Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 119

Wajibi Ne Mu Kasance da Bangaskiya

Wajibi Ne Mu Kasance da Bangaskiya

(Ibraniyawa 10:​38, 39)

  1. 1. A dā Allah yana aika saƙo

    Ta wurin annabawansa.

    Yau ta bakin Yesu Kristi, ya ce:

    ‘Mutane ku bauta min.’

    (AMSHI)

    In muna da bangaskiya,

    Za ta sa mu sami ceto.

    In mun nuna bangaskiya

    Za mu yi rayuwa har abada.

  2. 2. Yesu Almasihu ya ce mana

    Mu yi wa’azi da ƙwazo.

    Muna wa’azin nan babu tsoro

    Ga dukan maƙwabtanmu.

    (AMSHI)

    In muna da bangaskiya,

    Za ta sa mu sami ceto.

    In mun nuna bangaskiya

    Za mu yi rayuwa har abada.

  3. 3. Nuna bangaskiya na kāre mu,

    Za ta hana mu jin tsoro.

    Muna jimrewa don mun san cewa

    Cetonmu ya yi kusa.

    (AMSHI)

    In muna da bangaskiya,

    Za ta sa mu sami ceto.

    In mun nuna bangaskiya

    Za mu yi rayuwa har abada.

(Ka kuma duba Rom. 10:10; Afis. 3:12; Ibran. 11:6; 1 Yoh. 5:⁠4.)