Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Ci gaba da Bauta wa Jehobah a “Miyagun Kwanaki”

Ka Ci gaba da Bauta wa Jehobah a “Miyagun Kwanaki”

WANI ɗan’uwa mai suna Ernst da ya ba shekara saba’in baya ya ce: “Rashin lafiyata sai daɗa ƙaruwa yake yi kuma yana hana ni yin abubuwan da nake son yi.” * Kana fuskantar irin wannan yanayin ne? Idan ka soma tsufa kuma lafiyar jikinka da kuzarinka sun soma raguwa, za ka ji kamar kana cikin yanayin da aka ambata a cikin littafin Mai-Wa’azi sura 12. A aya ta 1, an kwatanta lokacin tsufa da “miyagun kwanaki.” Amma, hakan ba ya nufin an ƙaddara cewa za ka yi baƙin ciki a rayuwa. Za ka iya yin rayuwa mai ma’ana kuma ka bauta wa Jehobah da farin ciki.

KA CI GABA DA ƘARFAFA BANGASKIYARKA

Ku ’yan’uwa tsofaffi maza da mata, ku tuna Jehobah ya san matsalolin da kuke fuskanta. Bayinsa da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki sun fuskanci hakan sa’ad da suka tsufa. Alal misali, Ishaku da Yakubu da Ahijah sun makance. (Far. 27:1; 48:10; 1 Sar. 14:4) Sarki Dauda ya kasa ‘jin ɗimi.’ (1 Sar. 1:1) Attajiri Barzillai ya daina jin ɗanɗanon abinci kuma ba ya jin daɗin kiɗa. (2 Sam. 19:32-35) Ibrahim da kuma Naomi sun yi baƙin ciki saboda rashin abokan aurensu.—Far. 23:1, 2; Ruth 1:3, 12.

Me ya taimaka wa kowannensu ya kasance da aminci ga Jehobah da farin ciki? Ibrahim “ya ƙarfafa ta wurin bangaskiya” a lokacin da ya tsufa don ya gaskata da alkawuran Allah. (Rom. 4:19, 20) Mu ma muna bukata mu kasance da bangaskiya sosai. Kasancewa da irin wannan bangaskiyar bai dangana ga shekarunmu ko baiwarmu ko kuma yanayinmu ba. Alal misali, Yakubu ya ba da gaskiya ga alkawuran Allah duk da cewa ya makance, ya raunana kuma ba ya iya tashi daga gadonsa. (Far. 48:1-4, 10; Ibran. 11:21) A yau, Ines mai shekara 93 tana fama da wata cutar mutuwar jiki, amma ta ce: “Kowace rana ina ji kamar Jehobah yana yi min albarka sosai. Ina tunanin Aljanna a kowace rana. Hakan yana sa in kasance da bege.” Hakika, wannan ra’ayi ne mai kyau!

Muna ƙarfafa bangaskiyarmu ta wajen yin addu’a, da karanta Kalmar Allah da kuma halartan taron Kirista. Duk da cewa ya tsufa, annabi Daniyel yana yin addu’a sau uku a rana kuma ya ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah. (Dan. 6:10; 9:2) Tsohuwar gwauruwa Hannatu “ba ta rabuwa da haikali.” (Luk. 2:36, 37) Duk lokacin da ka halarci taro kuma ka yi ƙoƙari ka saka hannu, kana ƙarfafa kanka da kuma dukan waɗanda suka halarta. Jehobah yana farin cikin amsa addu’o’inka, ko da akwai wasu abubuwan da ba za ka iya yi ba.—Mis. 15:8.

Ka zama mai karɓan baƙi

Hakika, burin amintattun bayin Jehobah da yawa da suka tsufa shi ne su riƙa gani kuma su kasance da kuzari don su yi karatu kuma su halarci taro, amma yin hakan yana daɗa maka da wuya ko kuma ba ka iya yi gaba ɗaya. Shin mene ne za ka yi? Ka yi amfani da duk wani tanadin da aka yi maka. ’Yan’uwa da yawa da ba sa iya halartan taro sukan gaya wa ’yan’uwa su yi masu rekod ɗin jawaban da aka yi a taro don su saurara. Wata ’yar’uwa mai suna Inge da ke da shekara 79 ba ta gani sosai. Amma duk da haka, tana shirya taro ta wajen amfani da bayanan da ke cikin littattafanmu, waɗanda aka buga da manyan harufa ta kwamfuta da wani ɗan’uwa a cikin ikilisiya yake tanadar mata.

Kana iya yin amfani da lokacin da kake da shi wajen sauraron karatun Littafi Mai Tsarki da littattafanmu da jawabai da kuma wasannin kwaikwayo da ƙungiyar Jehobah ta wallafa. Ƙari ga haka, za ka iya kiran ’yan’uwa a waya don ku ‘ƙarfafa juna.’—Rom. 1:11, 12.

KA KASANCE DA HIMMA A HIDIMAR JEHOBAH

Ka riƙa yin wa’azin bishara

Wata ’yar’uwa mai suna Christa da ke tsakanin shekara 84 da 86 ta ce: “Rashin iya yin abubuwan da kake yi a dā yana sa mutum baƙin ciki sosai.” Shin ta yaya tsofaffi za su iya kasancewa da farin ciki? Wani ɗan’uwa mai suna Peter ɗan shekara 75 ya ce: “Ta wajen kasancewa da ra’ayin da ya dace. . . . Kada ka riƙa damuwa a kan abubuwan da ba za ka iya yi ba. A maimakon haka, ka riƙa yin abubuwan da za ka iya cim ma.”

Ka yi la’akari da wasu hanyoyin yin wa’azi. Wata ’yar’uwa mai suna Heidi da ta ba shekaru 80 baya sosai ba ta iya fita wa’azi gida-gida kamar yadda take yi a dā. Tana amfani da kwamfuta wajen rubuta wasiƙu. Wasu tsofaffi masu shela suna soma tattaunawa da mutane yayin da suke zaune wurin shaƙatawa ko kuma a tashar mota. Ko kuma idan kana zama a gidan kula da tsofaffi, za ka iya yi wa ma’aikatan da kuma wasu da ke wurin wa’azi.

Ka riƙa ƙarfafa ’yan’uwanka

Sa’ad da Sarki Dauda ya tsufa, ya ɗaukaka bauta ta gaskiya da himma. Ya ba da gudummawar kuɗi kuma ya yi shiri don mutane su taimaka wajen gina haikali. (1 Laba. 28:11–29:5) Kai ma za ka iya yin ƙoƙarinka wajen taimakawa a wa’azi da kuma wasu ayyukan Mulki da ake yi a faɗin duniya. Za ka iya tallafa wa majagaba da kuma wasu masu shela da ƙwazo a ikilisiyarku ta wajen ƙarfafa su da kuma ba su kyauta ko kuma shirya musu ɗan abinci ko abin sha. Ƙari ga haka, za ka iya yin addu’a a madadin matasa da iyalai da masu hidima ta cikakken lokaci da marasa lafiya da kuma waɗanda suke da ayyuka da yawa a cikin ƙungiyar Jehobah.

’Yan’uwa tsofaffi, kuna da daraja kuma hidimarku yana da muhimmanci. Ubanmu na sama ba zai taɓa manta da ku ba. (Zab. 71:9) Jehobah yana ƙaunarku kuma yana ɗaukan ku da mutunci. Nan ba da daɗewa ba, za mu yi shekaru da yawa muna rayuwa ba tare da wahalar da ke tattare da tsufa ba. A maimakon haka, za mu kasance da kuzari da ƙoshin lafiya kuma mu ci gaba da bauta wa Allahnmu Jehobah mai ƙauna har abada!

^ sakin layi na 2 An canja wasu sunaye.