Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 113

Bulus A Roma

Bulus A Roma

DUBI sarƙar da take hannun Bulus, ka ga kuma sojan Roma da yake tsaronsa. Bulus ɗan kurkuku ne a Roma. Yana jira ne har sai Kaisar na Roma ya shawarta abin da zai yi da shi. Ko da yake yana kurkuku ana ƙyale mutane su ziyarce shi.

Kwana uku bayan ya isa Roma ya aika a kira masa shugabannin Yahudawa su zo su gan shi. Saboda haka, Yahudawa masu yawa a Roma suka zo. Bulus ya yi musu wa’azi game da Yesu da kuma mulkin Allah. Wasu suka gaskata suka zama Kiristoci, amma wasu ba su gaskata ba.

Bulus kuma ya yi wa sojoji dabam dabam wa’azi waɗanda suka yi tsaronsa. A cikin shekara biyu da ya yi a kurkuku Bulus ya yi wa’azi ga dukan wanda ya sami dama. Domin wannan har gidan Kaisar suka saurari bisharar Mulki, wasu kuma cikinsu suka zama Kiristoci.

Amma wanene wannan baƙo da yake rubutu a kan teburi? Ka sani? Hakika, Timothawus ne. Timothawus ma an jefa shi kurkuku domin wa’azin Mulki, amma an sallame shi. Kuma ya zo nan ne domin ya taimaki Bulus. Ka san abin da Timothawus yake rubutawa? Bari mu gani.

Ka tuna biranen nan na Filibbi da kuma Afisa a Labari na 110? Bulus ya taimaka wajen kafa ikilisiyoyin Kirista a waɗannan birane. Yanzu, sa’ad da yake kurkuku, Bulus ya rubuta wasiƙu zuwa ga waɗannan Kiristoci. Wasiƙun suna cikin Littafi Mai Tsarki kuma ana kiransu Afisawa da Filibbiyawa. Bulus yana gaya wa Timothawus abin da zai rubuta ga abokansu Kiristoci a Filibbi.

Filibbiyawan sun yi wa Bulus kirki ƙwarai da gaske. Sun aika masa da kyauta a kurkuku, kuma saboda haka Bulus yana yi musu godiya. Wanda ya kawo wa Bulus kyautar sunansa Abafroditus. Ya yi rashin lafiya ƙwarai har ya kusa mutuwa. Yanzu ya sami lafiya kuma yana shirye ya koma gida. Zai kai wannan wasiƙa daga Bulus da Timothawus sa’ad da ya koma Filibbi.

Sa’ad da yake kurkuku Bulus ya rubuta wasu wasiƙu biyu da suke cikin Littafi Mai Tsarki. Ɗaya zuwa ga Kiristoci ne a birnin Kolosi. Ka san abin da ake kiran wasiƙar? Kolosiyawa. Ɗayan kuma wasiƙa ce zuwa ga abokinsa da ake kira Filimon wanda kuma yana da zama a Kolosi. Wasiƙar game da bawan Filimon ne Unisimus.

Unisimus ya gudu daga wurin Filimon zuwa Roma. Unisimus ya sami labarin cewa Bulus yana kurkuku a nan. Ya zo ziyara kuma Bulus ya yi masa wa’azi. Ba daɗewa ba Unisimus ya zama Kirista. Yanzu Unisimus ya tuba da gudun da ya yi. To ka san abin da Bulus ya rubuta a cikin wasiƙarsa zuwa ga Filimon?

Bulus ya ce Filimon ya gafarta wa Unisimus. ‘Na aika maka da shi,’ Bulus ya rubuta. ‘Amma yanzu ba bawanka ba ne kawai. Ɗan’uwa ne Kirista nagari.’ Sa’ad da Unisimus ya koma Kolosi ya kai waɗannan wasiƙu biyu, ɗaya ga Kolosiyawa ɗayar kuma ga Filimon. Sai dai mu yi tunanin farin cikin Filimon sa’ad da ya sami labarin cewa bawansa ya zama Kirista.

Sa’ad da Bulus ya rubuta wa Filibbiyawa da kuma Filimon, ya ba su albishir mai daɗi. ‘Zan aika muku da Timothawus,’ Bulus ya gaya wa Filibbiyawan. ‘Amma ni ma zan ziyarce ku ba da daɗewa ba.’ Zuwa ga Filimon kuma ya rubuta: ‘Ka shirya mini masauƙi.’

Sa’ad da aka ƙyale Bulus ya ziyarci ’yan’uwansa maza da mata a wurare da yawa. Amma daga baya aka sake kama Bulus aka jefa shi kurkuku a Roma. Yanzu ya sani cewa za a kashe shi. Saboda haka ya rubuta wa Timothawus ya gaya masa ya zo da wuri. ‘Na kasance da aminci ga Allah, ‘Bulus ya rubuta, ‘kuma Allah zai ba ni lada.’ ’Yan shekaru bayan da aka kashe Bulus, aka sake halaka Urushalima amma wannan karon Romawa ne.

Amma da ƙarin bayani a cikin Littafi Mai Tsarki. Jehobah Allah ya sa manzo Yohanna ya rubuta littattafansa na ƙarshe har da Littafin Ru’ya ta Yohanna. Wannan littafi na Littafi Mai Tsarki ya faɗi abin da zai faru ne a nan gaba. Bari mu ga abin da zai faru a nan gaba.

Ayukan Manzanni 28:16-31; Filibbiyawa 1:13; 2:19-30; 4:18-23; Ibraniyawa 13:23; Filimon 1-25; Kolossiyawa 4:7-9; 2 Timothawus 4:7-9.