Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LABARI NA 7

Gwarzon Mutum

Gwarzon Mutum

SA’AD da mutane suka fara yawa a duniya, yawancinsu sun yi miyagun abubuwa kamar Kayinu. Amma akwai mutum ɗaya da ya bambanta. Shi ne wannan mutumin mai suna Ahnuhu. Ahnuhu gwarzon mutumi ne. Dukan mutane da suke tare da shi suna yin miyagun abubuwa, duk da haka Ahnuhu ya ci gaba da bauta wa Allah.

Ka san abin da ya sa mutanen suka yi ta yin miyagun abubuwa? Ka tuna, wanene ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi rashin biyayya ga Allah ta wajen cin ’ya’yan itace da Allah ya ce kada su ci? Hakika, wani mugun mala’ika ne. Littafi Mai Tsarki ya kira shi Shaiɗan. Yana ƙoƙari kuma ya sa kowa ya yi mugun abu.

Wata rana Jehobah ya sa Ahnuhu ya gaya wa mutanen abin da ba sa so su ji. Ga abin da ya ce: ‘Allah za ya halaka masu mugunta wata rana.’ Wataƙila mutanen sun yi fushi sosai da suka ji haka. Wataƙila ma sun yi ƙoƙari su kashe Ahnuhu. Saboda haka, Ahnuhu yana bukatar ya kasance da ƙarfin zuciya domin ya gaya wa mutanen abin da Allah zai musu.

Allah bai ƙyalle Ahnuhu ya daɗe sosai a tsakanin waɗannan mutane masu mugunta ba. Shekara 365 kawai ya yi. Me ya sa muka ce “shekara 365 kawai”? Domin mutane a wancan zamani suna rayuwa mai tsawo fiye da zamanin nan. Ɗan Ahnuhu Me·thuʹse·lah ya yi shekara 969 a duniya!

Bayan da Ahnuhu ya mutu, muguntar mutane ta ci gaba ƙwarai. Domin Littafi Mai Tsarki ya ce ‘mugunta kawai suke tunaninsa a dukan lokaci,’ kuma ya ce ‘duniya ta cika da mugunta.’

Ka san abin da ya sa duniya ta cika da damuwa a wancan zamanin? Domin Shaiɗan ya sami wata sabuwar hanyar sa mutane su yi mugun abu ne. Za mu koyi game da wannan a gaba.

Farawa 5:21-24, 27; 6:5; Ibraniyawa 11:5; Yahuda 14, 15.