Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ta Yaya Za Mu Nuna Cewa Muna Kaunar Jehobah?

Ta Yaya Za Mu Nuna Cewa Muna Kaunar Jehobah?

“Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu.”—1 YOH. 4:19, Littafi Mai Tsarki.

WAƘOƘI: 56, 138

1, 2. Kamar yadda manzo Yohanna ya ce, yaya Allah ya koya mana mu ƙaunace shi?

HANYA mafi kyau da Uba zai koyar da yaransa ita ce ta kafa misali mai kyau. Manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Muna ƙauna, domin shi ne [Allah] ya fara ƙaunarmu.” (1 Yoh. 4:19, LMT) Saboda haka, a bayyane yake cewa Jehobah Uba ne mai ƙauna da ya kafa mana misali mafi kyau da zai taimaka mana mu ƙaunace shi.

2 A wace hanya ce Allah ya ‘fara ƙaunar mu’? Manzo Bulus ya ce: “Allah yana shaidar ƙaunarsa gare mu, da yake, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:8) Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu da gaske ta wajen ba da Ɗansa hadaya a madadinmu. Irin wannan ƙaunar ta ƙunshi bayarwa da kuma sadaukarwa. Mun amfana daga wannan gagarumar sadaukarwa, kuma hakan ya sa mun kusace shi.—1 Yoh. 4:10.

3, 4. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah?

3 A cikin halayen Jehobah, ƙauna ce ta fi muhimmanci. Shi ya sa Yesu ya ce dokar Allah mafi muhimmanci ita ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan ƙarfinka.” (Mar. 12:30)  Kalmomin Yesu ya nuna cewa Jehobah yana son mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu. Saboda haka, Jehobah ba zai ji daɗi ba idan ba mu bauta masa da dukan zuciyarmu ba. Hakan ya nuna cewa za mu ƙaunace shi da dukan ƙarfinmu da ranmu da kuma azancinmu. Abin da annabi Mikah ya ce Jehobah yake bukata a gare mu ke nan.—Karanta Mikah 6:8.

4 Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Ubanmu na sama da gaske? Ya kamata mu ƙaunace shi da dukan ranmu da mallakarmu. Kamar yadda Yesu ya nuna, hakan ya ƙunshi ƙarfinmu da tunaninmu da halinmu. A talifin da ya gabata, mun tattauna hanyoyi huɗu da Jehobah ya nuna ƙaunarsa ga ’yan Adam. Bari mu tattauna yadda za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da kuma kyautata ƙaunarmu a gare shi.

KA GODE WA JEHOBAH DON TANADIN DA YAKE YI MANA

5. Wane mataki ne za mu ɗauka saboda dukan abubuwan da Jehobah ya yi mana?

5 Mene ne za ka yi idan aka ba ka kyauta? Babu shakka, za ka gode wa wanda ya ba ka kyautar. Ƙari ga haka, za ka ɗauki kyautar da tamani kuma za ka yi amfani da ita a hanyar da ta dace. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga bisa ta ke, tana saukowa daga wurin Uban haskoki, wanda sakewa ba ta yiwuwa gareshi, ba kuwa inuwa ta juyawa.” (Yaƙ. 1:17) Jehobah ba ya fasa yi mana tanadin abin da muke bukata don mu rayu kuma mu yi farin ciki. Hakan ne ya sa muke ƙaunar sa.

6. Mene ne Isra’ilawa suke bukata su yi idan suna so su ci gaba da samun albarkar Jehobah?

6 Isra’ilawa sun yi shekaru da yawa suna jin daɗin abubuwan da Jehobah ya tanadar musu. Ya ba su dokokinsa da kuma abubuwan da suke bukata don su rayu. (K. Sha. 4:7, 8) Amma wajibi ne su riƙa bin dokokin Allah don su ci gaba da jin daɗin waɗannan abubuwan. Waɗannan dokokin sun haɗa da ba da hadayar “nunan fāri” ta ƙasar. (Fit. 23:19) Ta hakan, za su nuna cewa suna godiya ga Jehobah saboda ƙaunarsa da kuma albarkar da ya yi musu.—Karanta Kubawar Shari’a 8:7-11.

7. Ta yaya za mu yin amfani da ‘wadatarmu’ don mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah?

7 Mu kuma fa? Ko da yake ba a bukatar mu miƙa irin wannan hadayu a yau, ya dace mu nuna muna ƙaunar Allah ta wajen girmama shi da ‘wadatarmu.’ (Mis. 3:9) A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin hakan? Hakika, muna iya yin amfani da wadatarmu don mu tallafa wa wa’azin bisharar Mulki a yankinmu da kuma a faɗin duniya. Wannan hanya ce mai kyau ta nuna ƙaunarmu ga Jehobah ko da muna da wadata ko a’a. (2 Kor. 8:12) Da akwai wasu hanyoyi kuma da za mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah.

8, 9. Ta yaya dogara ga Jehobah zai nuna cewa muna ƙaunarsa? Ka ba da misali.

8 Yesu ya gaya wa almajiransa kada su yi alhini game da abinci da tufafi amma su ci gaba da saka ayyukan Mulki kan gaba a rayuwarsu. Ya daɗa cewa Ubanmu ya san ainihin abin da muke bukata. (Mat. 6:31-33) Saboda haka, mun dogara ga Jehobah don mun san cewa zai cika wannan alkawarin. Da yake muna amincewa da waɗanda muke ƙauna, idan muka dogara ga Jehobah sosai za mu ƙara ƙaunarsa. (Zab. 143:8) Saboda haka, ya dace mu tambayi kanmu: ‘Shin maƙasudina da salon rayuwata suna nuna cewa ina ƙaunar Jehobah  da gaske? Shin abubuwan da nake yi yau da kullum sun nuna cewa na dogara da shi ya biya bukatuna?’

9 Wani Kirista mai suna Mike ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah kuma ya dogara gare shi. Sa’ad da yake matashi, Mike yana da maƙasudin yin hidima a wata ƙasa. Sai ya yi aure kuma suka haifi yara biyu. Duk da haka bai daina tunanin hidima a wata ƙasa ba. Sa’ad da Mike da iyalinsa suka karanta labaran ’yan’uwa da suke hidima a wata ƙasa, sai suka tsai da shawara su sauƙaƙa rayuwarsu. Suka sayar da gidansu kuma suka koma ƙaramin gida. Mike ya rage yawan aiki da yake yi. Sai shi da iyalinsa suka ƙaura zuwa wata ƙasa, kuma sun yi shakaru biyu suna jin daɗin hidima a ƙasar, sai Mike ya ce: “Mun shaida cewa abin da Yesu ya faɗa a Matta 6:33 gaskiya ne.”

KA YI BIMBINI A KAN ABUBUWAN DA JEHOBAH YAKE KOYA MAKA

10. Me ya sa ya dace mu riƙa yin bimbini a kan abubuwan da muka koya game da Jehobah kamar yadda Sarki Dauda ya yi?

10 Shekaru 3,000 da suka shige, Sarki Dauda ya lura da abubuwan da ke sararin sama kuma hakan ya motsa shi. Ya rubuta cewa: “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa.” Ƙari ga haka, ya yi tunani game da Dokar Allah kuma ya ce: “Shari’a ta Ubangiji cikakkiya ce, tana mayar da rai: Shaidar Ubangiji tabbataciya ce, tana sa marar-sani ya zama mai-hikima.” Mene ne sakamakon irin wannan bimbini? Dauda ya ci gaba: “Bari batutuwan bakina, da tunanin zuciyata, su zama abin karɓa a gareka, Ya Ubangiji, dutsena da mai-fansana.” Hakan ya sa Dauda ya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Allah.—Zab. 19:1, 7, 14.

11. Idan muna ƙaunar Allah, mene ne ya kamata mu yi da koyarwar Littafi Mai Tsarki da Jehobah yake tanadarwa a yau? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)

11 A yau Jehobah yana koya mana abubuwa da yawa game da kansa da nufinsa da halittunsa da kuma Kalmarsa. Mutanen duniya sun ɗauki biɗan ilimi a jami’a da kuma manyan makarantu da muhimmanci sosai. Amma mutane da yawa da suka je irin waɗannan makarantun sun yi rashin bangaskiya kuma sun daina ƙaunar Allah. Amma, Jehobah yana son mu sami ilimi da hikima da kuma fahimi, wato yana son mu yi amfani da abin da muka koya daga gare shi don mu taimakawa kanmu da kuma wasu. (Mis. 4:5-7) Nufin Allah shi ne “dukan mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Muna nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta wajen yin wa’azin bishara da kuma taimakon mutane su fahimci nufin Allah ga ’yan Adam.—Karanta Zabura 66:16, 17.

12. Ta yaya wata matashiya ta nuna godiya ga tanadin da Jehobah yake yi?

12 Matasa ma za su iya nuna cewa suna ƙaunar Jehobah ta wajen nuna godiya don abubuwan da ya yi tanadinsu. Wata yarinya mai suna Shannon ta ce, sa’ad da take ’yar shekara 11, da ita da ƙanwarta ’yar shekara 10 sun halarci wani Taron Gunduma na “Godly Devotion” (Ibada ga Allah) tare da iyayensu. Sa’ad da ake ba da wani jawabi, an gaya wa matasa su zauna a wani bangare na musamman da aka keɓe. Ta ɗan yi fargaba. Amma ta yi farin ciki sosai sa’ad da aka ba kowane matashi kyautar wani littafi mai jigo Questions Young People Ask—Answers That Work. Ta yaya wannan kyautar ya sa Shannon ta ji game da Jehobah Allah? Ta ce: “A lokacin ne na san cewa  Jehobah ya wanzu da gaske kuma yana ƙaunata sosai.” Shannon ta daɗa cewa: “Muna farin ciki matuƙa cewa Jehobah Allah ya ba mu wannan kyakkyawar kyauta!”

KA KARƁI SHAWARA DA KUMA HORO DA ALLAH YAKE YI MANA

13, 14. Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da Jehobah ya yi mana horo kuma me ya sa?

13 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda Ubangiji yake ƙauna shi yake tsauta wa: kamar yadda uba yakan yi wa ɗan da yake jin daɗinsa.” (Mis. 3:12) Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da aka ba mu gargaɗi? Manzo Bulus ya ce: “Kowane irin horo ana ganinsa ba abin faranta zuciya ba, amma abin ban ciwo ne.” Hakan ba ya nufin cewa Bulus yana rage muhimmanci ko kuma amfanin horo, don ya ci gaba da cewa: “Amma daga baya yakan ba da amfani mai salama watau na adalci ke nan ga waɗanda sun wāsu ta wurinsa.” (Ibran. 12:11) Idan muna ƙaunar Jehobah, ba za mu yi fushi idan ya yi mana horo ba kuma ba za mu guji shawararsa ba. Ko da yake, hakan ba zai yi wa wasu sauƙi ba, amma ƙaunarmu ga Allah za ta taimaka mana.

14 A kwanakin Malakai, Yahudawa da yawa ba su saurari Jehobah ba. Bai dame su ba cewa hadayunsu ba sa faranta wa Jehobah rai. Saboda haka, Jehobah ya yi musu gargaɗi sosai. (Karanta Malakai 1:12, 13.) Yanayin ya yi muni sosai don Jehobah ya ce: “Zan aukar muku da la’ana, zan la’antar da albarkunku. Ko yanzu ma na riga na la’antar da su domin ba ku riƙe umurnina a zuciyarku ba.” (Mal. 2:1, 2, LMT) Hakika, ƙin bin dokokin Jehobah da gangan zai kawo mugun sakamako.

15. Wane hali ne ya wajaba mu guje wa a wannan duniya?

15 Duniyar Shaiɗan tana ƙarfafa mutane su zama masu fahariya da kuma son ƙai. Mutane da yawa ba sa son karɓan shawara ko kuma a gaya musu abin da za su yi. Wasu da suke karɓan shawara suna  yin hakan don ya zama dole. Amma, an gargaɗi Kiristoci kada su “kamantu bisa ga kamar wannan zamani.” Ya kamata mu san kuma mu bi “nufin nan na Allah mai-kyau.” (Rom. 12:2) Jehobah yana ba mu shawara a kan ƙari ta wurin ƙungiyarsa a kan batutuwa da yawa, kamar yadda maza da mata za su bi da juna da abokanmu da kuma nishaɗin da muke yi. Idan muka bi waɗannan shawarwarin, muna nuna cewa muna godiya kuma muna ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarmu.—Yoh. 14:31; Rom. 6:17.

KA DOGARA GA JEHOBAH DON YA TAIMAKE KA KUMA YA KĀRE KA

16, 17. (a) Me ya sa ya kamata mu nemi ja-gorar Jehobah sa’ad da muke tsai da shawarwari? (b) Mene ne Isra’ilawa suka yi maimakon su dogara ga Jehobah?

16 Idan yara suka hango masifa, sukan nemi taimakon iyayensu. Yayin da suke girma, sai su soma tsai da shawarwari da kansu don suna gani cewa sun waye. Hakan ba abin mamaki ba ne don suna girma. Amma, waɗanda suke da dangantaka ta kud da kud da iyayensu sukan nemi shawararsu kafin su tsai da shawara. Hakazalika, Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki kuma yana taimaka mana mu so nufinsa kuma mu aikata. Saboda haka, idan muna ɗaukan wasu matakai ba tare da neman shawararsa ba, hakan zai nuna cewa ba ma ƙaunarsa.—Filib. 2:13.

17 A zamanin Sama’ila, Filistiyawa sun ci Isra’ila da yaƙi. A maimakon su nemi ja-gora daga wurin Jehobah game da matakin da ya kamata su ɗauka, sai suka tsai da shawara: “Bari mu je mu ɗauki sanduƙi na alkawarin Ubangiji daga cikin Shiloh, mu kawo shi wurinmu, domin ya shigo a tsakaninmu, ya cece mu daga hannun abokan gabanmu.” Mene ne sakamakon? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aka yi babbar kisa ƙwarai: gama na wajen Isra’ila mutum zambar talatin [30,000], dakarai, suka fāɗi. Kuma aka kama sanduƙi na Allah.” (1 Sam. 4:2-4, 10, 11) Isra’ilawan suna gani cewa Jehobah zai kasance tare da su idan suka ɗauki sanduƙi zuwa bakin dāga. Amma a gaskiya, ba su nemi ja-gorar Jehobah ba, sun bi nasu ra’ayin kuma hakan ya haifar da mugun sakamako.—Karanta Misalai 14:12.

18. Mene ne ya kamata mu yi idan muna ƙaunar Jehobah?

18 Wani marubucin zabura da yake ƙaunar Jehobah sosai ya ce: “Ka kafa bege ga Allah: gama duk da haka zan yabe shi saboda taimakon fuskarsa. Ya Allahna, raina yana tagumi a cikina: Domin wannan ina tunawa da kai.” (Zab. 42:5, 6) Kamar wannan marubucin zabura, kana ƙaunar Ubanmu wanda yake sama kuma kana dogara gare shi kuwa? Ko da ka ce e, za ka iya ƙara dogara gare shi da dukan zuciyarka bisa wannan shawarar da ke Littafi Mai Tsarki: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”—Mis. 3:5, 6.

19. A waɗanne hanyoyi ne kake son ka yi ƙoƙari ka nuna kana ƙaunar Jehobah?

19 Da yake Jehobah ne ya fara ƙaunarmu, ya koya mana yadda za mu nuna muna ƙaunar sa. Bari mu ci gaba da yin bimbini a kan abubuwan da ya yi mana da kuma yadda yake ƙaunar mu sosai. Ƙari ga haka, bari mu nuna cewa muna ƙaunar sa ‘da dukan zuciyarmu, da dukan ranmu, da dukan azancinmu, da dukan ƙarfinmu.’—Mar. 12:30.