Koma ka ga abin da ke ciki

Tsare Bayananka

Tsare Bayananka

SANARWA TA MUSAMMAN: TA WAJEN YIN AMFANI DA WANNAN DANDALIN KO KUMA TA WAJEN SHIGAR DA BAYANANKA, KA BA MU IZININ YIN AMFANI DA BAYANANKA DON DALILAN DA AKA RUBUTA A KA’IDOJIN AMFANI DA KE KASA DA KUMA CIKIN JITUWA DA DOKOKIN DA AKA KAFA NA YIN AMFANI DA BAYANANKA.

 TSARE BAYANANKA

Muna daraja bayananka na sirri kuma muna shirye mu tsare su. A wannan ka’idojin amfani da dandalinmu, mun bayyana yadda za mu rika amfani da bayanan da ka ba mu ko wadanda muka samo daga wurinka sa’ad da ka shiga dandalinmu. Akwai bayananka da muke adanawa sa’ad da ka shiga dandalinmu kuma mun san muhimmancin tsare bayanan da kuma gaya maka yadda za mu yi amfani da su. Za ka iya ba mu wasu bayanai game da kanka. Alal misali, za ka iya ba mu sunanka da adireshin imel da adireshin gidanka da lambar wayarka ko wani bayani da zai taimaka mana mu gane ka. Ba ma bukatar ka sanya bayanai game da kanka kafin ka shiga sashen dandalinmu da jama’a suke shiga. Dandalinmu ya kunshi wadannan dandalin kamar su apps.jw.org da tv.jw.org da stream.jw.org da kuma wol.jw.org.

 MASU KULA DA BAYANANKA

Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc. wato, “Watchtower”, da ke birnin New York ne suke da mallakar wannan dandalin, kuma suna tallafa wa ayyukan da Shaidun Jehobah da aikin ilimantarwa da suke yi a duk fadin duniya. Wannan kungiyar ba ta cin riba ba ce. Idan ka bude shafi a dandalinmu ko ka yi gudummawa ko ka cika fom don a yi nazari da kai ko kuma ka yi wani abin da zai bukaci ka ba da bayananka, ka amince da wannan ka’idojin ke nan. Kari ga haka, ka amince a yi amfani da kuma adana bayananka a na’urorinmu da ke kasar Amirka kuma ka yarda Watchtower da kungiyoyin da ke tallafa wa Shaidun Jehobah a kasashe dabam-dabam su yi amfani da bayanan da ka bayar don aiwatar da bukatunka. Wannan kungiyar Shaidun Jehobah tana aiki tare da wasu kungiyoyinta a kasashe dabam-dabam. Wadannan kungiyoyin sun hada da ikilisiyoyin Shaidun Jehobah da ofisoshinmu a wasu kasashe da dai sauransu.

Wadanda za a zaba su kula da bayananka za su dangana da abin da kake yi a dandalin. Alal misali, idan ka yi gudummawa ga wata kungiyarmu a wata kasa, za mu tura sunanka da adireshinka zuwa ga wannan kungiyar. Ga wani misali, idan ka cika fom don a yi nazari da kai, za mu tura bayananka zuwa ga ofishinmu da ke kasar da kake, da kuma ikilisiyar Shaidun Jehobah da ke kusa da kai don a aiwatar da bukatarka.

Idan akwai wata dokar tsare bayanai a kasar da kake zama, za mu iya rubuta wadannan dokokin a karkashin shafin Data Protection Contacts don ka ga dokokin.

 YADDA MUKE KĀRE BAYANANKA

Muna daraja bayananka na sirri kuma muna shirye mu tsare su. Muna amfani da na’urorin zamani na ajiyar bayanai da tsare su don tabbata cewa babu wanda zai saci bayananka ko ya bude su ko ya sauya su ko ya goge su ko kuma ya yi amfani da su a hanyar da ba ta cancanta ba. Duk ’yan kungiyarmu da za su iya ganin bayananka da ma wata kungiya dabam da take taimaka mana suna da hakkin kāre bayananka. Za mu ajiye bayananka a na’urarmu har tsawon lokacin da ya dace muddin dai akwai bukatar yin hakan, ko saboda bin dokar ajiye bayanai.

Yayin da muke tura bayananka zuwa wani wuri, za mu tsare su ta wajen amfani da fasahar Transport Layer Security, wato TLS. Muna amfani da na’urorin da mutane kadan ne kawai suke da izinin amfani da su kuma muna adana su a wurin da ba kowa ba ne yake samun shiga don mu kāre bayanan da ka ba mu. Muna daukan matakai da dama don mu tabbata cewa bayananka ba su shiga hannun mutanen da ba su da izinin ganinsu ba.

 YARA

Idan shekarunka ba su haura goma sha takwas ba, to ka nemi izinin iyayenka ko wadanda suke kula da kai kafin ka ba da bayananka na sirri a wannan dandalin. Idan kuma kai mahaifi ne ko kana kula da yaron da ke amfani da dandalin nan kuma ka yarda yaron ya ba mu bayanansa, to, tamkar ka amince da wannan ka’ida game da yara ke nan.

 KUNGIYA TA UKU, WATO, MASU AIKI DA MU

A wasu lokuta, wannan dandalin zai kasance da hanyoyin zuwa dandalin masu aiki da mu (alal misali, za ka so ka cika fom a dandalinmu). Da zarar ka shiga dandalin masu aiki da mu, za ka san cewa ka shiga wani dandali dabam domin tsarin dandalin ya bambanta da namu kuma adireshin mashigar intane dinka zai canja. Mukan bincika ka’idojin tsare sirri na kamfanonin da muka zaba su yi aiki da mu a daidai lokacin da muka zabe su, kuma a lokaci-lokaci bayan haka, mukan bincika ka’idojinsu don mu tabbata cewa sun jitu da namu ka’idojin. Idan kana da tambayoyi game da ka’idojin tsare sirri na kamfanonin da suke aiki da mu, don Allah ka duba jerin ka’idojin tsare sirri da aka saka a dandalinmu.

 SAKON SABONTA WADANNAN KA’IDOJIN

A kullum muna sabonta abubuwan da ke wannan dandalin kuma muna inganta fasahar da muke amfani da ita. Kari ga haka, muna dada inganta abubuwan da za a iya yi ta dandalinmu. Saboda wadannan canje-canjen da kuma canji ga ka’idojin yin amfani da fasaha, za mu rika canja yadda muke amfani da bayanai a dandalinmu. Idan bukata ta taso mu canja Ka’idojin Amfani da Wannan Dandalin, za mu saka sanarwa a wannan shafin domin ka san sabbin bayanai da za mu rika samowa daga wurinka da yadda za mu yi amfani da bayanan.

 ACTIVE SCRIPTING KO YAREN JAVASCRIPT

Muna amfani da scripting mu inganta yadda dandalinmu yake aiki. Fasahar scripting yana taimaka wa dandalinmu ya mayar maka da bayanai da sauri. Ba ma amfani da scripting mu saka wata software a na’urarka ko mu samo bayanai daga wurinka ba tare da izininka ba.

Sai an kunna Active Scripting ko yaren JavaScript a mashigar Internet dinka kafin wasu sassan dandalin su yi aiki. Yawancin mashigar Internet suna bari a kunna ko a kashe wannan fasahar sa’ad da ka shiga wasu dandali. Ka bincika tsarin taimako da aka shirya don mashigar Internet da kake amfani da shi don ka san yadda za ka kunna fasahar scripting don wasu dandalin.