Koma ka ga abin da ke ciki

Ofishi da Bayanai Game da Zagaya

Muna gayyatarka ka zo zagaya a ofisoshinmu da kuma wuraren da muke buga littattafai. Ka bincika ka ga wurare da lokacin zagaya.

 

Tours Resumed: In many countries, we resumed tours of our branch offices on June 1, 2023. For details, contact the branch you would like to tour. Please do not visit if you test positive for COVID-19, display cold or flu-like symptoms, or have recently been exposed to someone who tested positive for COVID-19.

Nijeriya

Sanar da Ranar Zuwa Zagaya

Zai dace ne ku sanar da ranar da za ku zo zagaya? E. Don kada mutane su yi yawa kuma a tabbata cewa kowa ya ji dadin zagaya a ofishinmu, zai dace ku sanar da mu ranar za ku so ku zo. Ko kuna da yawa ko a’a. Ku sanar da mu ranar da kuke so ku zo akalla mako guda kafin ranar. Don zuwa zagaya a lokacin hutu, muna karfafa ku ku sanar da mu makonni kafin lokacin.

Idan ba ku sanar da mu ba, za ku iya zuwa zagaya a ofishinmu? Idan ba ku sanar da mu ba, ba za ku iya yin zagaya ba. Domin akwai adadin mutane da muke kai wa zagaya a kowace rana.

Wane lokaci ne ya kamata ku iso don ku yi zagayar? Don kada mutane su yi cunkoso, don Allah ku zo minti 30 kafin lokacin da kuka ce za ku zo.

Ta yaya za ku sanar da mu cewa kuna so ku zo zagaya? Ka danna “Sanar da Ranar Zuwa Zagaya.”

Idan ba za mu sami damar kai ku zagaya a ranar da kuka zaba kuma fa? Ku ci gaba da duba dandalin. Kuna iya samun damar zuwa zagaya domin wasu na iya canja ranar da suke so su zo ko kuma sun fasa zuwa.

Zagaya

Km 51, Benin-Auchi Road

IGIEDUMA 301110

JIHAR EDO

NIJERIYA

+234 7080-662-020

+234 8039-003-790

Takaitawa

Muna buga mujallar Hasumiyar Tsaro da Awake! guda miliyan 41 a yaruka tara a kowace shekara. Muna kai littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki zuwa jihohi da ke Nijeriya da kuma kasashe biyar a Afirka ta Yamma.

Saukar da Littafin Zagaya