Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Suna da Dokokin da Suke Bi Ne Game da Fita Zance?

Shaidun Jehobah Suna da Dokokin da Suke Bi Ne Game da Fita Zance?

 Mu Shaidun Jehobah mun gaskata cewa ka’idodi da kuma dokokin da suke cikin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau da za su faranta wa Allah rai kuma su amfane mu. (Ishaya 48:17, 18) Ko da yake ba mu muka tsara wadannan dokokin ba, muna yin rayuwa da ta jitu da su. Ka yi la’akari da yadda wasu cikinsu suka shafi batun fita zance. a

  •   Aure abu ne na dindindin. (Matta 19:6) Shaidun Jehobah suna daukan fita zance da muhimmanci don sun san cewa zai iya kai ga yin aure.

  •   Wadanda suka isa yin aure ne ya kamata su fita zance. Irin wadannan sun “wuce lokaci,” wato sun wuce lokacin da sha’awar jima’i ta ke da tsanani.—1 Korintiyawa 7:36.

  •   Ya kamata masu fita zance su zama wadanda suke da ’yancin yin aure. Akwai wasu da suka kashe aurensu amma a gaban Allah ba a yarda musu su yi aure ba. Me ya sa? Watakila ba zina ba ne ya sa suka kashe aurensu don fasikanci ko zina ne kadai zai iya sa a kashe aure.—Matta 19:9.

  •   An dokaci Kiristocin da suke son su yi aure da cewa su auri wadanda suke bauta wa Jehobah kadai. (1 Korintiyawa 7:39) Shaidun Jehobah sun dauki wannan dokar ba kawai ga wanda yake son koyarwarmu ba amma ga wanda yake bin ka’idodin Allah a matsayin Mashaidin Jehobah wanda ya yi baftisma. (2 Korintiyawa 6:14) Tun dā Allah ya dokaci mutanensa su auri wadanda imaninsu ya jitu da juna. (Farawa 24:3; Malakai 2:11) Wannan dokar har ila tana da amfani kamar yadda masu bincike na zamani suka gano. b

  •   Ya kamata yara su yi wa iyayensu biyayya. (Misalai 1:8; Kolosiyawa 3:20) Ga yaran da suke tare da iyayensu a gida, wannan dokar ta kunshi bin umurnin iyaye a batun fita zance. Wannan ya hada da shekaru da kuma wasu abubuwan da za a iya barin yaron ya yi a lokacin fita zance.

  •   Bisa ga Nassi, Mashaidin Jehobah ne da kansa zai iya tsai da shawarar soma fita zance da kuma wanda zai fita zance da shi. Hakan ya yi daidai da ka’idar nan: “Kowane mutum za ya dauki kayan kansa.” (Galatiyawa 6:5) Duk da haka, idan ya zo ga batun fita zance, mutane masu hikima da yawa suna neman shawara daga Shaidu da suka manyanta wadanda suka damu da su.—Misalai 1:5.

  •   Wasu abubuwa da yawa da mutane suke yi sa’ad da suke fita zance zunubai ne masu tsanani. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu guji lalata. Hakan ya kunshi yin zina, da yin jima’i da baki ko tsuliya, ko kuma yin wasa da al’aura tsakanin mutanen da ba su yi aure ba. (1 Korintiyawa 6:9-11) Yin abubuwan da za su iya ta da sha’awa tsakanin wadanda ba su yi aure ba “kazanta” ce kuma Allah ba ya so. (Galatiyawa 5:19-21) Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya haramta tadin iskanci da ya hada da “alfasha.”—Kolosiyawa 3:8.

  •   Zuciya tana da rikici sosai. (Irmiya 17:9) Za ta iya sa mutum ya yi abin da ya sani bai dace ba. Don su hana hakan faruwa, wadanda suke fita zance za su iya gujan wuraren da suna iya sa su cikin hadari. Za su iya daukan matakan da suka dace kamar kasancewa tare da mutane ko kuma su nemi wani da ya dace ya raka su. (Misalai 28:26) Wadanda suke so su yi aure sun san da hadarin fita zance ta intane, musamman yin hira da wanda ba mu sani sosai ba.—Zabura 26:4.

a Ko da yake wasu al’adarsu ta amince da fita zance, ba duka ba ne. Littafi Mai Tsarki bai ce dole sai mun fita zance ba ko kuma hakan ita ce hanya kadai na yin aure.

b Alal misali, wani talifi da ke littafin nan Marriage & Family Review ya ce “bincike guda uku da aka yi game da ma’aurata da suka jima da aure ya nuna cewa kasancewa a addini daya da gaskata abu daya da kuma imani daya ne suke sa aure ya jima (shekaru 25 zuwa 50 ko sama da hakan).”—Littafi na 38, fita na 1, shafi na 88 (2005).