Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Kirsimati?

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Kirsimati?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

Littafi Mai Tsarki bai ba da kwanan watan haihuwar Yesu ba, kuma bai ce mu yi bikin haihuwarsa ba. Littafin bincike na McClintock and Strong’s Cyclopedia ya ce: “Allah bai ce a yi bikin Kirsimati ba, kuma babu hakan a cikin Sabon Alkawari.”

Idan muka bincika tarihi, za mu ga cewa Kirsimati ya samo asali ne daga bukukuwan addinin arna. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa za mu ɓata wa Allah rai, idan muka bauta masa a hanyar da bai ce mu yi ba.—Fitowa 32:5-7.

Tarihin al’adun Kirsimati

  1. Yin bikin haihuwar Yesu: “Kiristoci na farko ba su yi bikin haihuwar [Yesu] ba domin sun san cewa yin bikin haihuwa al’adar arna ce.”—The World Book Encyclopedia.

  2. Ranar 25 ga Disamba: Babu tabbacin da ya nuna cewa an haifi Yesu a wannan ranar. Wataƙila shugabannin Coci sun zaɓi wannan ranar don ta yi daidai da bukukuwan da arna suke yi a wannan ranar ko kuma a lokacin sanyi.

  3. Ba da kyauta da yin liyafa da kuma biki: The Encyclopedia Americana ya ce: “Masu yin bikin Kirsimati suna bin salon masu yin bukukuwan Saturnalia, wani bikin Romawa da ake yi a tsakiyar watan Disamba. Alal misali, daga wannan bikin ne aka fito da bukukuwa na ba da kyauta da kuma ƙona kyandir.” Encyclopædia Britannica ya bayyana cewa ana “daina duk wani aiki da kasuwanci” a lokacin bikin Saturnalia.

  4. Wutar Kirsimati: Littafin bincike nan The Encyclopedia of Religion ya ce: Turawa suna yi wa gidajensu ado “ta wajen gyara itacen Kirsimati da wuta mai launi dabam-dabam” don bikin da suke yi a lokacin sanyi kuma don su yaƙi miyagun ruhohi.

  5. Bishiyoyi: “Limaman addinai na dā suna cewa kauci, wato wani irin itace da ke tsira a kan wasu itatuwa suna da iko sosai. Ana bauta wa holly, wani bishiya mai launin kore, a matsayin alamar dawowar rana.”—The Encyclopedia Americana.

  6. Bishiyar Kirsimati: “Yawancin Turawa arna suna bauta wa bishiyoyi, kuma ko bayan sun zama Kiristoci ma suna ci gaba da yin hakan.” Hanya ɗaya da suke yin haka ita ce, suna “ajiye bishiyar Yule a ƙofar gida ko kuma a cikin ɗaki sa’ad da ake hutu a lokacin sanyi.”​—Encyclopædia Britannica.