HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Satumba 2015

Kana Samun Ci-gaba don Ka Manyanta Kamar Kristi Kuwa?

Ko mun dade muna bauta wa Jehobah, za mu ci gaba da manyanta a ibadarmu.

Lamirinka Yana Yi Maka Ja-gora da Kyau Kuwa?

Ka koya yadda zai taimaka maka ka tsai da shawarwari masu kyau game da jinya, nishadi da kuma wa’azin bishara.

‘Ka Tsaya da Karfi Cikin Imani’

Mene ne za mu iya koya game da imani daga yadda Bitrus ya yi tafiya a kan ruwa?

A Wadanne Hanyoyi ne Jehobah Yake Kaunar Mu?

Shin yana yi maka wuya ka fahimta ko kuma ka yarda cewa Jehobah yana kaunar ka?

Ta Yaya Za Mu Nuna Cewa Muna Kaunar Jehobah?

Hakan ya kunshi bauta masa da dukan karfinmu da ranmu da azancinmu.

TARIHI

Albarkar Jehobah Ta Sa Na Wadata

Ka karanta tarihin Melita Jaracz, wadda ta yi fiye da shekaru 50 tana hidima ta cikakken lokaci da mijinta Ted Jaracz, wanda daya ne cikin mamban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.