zuwa rayuwa ta ruhu. A samaniya, Yesu ya miƙa wa Allah tamanin kamiltaccen ransa na mutum domin fansar ’ya’yan Adamu. (Ibraniyawa 9:24) Jehobah ya karɓi tamanin hadayar Yesu domin fansa da ake bukata a ceci ’yan Adam daga bautar zunubi da mutuwa.—Romawa 3:23, 24.

AMFANIN FANSA A GARE KA

14, 15. Domin mu sami “gafarar zunubanmu,” menene ne dole mu yi?

14 Duk da yanayinmu na zunubi, za mu iya more albarkatai masu yawa domin fansar. Bari mu bincika amfani na yanzu da kuma na gaba na wannan kyauta mafi girma daga Allah.

15 Gafarta zunubai. Domin mun gaji ajizanci, muna fama domin mu yi abin da ke nagari. Dukanmu muna yin zunubi ko a furcinmu ko ta ayyukanmu. Amma ta wajen hadayar fansa na Yesu, za mu sami “gafarar zunubanmu.” (Kolossiyawa 1:13, 14) Amma domin mu sami wannan gafara muna bukatar mu tuba da gaske. Dole ne kuma mu roƙi Jehobah cikin tawali’u, mu roƙe shi ya gafarta mana domin bangaskiyarmu a hadayar fansa na Ɗansa.—1 Yohanna 1:8, 9.

16. Mecece ta sa muke bauta wa Allah da lamiri mai tsabta, kuma menene muhimmancin wannan lamiri?

16 Lamiri mai tsabta a gaban Allah. Lamiri da yake sūka zai iya kai wa ga rashin bege kuma ya sa mu ji ba mu da amfani. Saboda gafarar da ta samu ta wajen fansa, Jehobah ya ƙyale mu mu bauta masa da lamiri mai tsabta duk da ajizancinmu. (Ibraniyawa 9:13, 14) Wannan ya sa mun sami ’yancin magana da Jehobah. Saboda haka, za mu iya yin addu’a a gare shi a sake. (Ibraniyawa 4:14-16) Kasancewa da lamiri mai tsabta yana ba da kwanciyar hankali, yana sa mu daraja kanmu, kuma yana ba da farin ciki.

17. Waɗanne albarkatai ne suka kasance masu samuwa domin Yesu ya mutu dominmu?

17 Begen rai madawwami a aljanna a duniya. “Hakkin zunubi mutuwa ne,” in ji Romawa 6:23. Wannan ayar kuma ta daɗa cewa: “Amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” A Babi na 3 na wannan littafin, mun tattauna albarkatai na Aljanna ta duniya. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Dukan waɗannan albarkatai da za su zo a nan gaba, har da rai madawwami a cikin ƙoshin lafiya, sun kasance masu yiwuwa ne domin Yesu ya mutu dominmu. Domin mu sami waɗannan albarkatai muna bukatar mu nuna cewa muna masu godiya domin wannan kyautar ta fansa.

TA YAYA ZA KA NUNA GODIYARKA?

18. Me ya sa za mu yi wa Jehobah godiya domin tanadin da ya yi mana na fansa?

18 Me ya sa za mu yi godiya ƙwarai ga Jehobah domin fansar? To, kyauta dai musamman tana da martaba idan ta ƙunshi sadaukar da lokaci, ƙoƙari, da kuma wani abu daga wurin mai bayarwa. Tana motsa mu sa’ad da muka ga cewa kyautar nuna ƙauna ce da gaske daga mai bayarwa. Fansar ita ce kyauta mafi martaba domin Allah ya yi sadaukarwa mafi girma ta wajen yi mana tanadinta. ‘Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya ya ba da makaɗaicin Ɗansa,’ in ji Yohanna 3:16. Fansa ita ce muhimmiyar tabbaci na ƙaunar da Jehobah yake mana. Kuma tabbaci ne na ƙaunar da Yesu yake mana, domin ya ba da ransa a gare mu da son ransa. (Yohanna 15:13) Kyautar nan ta fansa ya kamata ta tabbatar mana cewa Jehobah da Ɗansa suna ƙaunarmu.—Galatiyawa 2:20.

Neman ƙarin sanin Jehobah wata hanya ce ta nuna cewa kana mai godiya ga kyautar fansa da ya yi maka

19, 20. A waɗanne hanyoyi ne za ka nuna cewa kana mai godiya ga kyautar fansa ta Allah?

19 To, ta yaya za ka nuna cewa kana godiya domin kyautar fansa ta Allah? Da farko, ya kamata ka san Mai Bayarwa Mai Girma, Jehobah. (Yohanna 17:3) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki da taimakon wannan littafin zai taimaka maka ka yi haka. Sa’ad da ka ƙara sanin Jehobah, ƙaunarka gare shi za ta zurfafa. Sai kuma ƙaunar za ta sa ka so faranta masa rai.—1 Yohanna 5:3.

20 Ka ba da gaskiya ga hadayar fansa na Yesu. Yesu kansa ya ce: “Wanda yana bada gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada.” (Yohanna 3:36) Ta yaya za mu ba da gaskiya ga Yesu? Irin wannan bangaskiya ba a nuna ta da baki kawai. “Bangaskiya ba tare da ayyuka mataciya ce,” in ji Yaƙub 2:26. Hakika, bangaskiya ta gaskiya ana tabbatar da ita ta wajen “ayyuka” wato, abin da muke yi. Wata hanya ɗaya ta nuna bangaskiya ga Yesu ita ce ta wajen yin koyi da shi ba kawai ta wajen magana ba amma kuma ta wajen abin da muke yi.—Yohanna 13:15.

21, 22. (a) Me ya sa za mu halarci bikin Jibin Ubangiji kowace shekara? (b) Menene za a yi bayani a kai a babi na 6 da 7?

21 Ka halarci bikin Jibin Ubangiji kowace shekara. A yammancin ranar 14 ga watan Nisan, 33 A.Z., Yesu ya gabatar da bikin tuni na musamman da Littafi Mai Tsarki ya kira “jibin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 11:20; Matta 26:26-28) Wannan bikin ana kuma kiransa Bikin Tuna Mutuwar Kristi. Yesu ya kafa wannan domin ya taimaki manzanninsa da kuma dukan Kiristoci na gaskiya da za su kasance bayansu su tuna cewa ta wajen mutuwarsa na kamilin mutum, ya ba da ransa domin fansa. Game da wannan bikin Yesu ya ba da umurni: “Ku yi wannan abin tunawa da ni.” (Luka 22:19) Yin Bikin yana tuna mana ƙauna mai girma da Jehobah da Yesu suka nuna mana wajen fansa. Za mu iya nuna godiyarmu domin fansa ta wajen kasancewa a wajen Bikin Tuna Mutuwar Yesu. *

22 Tanadin da Jehobah ya yi na fansa hakika kyauta ce mai muhimmanci. (2 Korinthiyawa 9:14, 15) Wannan kyautar mai muhimmanci za ta amfani har waɗanda suka mutu. Babi na 6 da 7 za su yi bayani game da yadda hakan zai faru.

^ sakin layi na 21 Domin ƙarin bayani game da ma’anar Jibin Ubangiji, dubi Rataye, shafi na 206-208.